tsakure

528 8 1
                                    

ASSALAMU ALAIKUM

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼.

             *MABARACIYA*

Tun kafin nace wani abu da farko.
INAYIWA ƊAUKAKIN AL'UMMAR MUSULMAI BARKA DA WANNAN BIKIN SALLAH MAI ALBARKA.

Bayan nan kuma,albishir zanyi muku kucemin goro yan uwa,littafin MABARACIYAH kaman yanda na faɗa,to ba makawa lokacin yayi na fasowarsa duniyar yanar gizo gizo.
Zai fara zuwa a ranar LARABA,4 ga watan mayu,wanda yayi daidai da 3 ga watan shawwal..
Littafine mai tafiyah a hankali cikin salon rawar ƴan mata,yayi gaba kana yayi baya.  Labarine mai ɗauke da bangarori daban daban,kama daga ɗaukar fansa,CIN AMANA,GIDAN SARAUTA,GIDAN MARAYU,GIDAJEN GWAMNATI,MULKIN SHUGABANNI,ASIBITI,TSANGAYA,ƘUNGIYAR ASIRI,MUGUNTAR KISHIYA, da sauran wasu wuraren sosai a littafin nan.
Na shirya nishaɗantar daku da kuma faɗakar da ku harma da tura muku wani saƙo ta wanann littafin.

SHARAR FAGE

Ni halittace wacce take tamkar hawainiyah,da take fitowa a launi daban daban.
A wanni wajen ma inaga nafi hawainiyar saboda ita idan ta sanja launi bata bayyana a wata siffah ta daban.
Wasu na kirana da matsoraciya,wasu kuma azzuluma, yayinda a wani wajen nake amsa kiran saliha, wani wajen kuma ni mai daukar fansa ca,wasu garesu ni mayaudariyace yayinda wasu ke daukata majinginarsu, wasu kuma sukan kirani da shu'umar macijiyah,yayinda wasu kuma ke yimin kirari da jajirtacciyah.
A yanda ainihin sunan yake a zukatan mafi akasarin mutane har gani kaina shine MABARACIYAH  mace daya ƙwall acikin taron maza na almajirai¡¡...........
Shin amma ku zaku yarda da hakan,anya kuwa duk ni kadaice nake amsa sunan,ko kuma akwai masu kamanni kai?
Wace amsa ku kuka bawa kanku???
   



TSAKURE 1

Okay good,aikinku yana kyau da kuka taimaka min na kashe mabaraciyah,nayi nasarar kashe tsuntsu biyu da dutse ɗaya,na kasheta na shafe aikinta,sanann kuma ni nasamu yarda da kuma ƙarin matsayi daga cibiyar bincike,yanzu aiki da salo zai soma daga yanda yake.
Mataye a shirya, Viper ta fito daga cikin raminta bayan tsawon ɗaɗewar datayi a ciki tana dakon jiran ranar fitowa,yanzu matar datayi mata kanainai ta hanata fitowa ta matsa.
Lokacine ita ma daya kamata ta fito tayi nata sunan sanann tabawa zuciyarta abinda take muradi.
Mun shiga episode 2 na wasan,bansan kozanyi wasan dayafi nata ko ahah"
Tana kashe wayar ta zefata a aljihu tareda gyara ɗamararta da kuma hularta,wani mungun shu'umin murmushi tayi tareda cewa,
"Micijiya zata shiga cikin rigar mai kamata,yayinda shikuma bai san tana ciki ba,yayi zaton mai taimakonsa ce,inda zaiyi ta faɗamata sirrin yanda zai kamatan.
Mai zai faru?...shin tunda ta riga tasan ta inda zai kai farmaki zata barshi kuwa yayi nasarar.
Salon Viper lady shima daban yake da na mabaraciyah.

TSAKURE 2

"Kayi haƙuri yah muzanbilu,nayi maka alkwari daga wannan nadaina bazan sakeba,amma matar sarkin katsina babu mai hanani illatata koda ban kasheta ba saita ƙwammaci a kashetan"
Saurin zaburah muzanbilu yayi ya tashi tsaye tareda sunkuyowa yana kallon deejan,wacce ko a jikinta kaman ba ita tafaɗa ba.
"Deejah!mai kika ce,naji kunnena yajiyo min wani gagarren aiki,mai kike nufi da hakan"
"Basai ka tambayeni ba,lokacin da aikin ya kammala zakaji a kafafen yaɗa labarai cewar mabaraciyah ta kashe matar sarki Alhaji Bilyaminu muhammadu,wato Hajiyah Fulani Ateekah."
Wannan shine aikina na karshe akan manyan gari,daga nan kuma sai kaɗa hantar  masu bincike kawai"

Ya kukaji salon toh,yana nan zuwa a manhajar AREWABOOKS,karku manta chapter ɗaya nairah goma,kullum shafi biyu amma a haɗe suke,
Danna nan domin follow ɗina kar ayi babu kai ko babu ke.
Littafin tangal yake da kyautah ƴan uwa,kusanni da yi muku sauƙi,ayi follow please.

http://arewabooks.com/u/sadisakhna

Wannan kuma shine link ɗin littafin domin sakashi a reading list cikin sauƙi

https://arewabooks.com/book?id=625b1176a81b3be9855cfa30

_*sadi-sakhna*_
❤❤❤❤❤❤

MABARACIYAHWhere stories live. Discover now