RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*By Maryamah* 💞💞
©2020
*PAGE* 1⃣7⃣
Rayuwa da masoyi me dadi, Abubuwa dayawa sun faru cikin zaman Auran Hamdah da Abdulmalik. Tana wata na biyu da Aure Maryam ta haihu tasamu ya mace sun sha suna yarinya taci sunan kakarta Maman Yusuf din wato Ruqayyah suna kiranta Amal. Tuni ta koma aikinta da Sabuwar motar ta da Yah Abubakar ya Siya mata lokacin auranta Dan haka bata da matsalar transport.
Kamar yanda ta saba duk ranar juma'a takan raba wuni a cikin gidannasu Abdulmalik din saboda bata zuwa aiki ranar yau ma haka ta kasance, suna kicin tareda Anty Amarya kamar yanda suke kiran last wife din Alhaji Kamalu suna taya ta girki, A babban Dining me cin mutum 16 kamar wani conference table tana jera kayan abincinne ta jiyo sallama daga cikin palour. Yammata ne zakada zakada har su hudu se Babbar mace da akalla atayi sa'ar Hajja, kallo daya zakayi musu kasan jininta ne saboda kamar da sukeyi sosai. Gaba daya su ukun suka gaisar da Anty Amarya data fito daga kitchen din haka itama mahaifiyar tasu ta tsaya suka gaisa sama sama banda guda wadda kuma da alama itace babbarsu data dauke kanta gefe tana danna waya da taunar chewing gum. Part din Hajja suka nufa ita dai Hamdah tana tsaye tana kallon su dan babu Wanda ma ya lura da ita cikinsu. A falon Hajja suka baje nan da nan aka cika musu gaba da kayan makulashe bayan sun Dan taba ne su ukun suka shiga dakinsu Khausar se dayar data kame a kujera tana ta muzurai. Kallonta Hajja tayi aranta tana kara karantar halin yarinyar.
Haula kenan uwar jiji da kai da takama ita tsabar nata isar ko gaisuwa ma se an roka inbanda son cimma wata manufa tata Ina Abdulmalik Ina wannan kodaddiyar yarinyar? Muryar Hajia Hauwa ce ta katse mata tunani tace "Bari na shiga bangaren Amare haryanzu fa banga surukar tamu ba". Haula dataji kaman mahaifiyar tata ta daba mata wuka tayi saurin jifanta da wani kallo, inkiya tayi mata da ta nutsu sannan taci gaba " Ai naso inzo bikin wallahi hajia amma kinsan lokacin muna tsaka da campain ne ba dama se dai naga hotunan biki Amarya kam masha Allah". Murmushi hajja tayi dan tasan wannan magana ba har zuciyarta takeyinta ba se tace mata "Amarya ai tana nan cikin gidannan ma nazata ma kun ganta kafin ku shigo tana taya Halima girki". "Toh kila tunda kinsan ba saninta mukayiba Amma dai babu ma wata bakuwar fuska dana gani gaskiya sedai ko tana cikin kitchen ne". "Ok bari to a kira miki ita" cewar Hajja sannan ta shiga kwalawa Rufaida kira taje ta kirawo Matar Yayansu.
Tunda suka shiga palour Hajia Hauwa da yarta Haula suka zuba mata ido kowanne da abinda take kissimawa aranta. A bangaren Hajiya tsantsar kyau da gayu irin na Hamdah ne ya rudata, Ita kuwa Haula zuciyarta ce ta shiga tafarfasa wani irin bakin kishi yana taso mata, babu hadi Matar Abdulmaleek ta mata fintinkau nisan bana wasa ba. A she Momy cutarta tayi datake cewa wai farar fata kawai Gareta. Harta karaso ta zauna kusa da ita bata sani ba se kamshin turarenta da ya cika mata hanci. Faram faram suka gaisa da Hajiya Hauwa ta tambayarta ango da zaman kadaici acewarta, "Ai babu ma wani kadaici dan ita ma tana fita aiki dan zaman da take ita kadai bashi da yawa" cewar Hajja ita dai Hamdah murmushi kawai tayi. Juyawa hajia Hauwa tayi tayiwa Haula da kiris ya rage tayi bindiga inkiya da ido nata gaisheta, iya wuya ta shaqa dandai bata san manufar Momyn tata ba yasakata ce mata "Sannu dai yakike"." Yawwa sannunki" Hamdah amsa mata a ranta tana jin haushin irin kallon data kafeta dashi kamar wata mayya dan haka seta mike tareda kallon Hajja tace "Hajja bari na wuce zanyi girkin dare lokaci ya fara ja". "Toh ba damuwa kema dai ke kike biyewa rigimar Abdul in ba Haka ba ga abincin anan girkin me zakiyi". Murmushi tayi tana tafiya tace Aa Hajja kinsan shi daga girkin ki se nawa yake ci gara dai nayi masa".
"Haka nada kyau kuma shima ya ringa cin girkin matarsa Ai" cewar Hajia Hauwa da zuciyarta ke tafarfasa kaman zata fashe dan gani take kamar da gayya Hajja Fattu ke jan surukar tata a jiki, bata zaci cewar ta sake har haka da ita ba ganin irin kai ruwa ranan da akayi da ita kafin ta amince da auran, idan kuwa hakane ashe dole ta tashi a tsaye ta sake shiri Dan zama be gantaba, da ganin idanun wannan yarinyar ba karamar kissa zatayi ba amma ai in tasan wata bata san wata ba. Kwafa taja aranta tana ayyana abinda ya kamata tayi dan bazasu taba bari ya kufce musu ba, bokanta ya gaya mata shi din dai shine mijin Haula kuma aure ne irin wanda take so dan yaron yana da Nasibi a rayuwa sedai har yanzu ta kasa hango mummunan abin daya ce ze faru a gaba tunda har tayi sakaci Ya auri wannan yarinyar, koma dai menene tawa kanta alqawari seta raba auran nan ta maye gurbin sa Haula koda zata rasa komai data mallaka.
Sun jima suna tattaunawa da kawar tata sedai ko kadan taki bata fuskar da zasuyi magana akan hadin Abdulmalik da Haulan, suna shirin tafiya ya shiga gidan dawowarsa kenan daga aiki ya shiga ya bawa Hajja wasu saqo daya karbo mata a tasha. Kasan cewar Juma'a ce yayi kwalliya cikin wata shadda cream se daukar ido take. Cike da girmamawa yagaida Hajia Hauwan se qara daure fuska yake saboda wani kallo da Haula ta kafeshi dashi kamar zata hadiyeshi. Gani tayi ya qara mata kyau na musamman kodan ta dade bata ganshiba ga wani qasumba daya tara tasha gyara ji take kamar ta tashi ta rungumeshi. Kallo daya yai mata ya dauke kansa, yaganeta sarai Amma seyai biris da ita. ya tsani mace marar Aji se wani lanqwashe murya take wai tana gaishe shi, seda ta maimaita kusan sau goma sannan ya amsa mata da "lafiya" yayi wa Hajjan sallama yai waje. Zungurinta Hajia Hauwan akan ta bishi kamar dama tana jira cikin Hanzari ta cimmasa yana dab da barin main falon, jin alaman mutum na binsa a baya ya sakashi tsayawa sannan ya kalleta "yadai" ya fada fuska a daure".
"Ba komai dama rakoka nayi" ta fada tana gyara tsayuwarta. Se ya kalleta sama da kasa sannan yace "No bana bukata ba fita zanyiba gurin Matata zanje" yai gaba yabarta a tsaye kaman zata kurma ihu. Lallai ma ya raina mata hankali wato gurin matar sa ma zeje, kamar kazar da ruwa yawa duka haka ta juya cikin gidan, su Surayya dake zaune a falon sukace me zasuyi inba dariya ba. Ko takan Mahaifiyarta ta dake tambayarta abinda ya faru ba bata bi ba ta suri jakarta kawai tai ficewarta dan tanajin bazata iya qara koda minti daya cikin gidansu ba. Dole Hajia Hauwa tayi wa Hajja sallama suka tafi. Ko a mota inbanda kuka ba abinda take uwar nata rarrashinta Mansura kanwarta data gaji tai tsaki sannan tace "wai fisabilillahi ance daga Maleek dinnan babu wani namiji ne ko yaya da zaki bi ki tsangomi rayuwarki a kansa, mutum yace baya sonki to ki hakura mana ko ana dole Haba duk kin bi kin damu mutane wani yace kije inda yake ai Dama in ka nunawa namiji kana sonsa dole yama wulakanci bare ke ai dai ko bakida zuciya yakamata ki hakura haka... " "In naki kuma fa uwata Ina ruwanki koni sa'ar kice Dan ubanki" Haulan ta katse Mansura cikin masifa. "Allah ya taimaka" Sayyada karamar kanwarsu ta fada kasa kasa gudun kar fadan ya dawo kanta da haka suka karasa gida.
Bangaren su Hamdah kuwa a kitchen ya tarar da ita, miyar dake kan Gas take juya wa a hankali tana bin wakar data kunna harda Dan taka rawa. Sosai ta burgeshi, yanda take juya jikinta ya masa kyau se kawai ya ciro wayarsa ya shiga yi mata video. Aikinta take hankali kwance ita bata ma San da tsayuwar sa ba se kamshin turarensa dataji ya fara yawa a kitchen din, tunawa da tayi ta fesa kadan yasa bata kawo shi din bane. Duk lokacin datake missing dinsa se kawai ta fesa turarensa hakan na rage mata kewarsa sosai. Kaman ance ta juya taga mutum jingine da Freezer yana doka mata murmushi ba shiri ta saki ludayin dan Harga Allah taji tsoro ko kadan bataji shigowarsa ba. Saurin karasawa yayi ya rungumeta yana dungure mata kai "Matsoraciyar kawai, da in da zakije" bakinta taturo sannan tace "To ai kaine banji shigowarka bafa ko karar motarka banji ba se kawai naganka kana kallona". Gaban stove din suka karsa still tana jikinsa ya shiga bude tukwanen yace "Me kike dafawa ne haka tun daga office nake jiyo kamshi duk yawuna yagama tsinkewa". Steamer ya bude, burabuskon shinkafa ne fari kal se tashin kamshi take. Tana kallon yanda yake hadiye yawu Dan tasan yanda yake son abincin, janye jikinta tayi ta dakko warmer din data ajiye a gefe tashiga juye hadaddiyar miyar Irish potatoe data ji nama yankan kanana dakuma vegetables, shi ya kwashe Burabuskon bayan ta diba wani a Warmers daban da zata kai wa Alhaji dan Yau yake dawowa. A tare suka jera kayan akan dining sannan suka shiga wanka. Suna tsaka da cin abincin sukaji sallamar Khaleefa shida Amrah da Afrah yaran Anty zahra. Da murnarta ta taresu suka dan gaisa kamin a fara halin da aka saba yana kwasar girki yana kushewa harda cewa Abdulmalik ya nemi Pligil dan dakyar in cikinsa baze baci ba wannan jagwalgwalon. Seda yai sallar isha sannan yai mata sallama tana ta mitar meyasa Anty zahra bata biyo suba dama Hamida tasan inda ta ajiyeta, rabon data je mata har ta manta. Dariya yayi yana cewa sunfi kusa ai ita kuma Anty Zahra dare ne yayi shi yasa bata zoba suma din sun takurane aka kawo su kwanar mata.
Washe gari a gidan Anty Zahra suka wuni se tsokanarta take wai kodai tare zasu juye irin wannan kiba da tayi haka (dayake itama tanada karamin ciki) dariya kawai tayi tana cewa "Haba Anty wallahi banida komai kawai dai hutune a haka ma fa Dan yanzu Ina fita aiki rana na dukana". Haka suka wuni suna hira sai bayan magriba suka tafi.
Rayuwa nata garawa kwanaki na shudewa se gashi wai har ana ba tun shekara da auranta, babu abinda ya chanza cikin kulawar da sukewa junansu sai daima abinda ya karu, zuwa yanzu tafara damuwa akan maganar samun ciki. Wata biyu da suka wuce da tayi missing period harta fara murna sedai watan gaba sega period dinta yazo abin tausayi har kuka tayi yaringa mata dariya kuwa. Tuni ta gama service se zaman shiru duka babu dadi abokan hirar ta ta duk sun tafi makaranta Khausar ce kawai Autar su Abdulmalik a gida ita kuma ba wani shirin kirki sukeyi da ita ba dan kusan shekarunsu daya dan haka ta rainata hakan yasa take kiyaye duk abinda ze hada su. Ita kam ta qagu dan har Mumcy ta kira wai ta mata prescribing maganin da Zata sha ta samu ciki se kawai tayi dariya tace mata wai saurin me take ta jira setayi goma ma.
Abinda ya qara mayar da hankalin ta akan tunanin tun wata ranar da Anty Amarya ke cewa Abdul din "Ni kuwa Abdul duk sa'annin auranku daga masu haihuwa se masu tsohon ciki mu kunki yo mana miji ko kishiya gashi dai Fatima ta haihu jiya da namiji naji ma wai sunanka za'a sakawa Dan" ta karasa cikin sigar dariya sedai tsaf yagane magana ce ta gaya musu shida Hamdan. Fatima Kanwarta ce datai mutuwar son Abdul din Amma yaki haka ta hakura sati dayane tsakanin auransa da nata shine yanzu ta haihu. Se yayi dan murmushi sannan yace "Haba dai Anty mudin nawa muke kuma auramma shekara daya kawai bari dai mudan kara hutawa tukunna kin babies din nan duk takura ce dasu suzo su hana mutum rawar gaban hantsi sudai Allah ya raya musu". Baki ta rike alamar mamaki ta daiyi shiru kawai, Mikewa shima yayi Dan dama tun fara maganar Hamdah ta shige gurin Mama Second wife din saboda suna shiri da ita babu laifi, ta fuskanci a fuska kadai Anty Halima ke nuna tana sonta amma a badini ta ringa yaba mata magana a fakaice kenan se yanzu ta gane dalilin saboda Be auri Kanwarta bane.
Da yamma ya shigo gidan, A dakinsa ya tarar da ita a kwance rubda ciki, bayanta ya hau ya zauna ba shiri tashiga tureshi tana "Wayyo Mumcy ya ballamin baya wayyo Abbah ya fasamin ciki kuzo ku ceceni". Birkitota yayi yana cewa "Muga cikin Ina ne ya fashe" ya shiga yi mata chakulkuli tana dariya. Seda komai ya lafa sannan yace mata "meya sa dazu kika gudo kika barni". Seta chanza fuskarta zuwa kalar tausayi sannan tace "Jaan maganar Anty fa gaskiya ce, ya kamata musan abinyi ko asibiti ma muje a duba mu". Hade rai shima yayi ya riko hannunta yace "Look Hamdah bana son shirme kema kin fara daukar irin tunaninsu kenan, ita kanta datake miki maganar kin san shekararta nawa a gidan nan kafin ta haihu?" Seta girgiza masa kai alamar Aa sannan ya ci gaba "To rana Daya akayi auransu da Mami kinga Yaya Mansur ne Babban dan Mami yama girmeni da kusan 2 years, ita kuma Sharifa ce first daughter dinta inaga befi ta baki shekara daya ba. Koma ba haka ba kindai san baki kaini son ki haifarmin baby Girl me irin idon nan naki bako" ya karasa yana shafa saman idonta "To ki sauraramin da batun haihuwa yanzu, Allah daya bawa kowa ze bamu muma layi ne bezo kanmu ba kinji ko".
"Naji amma dai Jaan yakamata dai muje gurin Dr mudai tabbatar da lafiyar mu sannan se muci gaba da addu'a kawai". Banza ya mata ya shiga bathroom tasan ba amsata zeyiba Dan haka ta Mike itama tashiga jera masa kayan gugarsa da aka kawo a closet.Please vote
Share and
Like
ESTÁS LEYENDO
RUBUTACCIYAR QADDARAH
RomanceStory of two lovers Hamdah and Abdul'ahad who were blindly in love but didn't realize until it was too late for them, yes they are meant to be together but destiny keep them apart..