chp 13_14

139 3 0
                                    

*(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)*

             *MABARACIYAH*
           (mai harshen damo)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε.
          

_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)

                                       

Paid book #400
3131951977
Auwal sadiya
First bank

Mai turo kati kuma ta wanann number MTN
09035784150

Mutanen niger su tuntubi wanann number
+227 97 21 16 15

Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a.

      _____________________
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃


 
                                       

13••14






Dukkan mu kallonta muke yanda take nishi numfashinta yana sama da kasa,kaman da alama yana mata wahala wajen shagarsa.
Gashi dukkanmu dagani har khairi da kuma sauran yaran an rasa mai matsawa kusada itah,ganin hakanne yasa na jawo khairi tareda yimata raaɗa a kunne ,na taje ta ƙira inno a ɗakinta.
Bata daɗe da fitaba sai gata tashigo itada innon.
Saurin ƙarisawa wajen ta tayi,wanda har yanzu razanar bata bar jikinta sosai ba.
"Khamriyyah lafiyah kuwa,kinga ɗago ko kalleni,menene ya faru"
Tana yi mata magana tana tofamata addu'o'i a jikinta,dan abinnata yayi kama da wanda aljanu suka ra'esu.
A hankali take sauƙe sautin kukannata,har ya zamo iya ajiyar zuciya kawai takeyi,kallon inno take da kuma su sabrah,sai a sanann ma takula asheda mutane a kanta.
Da alama kenan duk tambayoyin da inno tayi mata batasan tanayi ba.
Mamaki abin yabani,wai dama haka masu aljanu sukeyi,danni ban taba ganin mai yiba,tunda mu iyah rayuwarmu to ta ƙarene dag makaranta sai kuma gida.
Bamuda buƙatar yawo yawo irinna yara,dan idan wasanne har ma munyi yawa inaga.
"Kalleni khamriyyah,yanzu kinajin mai nakecewa,in kinaji ki ɗagamin kanki"
Ɗaga kan khamriyyah tayi,wanda hakan yake nuna taji abinda inno ta faɗa kenan.
"Mai yafaru dake,ki faɗamin idan har kin ɗaukeni a matsayin uwa,kaman yanda na ɗaukeki a matsayin ɗiyata"
Jijjiga kai khamriyyah tafarayi tana ƙara dawowa da kukannnata,saidai yanzu a cikin hankalinta takeyi,bana razana bane,
Yanda take kukan da kuma abinda yake kan fuskarta,ya isa shaidawa mutum batason amsa tambayar da inno tayimata.
"Kiyi haƙuri inno.....in in in ?"
Daga haka ta gagara sake cewa furta wata kalmar bayan haka.
Ganin tambayar bazai haifar da wani ɗa mai ido ba,saima ƙara saka ta kogin ɗimuwa,yasa inno sauke ajiyar zuciya tareda dafa kafaɗarta
"Kiyi shuru ya isa haka to kukan,ki kwantar da hankalimki,inshaallah babu abinda zai faru,daga ni har sabin ƴan uwanki a shirye muke da mu tarbeki a cikinmu,sannan mu saurari kukanki,a duk lokacin da kika yi ra'ayin sanar da mu,in allahh ya kaimu gobe zan yi ƙoƙarin sanar dake wasu addu'o'i kafin a salak8 kema a islamiyyah."
Ɗaga kai khamriyyah tayi,alamr taji abinda innon ta faɗamata,sannan ta koma ta kwanta tareda rufe jikinta ta mayafi.
Juyowa wajenmu inno tayi tareda yimana magana muma,ganin yanda mukayi tsuru tsuru muna kallonsu
" yanzu dare ya fara ku samu ku kwanta gobe da makaranta."
"Toh"
Shine kawai abinda bakimmu yasamu ƙwarin gwiwar fada.
Da safe tashi mukayi har khamriyyan kaman babu abinda yafaru jiyan.
Shirin mu mukayi kaman kullum cikin kayan makarantar tamu,har zan fita zuwa wajen karyawa khairi ta riƙe hijabina ta bayah.
"Wlh baki isaba sabrah,haka kawai jiya ki sakawa hijabinki manja shine yanzu kuma ki ɗauki nawa,wlh ki ciremin"
Juyawa nayi na kalleta,duk da nasan banawa bane,ammafah babu alamar zan karbi laifin ko kuma na cire hijabin saima ƙoƙarin ƙwace riƙon datakemin nakeyi.
"Dallah ki sakeni,a gidan uban wa na saka manja a hijabinnawa,wannan ne nawa,saidai idan ke kika saka manjan"
Faɗa muka fara har hijabin yana ƙoƙarin yagewa,inno ce ta fito daga ɗakinta da ɗan ƙaramin yaro a hannunta wato Abdoul wanda take riƙo,ɗaya hannunnata kuma da naira goma guda biyu na taran mu.
Sakin baki tayi tana kallon yanda muke ta faɗa bayan ita kuma tana ciki tana nemo mana kuɗin break fast..
Ranƙwashi ta saki mana a kai kowa guda ɗayah,take kuwa khairi ta fasa ihu tana tsaramata abinda nayi mata.
Kallona tayi nayi saurin kauda kai ina jiran mai zai biyo baya.
"Hmmm wai sabrah nikam wannan faɗannaki na rashin gaskiya yaushe zaki daina ne?"
"Ba nata bane hijabin nawa ne fah inno"
"Wlh ƙarya take,ga can nata ita taci ɗan malele a wajen su Umaimah,ni banci ba"
"Yi shuru nasan ita taci ai,to cire hijabin ki bata,ki dau naki ki saka,wani ne yahana ki kaishi wajen wanki,gashi yau monday,kai sabrah allah ya shiryeki"
Cun'buna baki nayi bayan wulga mata hijabunnta,tareda fasa kuka ina zama a wajen.
"Ni wlh to inno bazan je makaranta da nawa hijabinba,malam Ɗahiru dukana zayyi, koroni zayyi kona jema"
Hijabin khairi ta ɗauka ta saka tareda ƙarbar nata kuɗin tayi waje,tunda an ƙwata mata hijabinta shikenan.
Shigewa ɗaki inno tayi bayan ta zabga min harara,alamar aiki bai isheni ba.
Bayan tashige nikuma tsayawa nayi ta burburwar ganin yanda khamriyyah ta tsiramin ido tana kallona,ashe tun sanda muka fara faɗan ma tana ɗakin tana kallommu,amma baxaka ce da mutum a wajen ba.
"Meyasa kika yi shuru kina kallonmu"
Banyi zaton zata amsamin ba sai naji tayi magana
"Saboda sha'awa kuke bani sosai"
Tunani na tafi a raina,
"Sha'awa kuma,muna faɗa kice sha'awa?"
Bata mayarmin amsar ba inno tafito daga ɗakin tareda kallona
"Dallah tashi ki ciremin kayan nan inba so kike kiyi datti dasu ba,dama burinki kenan ki zauna a gida ai,in kika kuskura baba shehu ya ganki baki je makaramta ba bada ke zayyi ke kika sani"
Jikina ne yayi sanyi,dan na tsani jin an ambata min kalmar za'a bayarni.
Tashi nayi na cire riga da wandon na mayarda doguwar rigata wacce na cire.
Komawa nayi kan kujerar da khamriyyah take na zauna mun kallon juna.
"Khamriyyah meyasa bakya yin magana sosai?...."
"Saboda bana buƙatar yin hakan,idan naji buƙatar hakanne nakeyi,saidai bawai buƙatar hakan yana daga cikin abinda nake so bane,saidan yana daga cikin kaɗdarata"
"Ƙaddara kuma?....meyasa kike magana kaman manyan mutane,kowani babban ma da ƙyar zai gane"
"Kamawa tayi shiyasa,sannan yawan magana ko yin magana bashi yake sakawa ka iya magana ba,saidai idam ita maganar tasoka da iyata"
"Amma....."
"Sabrah ke kuma kin kasance mai yawan tambaya sannan da manta damar da kike da itah rahama ce.
Duk da kina gidan marayu amma kuma kinada uwar da ko ita ta haifeki iyakaci,kina da ƴar uwar da kuke jini ɗaya,sanann kinada kwanciyar hankali babu fargaba,uwa uba sunada muradin baki ilimi wanda zakije ki dawo kina gaban idonsu,meyasa kike wasa da hakan?..."
"Kin ban mamaki,yanxu fah kika ce muna burgeki da muna faɗa,yanzu kuma kina cewa meyasa mukeyi?"
"Kina burgeni saboda kin samu damar yin faɗa da ƴar uwarki,kina ban takaici saboda kin bari kina faɗa da ƴar uwarki"
"Kinada abin mamaki,dole kiyi shuru,dan idan kikayi magana babu mai cewa ke yarinya ce"
"Kema kinada abin mamaki da kika kasa tambayata meyasa banawa kowa magama saike kaɗai"
Shuru nayi sai a sannan ma nayi tunanin hakan,bata yiwa kowa magana ba saini kaɗai meyasa toh.
"Meyasa toh?..."
Ƴar dariyah tayi kafin tace.
"Karki damu haka kawai nake jin na yarda dake,amma maƙasudin dalilin hakan,bazan iyah faɗamiki ba,dannima bansan shiba tukunna"
Rasa abinda zance ma nayi,dan gaskiyah wannann akwai wani abu tattare da ita.
"Menene a rayuwar taki toh da kike cewa na more.....kodayake manta kawai kince bakyason yawan tambaya"
Suna cikin magana ne,inno tafito daga ɗakin.
"Tunda bazaki je makarantar ba ai saiki jata ku zagaya koh,ko kina nufin yau a nan zaki yini kai"
Tashi nayi na miƙa mata hannu takama muka yi hanyar fita,dan dama sonake mu fitan,ina tsorone kar inno tace nayi shishshigi.
Sashen maman yara muka fara zuwa,bamu daɗe ba muka fito,dan ma mun ɗan tsayah munci ƙosai data bamu,daga nan sai mukayi hanyar sashen hajjah.
Turuss nayi har sannan muna sakale da juna na kalleta.
"Kiyi a hankali,hajjah faɗane da ita sosai,zata iya kai miki duka ko kuma tayi ta miki faɗa,amma karki du tanada ɗan kirki,idan muna zaune zaki gane hakan"
Ɗaga min kai tayi bayan tagama jin abinda nace,daga nan jata muka shiga ciki.
Da sallama na shiga falon da ƙarfi,anty juwairah ce ta tashi da sauri daga kan kujerar datake kawance ta rufemin baki
Magana tafarayi cikin murya ƙasa ƙasa,har sannan hannunta na kan bakina,
"Kehh yi shuru haka,hajjah tana bacci,batada lafiya magani tasha,idan kika tasheta kinsan sauran"
Ɗaga kai nayi kafin ta cire hannun ta akan bakina,gyara bakin nayi kafin na gaisheta.
"Anty juwairah ina kwana?"
"Lafiyah kalau wanann ƙawar takice kenan? Sabuwar ƙanwata"
Tafaɗa dana ƴar dariyah idonta na kan khamriyyah,itama khamriyyam murmurshi tayi kafin ta gaisheta kaman yanda nayi.
"Ke wai tukunna ma,meyasa bakije makaranta ba dukka sun tafi,ko dan ankawo miki sabuwar ƙawane,kefah dama in kika samu abu sabo..."
"Ahah anty ba haka bane,manja na shafa a hijabin kuma ba'a wanke shiba shiyasa"
"Hmmm in ɗan kamfaine ai kin iya kawowa na wanke miki,dayake hijabin makarantane sai kice kin manta,kuzo muje waje haka karmu damu hajja tana bacci"
Tashi anty juwairah tayi ta fita muma mukabi bayanta har bayan gidan,inda muke shanya kuma ƴar bishiyoyi suke,ear piece ne a kunnenta tana tafe muna binta har muka je wajen wasu kujeru na dutse,zama tayi muma muka zauna.
Cire abin kunnen nata tayi tana kallon mu ,musamman na khamriyyah hankalinta yafi komawa kanta.
"Dagaskene sunan ki khmariyyah,kokuma ƙaryar sabrah ce"
"Eh .....inaga sunana ne,koba nawa bane ma ina son yin amfani dashi tunda bansan nawa ba"
"Kaman ya baki san naki ba,a ina kike kafin a kawoki nan wajen"
"Bansani ba,ina rayuwane amma bansan wace kala ba,lokacin data faɗamin sunan naji ina sonsa sosai"
"Kinada abin mamaki sosai,sannan daga gani kin fuskanci kaɗaici a rayuwarki da dama,saidai ina so kisani zamu kasance a duniyarki,bazakiyi kaɗaici ba daga yanzu"
"Nagode anty juwaira,nima zan ɗaukeku tamkar ƴan uwa na jini,nayi alkawarin yin komai domin faranta muku da kuma yarda daku kaman yanda kukayi min"
Rugumeta anty juwairah tayi tareda jin daɗi maganarta,dan kaman yanda nake jinta a raina haka itama anty juwairah n.
Mun daɗe a wajen muna zaune,wani lokacin mu tashi muyi wasa mu dawo,ko kuma ita anty juwairah da dunga bamu labarin makarantarsu,dan hutun jss suke har yanzu mai tsayi,basu koma ba tukunna.
Washagari dole na tafi makaranta tunda inno ta wanke min kayan,kuma da gargaɗeni da kada na sake zama a gida banje makaramta ba indai inaso naci gaba da zama tareda su.
Tunda ga ranar anty juwairah ce takasance tana jan khamriyyah a jiiki,idan muka tafi makaranta takan zuwa wajenta ta koyamata abubuwa da dama.
Idan muka dawo kuma a yita wasa,har zuwa lokacin tafiya islamiyyah,dayake satinta ɗayah aka sakata a islamiyyar itama.
Lokaci da baifi wata guda ba mukayi wani sabo da ita sosai,musamman ma anty juwairah wadda take yini da ita a kullum,dama kuma gata mai son yara da haƙuri,sai hakan yaƙara saka shaƙuwa a tsakaninsu.
Hutun su anty juwairah ne ya ƙare bayan wata ɗayah da satuka da zuwan khamriyyah,yazama dole ta koma domin ta cigaba da karatunta.
Ana gobe zata tafi muna zaune a sashen hajjan wajenta inda take haɗa kayan makarantar,dan motar safe zata bi ta koma.
Dukkanmu munyi jugum muna kallon ta,itama da alama jikinnata yayi sanyi na barin gidan.
Khamriyyah ce ta rarrafa tareda kama bakin jakar tana tayata zugewa,fuskarta duk tayi wani iri da tafiyar anty juwairah,kallon ta anty juwairah tayi tareda dafa kafaɗarta.
"Karki damu kinji babbar ƙanwata,wata uku kawai mukeyi mu dawo,yanzu zakiga lokacin yayi na dawo,zamu cigaba da karatun mu a lolacin,kafin sannan ga nan ƴan uwanki ku cigaba da zama dasu kuna wasa kinji"
Daga kanta tayi hawaye yana bin kuncinta,a yanda na kulada ita iyah anty juwairah kawai ta fi sabawa da itah sai kuma nida inno da khairi.
Deen ma wani lokacin zakaga suna magana dashi jefi jefi.
Washagari muna gani anty juwairah ta shiga mota ta tafi,ba kaman ko yausheba wannan karon nafi damuwa da tafiyar tata,saboda nasan yanzu khamriyyah zata zauna a gida ita kaɗai.
Da daddare bayan munci abinci muna zaune a ɗakin inno an saka fitilar ƙwai a gaba muna bada haddar izu ɗayanmu,dan ganin makarantar basuda tausayi wajen duka yasa inno take biyamana kafin muje mu bayar.
Abin mamakin biyawa ɗayah akewa khamriyyah takawo tass,kaman dama tayi haddar wajen,saidai kuma da inno tambayeta cewa tayi batayiba,duk da abin da mamaki amma kuma Allah ba irin mutanen daya baya halitta da kuɗirar sa.
Bayan mungama karatunne na kalli inno tareda yi mata magana.
"Inno da an saka khamriyyha a makarantarmu,tunda anty juwairah ta tafi iyah ita kaɗai zata zauna a gidan kawai"
Shuru inno tayi tana kallona kafin tayi min hararar wasa.
"Uhm wanann,kin faye iyayi,to dama munyi maganar da baba shehu,har yafaɗawa shugaban makarantar ma,gobe zata fara zuwa,zasuyi mata interview sai su bata aji"
Tsalle nayi na ɗale inno kafin na komo wajen khamriyyah na faɗa kanta muka zube a wajen muna dariyah.
Itama dariyar take da alama taji daɗin hakan sosai.
Haka muka kwana muna labarim makarantar dakuma mutanen dazamu hadata dasu washagarin
Da'akayi mata interview bata wani ci sosai ba amma dayake tana da ilimi kuma primary ne sai aka barta kawai a ajinmu,wanda hakan dama mukeso dukka.
Tafiyah tayi tafiyah wasa wasa khamriyyah tayi shekara guda da zuwa cikin rayuwarmu,duk wanda ya ganta bazaice itace a shekarar bayaba.
Tayi kyau tayi ƴar ƙiba,duk da jikinta ba mai nuna girma ne sosai ba.
Ance saika zauna da mutum kake gane halinsa,hakane wannan maganar,kaman yanda nakeda tsokana da kuma son mutane,surutu da kuma masifah.
Ita kuma khariyyah tanada sanyin zuciyah da kuma rauni ba kaman mu ba gaskiyah.
Yayinda shikuma deen yake da wasa da dariyah,duk da cewa baikaimu a haifeba amma kuma yanada tsayi sosai.
Ita kuma maryam shuru ne da ita da kuma zurfin ciki. Idan anyi mata abu saidai tayi dariyah kawai.
Duk cikinmu khamriyyah tanada wuyar sha'ani,duk da tayi shekara tareda mu amma har yau babu wanda yagane ainihin cikinta da halayyarta,tanada nutsuwa da lura akan abu kafin tasan wane irin mu'amala zatayi dashi.
Wani idan ya ganta zaice sanyin rai gareta da haƙuri,amma haƙiƙanin gaskiya takan share abune idan bai kaita bango ba,amma idan har abu yabata mata rai to tanada zuciya da kuma ɗaukar mataki.
Wannan dalilinne yasa kowa ke shakkarta a ajinmu,sanann za'ayi mata abu ta shanye amma banda jurar taba ɗayanmu ko kuma cemana ƴan gidan marayu,wannan bata ɗaukar so koda wasa.
Wani lokacin idan ana faɗa ita su khairi guduwa suke,nice nake ɗan tsayawa najata mutaho gida.
Haka rayuwar tamu ta kasance har muka zana jarabawar shiga matakin secondry ƙarama.
Da gudun mu muka shigo gida muna murnar gama zana jarabawar,kowa yana ihu da murnar zamu shiga muma secondry.
Turus dukkanmu mukayi ganin wasu mutane biyu mace da na miji,sun ɗan manyanta,da alama mata da mijine.
Kallon mu suke ɗauke da murmushi a fuskarsu.
Hajjah nagani tayi shuru da itah,da alama a sashen ta wannan mutanen zasu ɗauki yaro.
Tantama tace ta share kuwa danaji maganar da baba shehu yakeyi,dama inkaga sabin mutane a gidannan toh wani za'a ɗauka a cikinmu.
"Toh kungansu nan yaran sun dawo daga makaranta,duk da sun ɗan girma amma basu wuce ɗauka ba har yanxu"
Faɗaɗa murmushinta matar tayi,jin abinda baba shehu ya faɗa
"Hakane kam gasunan mashaallah,to wacce ce maryam a cikinsu toh"
Tafaɗa tana ƙare mana kallo domin gano wacece maryam ɗin
Dukkan idon mu sauƙa yayi akan maryam ɗin wacce tayi wuƙi wuƙi,tana kallon mutanen.
Haƙika har a raina banason rabuwa da itah,saidai kuma ina yimata murna da samun wanda zasu ɗauketa a rayuwar nan kuma si kula da itah,musamman danaga alamar mutunci kwance akan fuskarsu.
Kuma dama ance labarin zuciyah a tambayi fuska,duk da wani lokacin kansa labarin daba shine daidai ba akan fuskarta su.
Jawota baba shehu yayi tareda turata gaban matar,ganin hakan yasa ta tsugunna daidai tsayinta,zuwa lokacin duk murnar data ɗebo daga makarantar ta zubar da itah,sai hawaye daya fara taruwa akan fuskarta.
Share mata hawayen tayi tareda yi mata murmushi wanda yake nuna kada ta damu komai zaizo da sauƙi.
"Ki kwantar da hanlinki inshaallah komai zai daidaita,munyi miki alƙawarin zamu riƙeki tamkar yanda zamu riƙe wanda muka haifa.
Duk da cewa Allah bai bami haihuwa ba,amma kuma hakan bai hanamu sanin ya soyayyar samun ɗa take ba,mun sameki inshaallah zamu riƙeki yanda ya kamata maryam.
Muna fatan kema zaki riƙemu tamkar iyayenki"
Ɗaga kai tayi tana share hawayenta,alamar taji abinda tace ɗin.
Tashi tayi tareda kallon hajjah wanda aka ce itace mariƙiyarta.
"Mungama dama cike ciken takardar jiyah,yanzu muke son wucewa da itah cikin garin katsina,saboda akan hanya muke"
"Toh ba matsala,dan allah ku riƙeta da amana,batada matsala ko kaɗan,yarinya ce mai nutsuwa"
"Karki damu zamuyi iya ƙoƙarin mu sosai"
Kayan maryam ta miƙo,dan dama tariga ta haɗa kayan tunda safe.
Muna tsaye munyi soƙoƙo bama cewa komai,abin yabamu mamaki sosai,tashi ɗaya mun shigo da murna tare,lokaci ɗaya ita kuma za'a tafi da ita.
Kallon mu take lokacin da matar ta kama hannunta suka fita daga gidan,binsu mukayi a baya cikin sanyin jiki,muna gani har suka shiga mota suka ƙulewa ganinmu kafin muka dawo gida.
Murnar da muka shigo munayi na gama primary lokaci ɗaya ta koma ciki,kowa a cikin mu yayi jugum,cin abincima ya gagaremu,a duk lokacin da aka ɗauke ɗaya daga cikinmu a lokacinne muke tunawa da matsayinmu,wanda ba ɗaya yake da yaran da suke gidan iyayensu ba.
Haka muka gama jimamin rashin ƴar uwartamu har muka daina,ganin duk abinda zamuyi bazata dawo ba ta tafi kenan.
Zaman gida mukeyi kafin a sama mana makarantar sazamu tafi,sai murna muke dan munsan makarantar kwana za'a kaimu kaman sauran yaran gidan.
Kwatsam sai mukaji baba shahu wai bazai kaimu makarantar kwana ba a gida zamuyi,roƙonsa mukai tayi amma ya ƙeƙasa ƙasa yace bazamuje ta kwana ba a gida zamuyi.
Shirye shiryen tafiya makarantar muke har an siya mana uniform,shikuwa deen muna gani aka yi masa siyyah na kayan makarantar kwana zai tafi.
Kallon khairi nayi wacce take zaune tana kallon maman yara tana yiwa deen shirin tafiyah makaranta,an siya masa abubuwa zai tafi mukuma bazamu je ba.
"Wlh baba shehu baya kyautawa miye zai wani ce bazamujeba banda mugunta,ni wlh makarantar kwana nakeso "
Tafaɗa tana matse idanu,nidai kallonta nakeyi nida khamriyyah,wacce ta gimtse dariyarta ganin abinda khairi takeyi.
"Hhhhh yanzu khairi saboda sakalci dan bazaije makarantar kwana ba sai fara kuka?"
"Eh ɗin ina ruwanki toh,kuma nace kuzo muje muyi masa kuka ina kun ƙi zuwa"
"Kutt an gaya miki kowa irinkine,ba inda zanje"
Khamriyyah ta faɗa tana sake shƙewa da dariyah,wanda yaƙara ƙular da khairyyah.
Bayan wata guda da tafiyar maryam shima deen ya tafi makaranta,yazamo sauran mu uku kawai a sa'anninmmu,har sanann bamu fara zuwa makarantar da baba shehu yafaɗa zamu je ba,muna nan muna ɗan aikace aikace a gidan,tunda yanzu mune manya mata,anty juwairah tana makaranta.
A zaune muke muna cin abinci suwaiba wacce itama a wajen maman yara take tazo ƙiranmu mu ukun.
Gabana ne ya faɗi rass ganin mutane biyu mace dana miji,ko ba'a faɗaminba nasan mai ya kawosu sarai,dan abune da duk wani yaro na gidan ya sani,indai kaga mutane a gidan to wasu zasu ɗauka,yaran dun ƙarene har an zo kanmu ko me?...
Katsewa nayi da tunanin jin mutumin yana cewa,
"Eh gasunan kam ƴan biyune yanda kace,saidai guda ɗaya muke so zamu ɗauka daga cikinsu,wacce tafi farin siririyar zamu ɗauka"
Kutt mai suke nufi,ai khairyyah zasu ɗauka,ina bazan iya rabuwa da ita ba,inno ma bazata iya ba.
Jijjiga kai na farayi har sanda aka ce mushiga cikin gida,zasuyi magana,kafin azo ɗaukarta.
Tun daga bakin ƙofar khairi take zabga uban kuka kaman ance mutuwa zatayi,nasan bana komai bane sai rabamu da za'ayi da ita.
Kallonta nake amma banida ƙarfi ko ƙwarin gwiwar cewa tayi shuru,har muka shiga sashen namu wajen inno.
Lokacin da labarin ya doki dodon kunnenta tashi tayi zumbur ta miƙe tana salati ,riƙo hannun khairin tayi tana dafa bayanta,daga cikin idonta zaga hango tsagwaron tashin hankali a ciki,da kuma fargabar rabata da za'ayi da khairin.
Duk abinda ake dagani har khamriyyah babu wanda yace komai,saima kallonsu tamuke ganin yanda ta ƙaƙume inno tana zabga kuka.
Wulgawar khamriyyah nagani tashiga ɗakinmu,bata daɗe ba sai gata ta fito da jakar kayan ta a hannunta.
Duka kallonta mukayi da mamaki,har wacce take kuka shuru tayi tana kallonta.
Inno ce tasami ƙarfin gwiwar yi mata magana.
"Khamriyyah yana ganki da jaka ina zaki tafi haka?"
"Inno binsu zanyi,zanje na faɗa musu su tafi dani su ƙyale khairiyyah,bazan iya jurar ganin sun rabata da ƴar uwarta ba,ko kuma su rabata da mahaifiyarta ba,wacce take sonta tamkar ita ta haifeta"
"Amma.....khamriyyah baki daɗe da zuwa nan wajen,har yanxu kina buƙatar wanda zasu ɗebe miki kewa,kuma kinga bamu san halin da suke dashi ba,karki koma gidan jiya"
Matsowa nayi kusada ita nima tareda dafata,tayi mana abubuwa da yawa,bai kamata bayan halin data shiga kuma tasake jefah kanta wani ba saboda mu.
"Eh hakane khamriyyah bai kamata ki tafi ba bayan baki daɗe da zuwaba,sannan baki san wane kala bane,indan ta khairyyah ne karki damu da itah ni zan bisu su tafi dani in......."
Saurin rufe mata baki khamriyyah tayi tareda jijjiga kai.
"Kinfaɗi dalilin daya sa zan bisu,idan harke zaki tafi kibarta menene dalilin hakan toh,komin yanda zaki buƙaci wani a rayuwarki baikai ya ita ba,koda na barki kin tafi kina tunanin zaki ciresu daga rayuwaki ne?,kin manta abinda na faɗa miki lokacin dana ganku kuna faɗa,nafaɗa na ƙara faɗa kuna burgeni sabrah,kuma zan iya komai indai zan iya wajen ganin kun kasance tare.
Zan tafi amma karki damu,ba kaman sauran yaran dasuke tafiya na ni zan dawo gareku,dan nan wajen yazama tamkar gidanmu inda aka binne cibiyata haka nake jinsa,kaman yanda nayi alƙawarin zam ɗaukeku tamkar ƴan uwana hakan bazai sanja ba ina kan baka ta"
Matsawa tayi kusan inno inda suke zaune itada khairi.
"Inno ke mahaifiyata ce,kuma har duniya ta naɗe bazan daina ganinki a hakan ba,kin rungumeni keda sauran yaran da suke wajennan,baku ƙyamceni ba,sanda nake buƙatar taimako kunyimin,dan haka nima bazan so ganin rabuwarki da ƴaƴanki ba,nice yakamata na tafi ba ɗaya daga cikinsu ba.Zan tafi ina muku fatan alkhari"
Har ta kama hanyar zuwa office ɗin baba shehun na bita tareda rungumeta ta baya,waye zai min haka inba khamriyyah ba,ta kwammaci tayi komai akan su rabani da ƴar uwata,batasan itama banason rabuwa da ita ba,domin ta zama tamkar wani sashe na jikina.
"Khmariyyah idan kika tafi keɗin kina tunanin zaji daɗi,anty juwairah ma datake makaranta bazata ji ɗadi ba idan ta dawo bata ganki ba"
"Nasan bazakiji daɗi ba,haka itama anty juwaira bazata ji daɗi ba,amma rashin jin daɗinku shine zai tabbatarmin dazanyi ƙoƙarin dawows ku jirayeni zan dawo gareku,dan mun zama ɗaya"
Baba shehu ne ya shigo daukar khairiyya da kayanta sai kuma yaga khamriyya riƙe da jakar kayan ta da'aka siyo mata,tun kafin yayi magana ta tura ni bayanta tareda kallon baba shehun
"Baba shehu nice zan bisu ba khairiyyah ba"
"Ke kuma?amma ai ita suka zaba,wanda suke so ai ita zasu ɗauka"
"Amma saboda ita sukeso shikenan saisun ɗauketa kodah za'a rabata da ƴar uwar da ita kaɗai tarage mata,haka kuma ga mariƙiyarta wacce takejinta kaman ƴar ta? A tunani na muba bayi bane ƴan tattune,ahali na jini kawai muka rasa,hakan bai kai a maidamu marasa galihu ba,indai kai ka yarda to nice zan bisu ,idan basa buƙata toh suje wani wajen"
Yanda ta tsayah tana zanzaro masa bayani babu alamar tsorone yasahi shan jinin jikinsa,tabbas gaskiya ta faɗa,su bazasu ɗauki duka biyun ba saidai su ɗau ɗayah,koda hakan na nufin rabasu ne.
Karkata kai yayi tareda cewa
"Shikenan hakane kam,zo muje toh,idan sun amince saiku tafi,idan kuma sunga basu aminceba shikenan sai suje wani wajen"
Hannun baba shehun ta kama suka fita,har sunje bakin ƙofah ta juyo ta kalleni.
Biyosu nayi a guje zan bisu office ɗin tayi saurin yimin alama na tsayah,nasan nufinta kar naje su ganni su ce ni zan bisu shiyasa ta hanani binsu.
Ina kallonsu har suka bacewa ganina,shikenan nayi rashin ƙawata sauran guda ɗayan itama,taya zam manta da itah,kaman yanda tace zata dawo anya kuwa zata cika wannan alƙawarin,nacewa zata dawo garemu.
Juyawa nayi na koma ɗakin mu na ƙwanta,duniyar nakeji tayimin zafi tana juyamin.
Ko yaushe zamu daina sabawa da junanmu ana ɗaukemu,kumafah dolene a ɗaukemu saboda wasu su sami inda zasu zauna suma.
.........hmmmm








Taku
_sadi-sakhan_
Ƴar mutan jama'are.

MABARACIYAHWhere stories live. Discover now