RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*By Maryamah* 💞💞
©2020
*PAGE* 4⃣4⃣
Nigeria.
Karfe 2pm Jirgin British airways ya sauka a filin sauka da tashin jiragen Sama na Malam Aminu Kano dauke da Passengers ciki harda Dr Abdul'ahad Abdullahi Galadima. Tafiya yakeyi cike da kuzari yana ratsa Aiport din zuwa inda ya tabbatar da Fahad dayazo dauka sa yake jiransa. Cikin doki suka rungume junansu, Fahad daya bude ido sosai yana kallon Aminin nasa daya tasamma shekara ne ganshi ba yace
"Man wai dama kai Fari ne? Kai tsaya ma kana kallon kanka a Mirror kuwa" daidai lokacin da suka zauna acikin motar, murmushi kawai yayi dan yasan dole ze sha tsokana shi kansa yasan ya canza ba kadan ba.
"Aboki gaskiya Amaryar nan ta iya kiwo dan Allah in zaka koma zan bika nima naci girkinta ko zanyi kyau haka'. Duk wasa yakai masa yana dariya yace
"Tunda ance maka abinci kadai nake ci nayi kyau din ba to abinda yafi qarfinka me dan iska". Dariya sosai Fahad yayi harda dukan steering yana cewa "Ina yafi qarfin ubana ma balle ni ai sekai".
Seda suka hau titi sosai fuskarsa ta chanza da yanayin damuwa ya kalli Fahad dake tuqi yana murmushi shi kadai yace
"Fahad how is Ni'ima doing? Why on Earth ma da zaku boyemin ciwonta?" Kallonsa kawai Fahad yayi ganin lokaci daya fuskarsa ta chanza daga farin ciki zuwa damuwa yace
"Wallahi nikaina ban sani ba, i was out of town for some assignments seda na dawo Ammi take sanar dani but she warned me kar na gaya maka". Shiru yayi yana kallon window babu wanda ya qara magana har suka shiga cikin Asibitin AKTH. A kofar ICU inda yake da tabbacin an kwantar da Ni'iman ya tarar da Ammi, Khadija, Hafsa se Umma wato mahaifiyar Ni'ima da yayyenta Maza guda biyu da Amna qanwarta suna zazzaume akan qatuwar dardumar da suka shimfida. Sannu da zuwa suka shiga yi masa gaba daya yana amsa wa dakyar yanemi guri kusada Umar Yayan Ni'ima ya miqa masa hannu sukayi musabaha haka Naseer ma. Hibbatullah yarinyar Khadija ta dane cinyarsa tana masa surutu ya shafa kan yarinyar kawai ba tare da yace komai ba.
"Babana ya hanya ya Amarya? se kuma aka taso ka ba shiri ko seda nacewa Yaya ta barka kawai tunda dai wannan ciwo ne sedai kawai a nema mata rangwame da ga Allah babu ranar tashi" tayi maganar cikin lafazin da yake nuna rauninta. A cikin Yayanta Allah ya dora mata qaunar Ni'ima se kuma ya bata ita me tsananin larura da tun tana yarinya ake saka mata ranar mutuwa gata dai har yanzu se wahalar kawai ake sha."Aa Umma ko daya dama ina shirin zuwa dan na samu sauqin ayyukan da nakeyi kuma se wannan din ta kasance yanzu me Dr din yace akan condition dinta?"
"Likitan yana ciki yanzu ma tunda muka zo babu wani takamaiman bayani da suka bada in akayi magana se suce wai seka zo ko Umar sunqi magana dashi" tayi maganar cikin son kecewa da kukan tausayin yar tata. Se sukayi shiru gaba daya, Ammi dake kallonsa tundazu abu biyu na yawo a zuciyarta. Na farko jin dadin sauyin data gani a tattare dashi wanda ko makaho ya shafashi yasan an samu sauyi sosai a rayuwarsa se kuma tausayinshi akan halin da matarsa take ciki, fitowar likitance ta katse musu magana ya miqe da sauri ya qarasa inda yake ya bashi hannu.
"Mr Galadima muje office dina ina son magana dakai" binsa bayan Dr Isha yayi yana tafiya kamar mara laka a jiki, gaba dayansa yayi sanyi. Rashin lafiyar Ni'ima na matuqar daga masa hankali. Seda ya zauna sosai a kunerar dake kallon likitan sannan ya turo masa folder dake dauke da hotuna na scanning. Beyi magana ba yajasu ya fara dubawa a hankali cikin zuciyar sa inbanda salati da tasbihi babu abinda yake a zuciyarsa wata zufa tana keto masa. Hotuna ne kusan guda biyar wanda aka mata.
"Am Galadima I'm sorry to say but she just have a little chance of survival, ka duba pictures din nan sosai(ya miqa masa wasu copys daban) kayi comparing da scanning results dinta. Dayan kidney dinta ta harbu, and about her heart" se yayi shiru.
YOU ARE READING
RUBUTACCIYAR QADDARAH
RomanceStory of two lovers Hamdah and Abdul'ahad who were blindly in love but didn't realize until it was too late for them, yes they are meant to be together but destiny keep them apart..