Part 49

666 52 3
                                    

RUBUTACCIYAR QADDARAH*

*By Maryamah* 💞💞

©2020

*PAGE* 4⃣9⃣

"Abdul'ahad issa story time" Hamdah dake tsaya akansa ta fada.

"Wayyo Allah yarinyar nan baki da tausayi, ji nan yanda hannuna duk yayi ja ya kumbura saboda wahalan kama gashinki sannan ko hutawa banyi ba kice min wani story time go on Television ki kalli labarai mana". Kallonsa tayi ta dan harareshi ta gefen ido kafin tayi gaba tana cewa

"Ji kaman wani dayayi abin kirki kitson da duk sun gama warewa ma"

"Haba dan Allah" ya fada yana tashi zaune kitson da ya shafe awa biyar yanayi shi ne za'a ce ya ware. Seta zame hular kanta gashin data tattare ya zubo har kusan kan mazaunanta baqi sidik se walwali yake, babu alamar anyi kitso se farkon kawai inda be qarasa warewa ba.

"Allah ke kika kunceshi seda nace a saka sabulu kika qi yanzu gashi nayi wahalan banza dama kinsan kanki baze kitsu ba kika saka mutane wahala".

"Ko kuma kaidai daga gani akan wasu kace se anyi ai gobe in aka ce kayi bazayi ba" ta fara masa gwalo. Kiran sallar da wayarsa yayi ne ya katse masa amsar daya so ya bata, se ya miqe yana cewa "kiyi alwala muyi jam'i" ya shige toilet. Dayan dakin taje tayo alwalar ta shimfida musu sallaya kafin ta saka dogon hijab dinta ta zauna tana shan ruwa har lokacin be fito ba. Ruwan da taji an watsa mata a fuskaka yasa ta kalleshi, ashe wanka ya yi. Farar jallabiyya ya saka ya fesa turare sannan ya jasu sallar. Bayan sun idar hijab din kawai ta cire ta miqe kafa daidai akan sallayar tana cewa

"Abdul'ahad yunwa nake ji kuma ni dan wake nake so naci da yajin tafarnuwa da tomatoes da onion, boiled egg...."

"Ai seki tashi ki dafa kuwa, wannan uban lissafin ni an ce miki nasan ingredients din hada wani dan wake ne" yai saurin katseta. Seta bata fuska harda buga kafa kamar wata yarinya tace

"Zan nuna maka fa dan Allah in nayi da kaina bazan iya ci ba, in ba haka ba to ka kaini gidan Aliya sena kirata tayi mun"

"Wace ce Aliya?"

"Course mate dina ce"

"Babu inda zakije get up muje kitchen din ki nunamin yanda akeyi". Seta miqe da sauri kuwa ya tareta dan ya tsorata da yanda ta miqe din, "Hamdah meye haka what if you hurt your self or the baby you know i won't takr it lightly with you ko?" Seta saki murmushi, kulawan da yake bata ta daba ce. Abdul'ahad qarshe ne gurin iya soyayya da tattalin mace. Hannunsa cikin nata suka isa kitchen din ya ja mata kujera ta zauna tana bashi command.

Kamar me girka abincin biki haka yayi kacakaca da kitchen din, taimakonta daya danwaken ya hade saboda ita ta zuba masa kuka da quantity din kanwar da ze kwaba dashi. Haka ya damula mata kitchen kamar anyi dambe yace kuma baze gyara ba tunda yayi girki ita tayi wanke wanke. With irritating face yake kallon dan waken data zage tana ci, dan dai kawai Ammi tace yaringa barinta tana cin duk abinda take so shi yasa. Seda tayi nak ta sha ruwa sannan ta shiga gyaran kitchen din yana zaune yana kallon ta dan ya rantse bazeyi ba se tura baki take tana riqe baya a dole ta gaji.

Wunin ranar haka suka yishi se wani shan qamshi yake itama ta debi iskar data kwaso shi ta watsar.

"Anty Hamdah fushi kuma akayi da Abdul'ahad" ya fada daidai sanda ya tsaya akanta tana qoqarin cire dan kunnenta dan ta fara jin bacci, ta gaji da jiran labarin yana sane kuma yai mata shiru. Seta zagayeshi ta haye gadon tana qunquni "dan ma mutum yaga an damu da labarin shine ze wani shanya mutane, to kasa maida yaji ka cinye shi". Seya saka dariya dan yajita, rigar jikinsa ya cire sannan ya kashe haske shima ya hau gadon.

"Malam ka tashi ka tafi can dakin, koma ka tafi apartment dinka mana ana dole ne" Hamdah tayi maganar cikeda tsiwa ganin yana qoqarin shiga jikinta. Seya miqe zaune shima tareda kunna bed side lamp yana kallon fuskarta, "wai duk saboda labarin ne to yi haquri zo kiji" fitilar ya sake kashe wa kafin ya janyota cikin jikinsa kansa akan kafadarta ya fara magana.

RUBUTACCIYAR QADDARAHWhere stories live. Discover now