Part 29

549 49 0
                                    



*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

*By Maryamah* 💞💞

©2020

*PAGE* 2⃣9⃣


Da kallo ta ringa bin Ni'ima dake ta faman doka mata murmushi, at last yau taga Hamdah, Hamdan data hanawa mijinta walwala. Matar da tayi awon gaba da dukkan farin cikin Mijinta. A tsahon zaman auransu tasan Gangar jikinsa kawai ta aura amma zuciyarsa tana tare da wata duk da hakan ba wani damunta yake sosai ba saboda ita take sonsa, ta sani tausayine yasa ya aureta ba wai dan Soyayyaba kuma har zuwa yanzu bata da yaqinin ya karbeta a matsayin masoyiyarsa.
"Ina ta jin labarinki a bakin Dadyn Hamdah dama nace duk randa muka zo Nigeria sena nemeki se gashi bani da rabon shan wahala na ganki ma a free" Ni'ima ta fada tana qarewa Hamdah kallo cikin yaba kyau da kyawun surar da Allah ya mata. Tabbas ta isa a sota, ta isa ta dauke hankalin ko wanne namijin da ya isa da kansa, ayanda take ganinta a hoto se taga har tafi kyau a fili dan tuni ta haddace kamannin Hamdah tsaf saboda yawan hotunanta a cikin gidansu. Tabbas da ace ta kasance cikin mata masu tsananin kishi da batasan yanda zata kaya musu a wannan haduwar ba, kilan da se ta kasheta duk hukuncin da za'a mata sedai ayi mata shi. Tana matsayin matar Abdul'ahad ne kawai kuma uwar yarsa bayan wannan bata da sauran wani matsayi a gurinsa ta sani. Kallon yanda Hamdah Karama da nketa liqewa Hamdan take wani tunani ya darsu a zuciyarta, irga kwanakin da take ganin su suka rage mata tayi a zuciyarta ko ba komai rabin burinta ya cika taga Other Half din Abdul'ahad, abu na qarshe shine ta sake hadasu, su zauna a karkashin inuwa daya ma'ana a matsayin ma'aurata.
"Zaki iya hada miji da ita, zaki iya jure kallon Abdul'ahad yana nuna mata irin soyayyar da kikayi kwadayin samu a gurinsa" zuciyarta ta shiga tambayarta, setaji hawaye na neman kawo mata dan haka ta miqe tana tambayar Maryam Toilet, Bedroom dinta ta kaita sannan ta dawo gurin Hamdah data zauna a zahiri hankalinta yana kan Little Hamdah dake ta faman zuba mata surutu a badini kuwa ta kusan zuwa China a tunani, tunanin da takamaimai bata san name takeyi ba.

"Hamdah nasan zaki ga laifina wallahi nima bansan....." Seta katse wa Maryam din magana tace
"Baki laifin komai ba Maryam, kilan keda mijinki baku san kasancewar mu tare. Amma meya sa baku gayamin yayi aure har ya haifi ya ba? Meyasa duk lokacin dana tambayeki ko Yusuf se kucemin baku san inda yake ba? Maryam cewa fa kikayi rabonki dashi tun muna makaranta meye ribar boyemin da kukayi" se ta dakata saboda fitowar da Ni'ima tayi, Hawayen da suka fara sakko mata ta shiga gogewa Little Hamdah na tayata dukda bata gane komai, Zaman mayafin kanta ta gyara sannan ta dauki jakarta da key din motarta ta nufi kofar tana cewa "Na tafi zan aiko Hamidah anjima ta karbarmin kayan kawai" bata saurari magiyar da take mata ba ta sa kanta waje a zuciyarta tana tunanin if Maryam is truly her Bestfriend. Cikin motar ta shiga ta zauna amma ta kasa kunnata se kawai ta kifa kanta akan stirring ta saki kuka me ciwo, tsohor Soyayya ce taso mata akansa, da kadan da kadan take tuna wancan lokacin, kalamansa daidai da suke da mugun tasiri a zuciyarta da bata taba mantawa dasu ko sau daya ba, ashe ita take shirmenta, ita take tunanin akwai wata *RUBUTACCIYAR QADDARAH* a tsakaninsu. Ita take ganin kamar wata rana zasu zama abu daya, Ashe duk shirme takeyi tuni yayi aure ya manta da babinta a rayuwarsa. Kila ma ko ganin daya mata yanzu be gane ta ba shi yasa ma yayi tafiyarsa.
Haka taci gaba da kukan da babu me rarrashinta.

****************************************

Ta cikin Mudubin motarsa yake kallonta saboda glass dinta masu haskene bata rigada tayi musu Tint ba. Duk saukar hawayenta daya yana jinsa kamar digon Dalma akan zuciyarsa ne amma yaya zeyi? Ya rigada yayi wa kansa alkawarin cireta daga zuciyarsa tunda dai bashi da Sa'a, a koda yaushe baya taba zuwa a daidan lokaci se wani ya rigashi Fara gini tukunna. Be manta da Hamdah ba, abubuwa da yawa sun faru dashi bayan rabuwarsu wanda sedaga baya yake ganin duk laifinsa ne. Shi yayi saurin Cire tsammani yaja da baya a filin daga, ya sani da ace ya saurareta a wancan lokacin da kilan abubuwa basu tafi akan yanda suke yanzu ba amma yaya zeyi? Qaddarar Auran Ni'ima da Haihuwar Little Hamdah ce ta saka shi wannan fushin zuciyar ya tafi akan abinda befi ya dauke shi a matsayin wasa ba.
Ji yake baze iya jure kukan nata ba, har yakai hannu ya bude motar da niyar zuwa ya rarrasheta sedai ko me ya tuna se kawai ya maida kofar ya rufe. Ganinta a yanzu ya qara hura wutar soyayyrta a zuciyarsa da wani bala'in kishinta. A duk lokacin daya tuna ta taba aure ji yakeyi kamar ya kashe kansa tsabar kishi. Harga Allah yaji dadin Mutuwar Abdulmalik, abinda ya hanashi dawowa rayuwarta a lokacin uzurine babba wato Matarsa.

RUBUTACCIYAR QADDARAHWhere stories live. Discover now