chp 9__10

157 3 0
                                    


       *MABARACIYAH*
          

_hakkin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
                                       
Chp link
https://arewabooks.com/chapter?id=62779565e4461fd926ec37da

Free page
9••10

Daurah_____5:00pm

Mutanene guda biyu mace dana miji zaune a bakin rafi suna hira,gefen ƙafarsu kuma ruwa yana wucewa,daga kallon yanda suke kasan suna jin dadin yanayin sosai.
Kallon mutumin dayake zaune a gefenta tayi,kafin ta sau ɗan sansanyan murmushi.
Doguwar rigace a jikinta baƙa,sai kanta ma ta nannaɗeshi da baƙin mayafi.
Wanda hakan yafito da jar fatarta sosai irinta fulani.
"Yah muzzanbil nayi mamaki danaga yanda kamaida wajenann,gaskiya wajen yanada tarina ni'ima,amma hakan fah rani yana zuwa zaku bar garin fah ku koma gun daban koh.
Yaushe za'a daina wannan tashi tashin na almajiraine?inaga kuma lokaci yayi dazaku zamanta tsarin karatunku nan"
"Lallai ma deejah har yanxu kina nan da  ƙorafinki,yanzu idan muntashin menene zai shafeki a ciki"
"Babu komai,kawai dai kasan bazan biku bane,kodah yake ni wani satin ma fah nake son shiga cikin garin katsina,wannan hutun jakin da kaya akai ya isheni haka"
"Hmmm wai ke ba namijiba amma kina birkita hankalin manyan gari,nayimiki magana kibar wanann aika aikar amma sam kin ƙiji sam"
"Bazan iyah dakatawa ba saina gama tukunna,a lokacin dana gama zan fito kowa yasan nice,kafin zuwan lokacin nashiryah kallon tsagwaron tsana a idanuwan wanda nayi sanadiyyar mutuwar masoyansu,nikaina nasan abin akwai babbar wuyah idan lokacin yazo"
"Kwanaki kincemin na faɗamiki idan yadiko lami tazo ganin gida,to tazo jiyah a satinnan zata koma,maiyasa kike buƙatar zuwanta,wani abin kike ƙoƙarin shiryawa ko"
"Hhhhh kai ya munzanbill mai ka maidani ne,kafin nan inaso ka ƙarisamin bayanin yanda ake laƙanin karshennan,saboda inada buƙatar sa a cikin shirina"
"Deejah ina jiyemiki kiyi abinda zai jawo hatsari ga rayuwarki fah,wanann abin yakamta ki tsayah iyah haka"
"Kayi haƙuri yah muzanbilu,nayi maka alkwari daga wannan nadaina bazan sakeba,amma matar sarkin katsina hajiya fulani babu mai hanani illatata koda ban kasheta ba saita ƙwammaci a kashetan"
Saurin zaburah muzanbilu yayi ya tashi tsaye tareda sunkuyowa yana kallon deejan,wacce ko a jikinta kaman ba ita tafaɗa ba.
"Deejah!mai kika ce,naji kunnena yajiyo min wani gagarren aiki,mai kike nufi da hakan"
"Basai ka tambayeni ba,lokacin da aikin ya kammala zakaji a kafafen yaɗa labarai cewar mabaraciyah ta kashe matar sarki Alhaji Bilyaminu muhammadu, ta farko wato Hajiyah Fulani Ateekah."
Wannan shine aikina na karshe akan manyan gari,daga nan kuma sai kaɗa hantar  masu bincike kawai"
Tunda tafara maganar munzanbilu yasaki baki yana kallonta haƙiƙa yanzu tafara bashi tsoro,anyah kuwa itah ce wacce yasani tana yarinyah.
"Wayyyo jina nake kaman tsuntsuwa wacce ta fito a cikin keji,bayan shekara guda zanje aiki,hmmmm masu bincike da V-ladies ya zakuji inkuka yi arba da aikin MABARACIYAH wanann karon,yah muzanbilu kaidai kafaɗawa yadiko lami zam bita masarautar katsina inda take aiki idan ta tashi tafiyah.
Daga nan sai aiki yasoma"
Shigewa cikin gidan tayi tana tafe tana rera waƙa hankalinta kwance.

      *______*________*_______*

Zabga mata mari yayi har saida jini yafita a cikin bakinta,
"Ogah yace muyi ta dunkanki harsai kin faɗin gaskiyah,har yanxu bazaki faɗi abinda kuke aikatawa ba koh,yau kwana uku amma kinƙi cewa komai kega mai taurin kai koh."
Duk dukanta dayakeyi babu abinda tace,saima ƙara tamke bakinta datayi,alamar b'ata lokacinsa kawai yake.
Yana cikin dukanta ne dec. Sadeeq yashigo wajen,cell ne na ƙarfe,a wani waje killacecce da alama sai ana son tambayan wani mai babban laifi kafin akawoshi wajen.
"Har yanxu bazakiyi bayani ba baiwar allah,dan kinga muna miki sako sako,to ki sani akan wannan case ɗin zamu iyah kasheki,kinsam tsawon lokacin damuka ɗauka muna neman koda karamar sheda akan wannan case,ɗin sai gashi tashi ɗayah mun samemi,ina so ki faɗamin mainene haɗinki da wannan logon na hoton macijiyah da muka gani a cikin laptop ɗinki,shine desame logo da aka samu a jikin gawar dr. Bukar.
Sannan tsawon shekara guda ana mana hacking,bamu taba ankara ba sai wancan watan,wanann dalilinne yasa muka saka virus a website ɗin,abin mamaki kuwa saigashi mun sameki da neman mai gyaran irin wannan virus ɗin,hakanne yasa muka tura wani ma'aikacinmu yaje ya gyarah,yasaka alama a web ɗinki,wanda kina sake ƙoƙarin shiga web ɗinmu sunanki da inda kike zai nuna,abin mamaki kuma da ID ɗin ɗayah daga cikin ma'aikatanmu ake shiga tsawon shekara gudan,wanda kin boye information ɗin ID ɗin,duk yanda akayi muna da spy a cikin headquater ɗinnan bamu saniba.
Inaso ki faɗamin wacece ke,sannan meyasa kike aiki damasu kashe kashen nan,nasan dole ke ɗaya daga cikinsu ce"
Ɗago fuskarta khairiyyah tayi waccd ta sanja kamanni ta kalli dec. Sadeeq,ɗan ƙaramin murmushi tayi na ƙarfin hali kafin tace,
"Babu amfanin faɗamaka tunda iyah bayanin daka samo kenan,dan koda na faɗamaka ba lallai ka ganeba,dan haka zai fi kyau kayi haƙuri da iyah saninka"
Wani babban mutum a gefe bai bari ta gama magana ba ya gwabza mata duka,faɗuwa tayi akan gwiwoyinta saboda tsabar jifata datayi daga azabar dasuka gana mata a tsawon sati gudan.
Buɗe ido tayi tana kallon cikin idon dec. Sadeeq ɗin  bayan tasake tsayawa akan gwiwoyinta,da alama har sannan zuciyarta bata karaya ba.
"Shin ke yarinyar mabaraciyah ce?"
"Ya danganta daga yanda ka ɗauka,kawai amsa ce bazaka samu a wajena ba,kaman yanda ka taba kama ɗayah daga cikin yaran mabaraciyah ka kasa samun amsa"
Zaro ido dec. Saddeq yayi,da alama bayyi tunanin tasan binciken dasukayi akan wata yarinya shekara ɗaya data wuceba.
Bindiga ya fitar daga cikin aljihunsa ya nuna akan khairiyyan.
"Har yanzu bakaji abinda waccer yarinyar ta faɗamaka ba,bazaka samu  amsa daga irin muba da barazanar bindiga,saboda mu bada kuɗi aka sayemu ba,ka gane hakan mana"
Zefar da bindigar yayi tareda cewa
"Kinsan bazan kasheki ba saboda ina buƙatar bayanai,amma hakan bazai hana na hukuntaki ta mummunar hanya ba domin samun amsar danake nema ,ki jira dawowa ta,kafin sannan ki tabbatar kim tanadi amsoshin dazaki bani kafin ki rasa yatsunki na hannu dana ƙafa"
Ƙarar wayarsa ne yasa shi fita waje domin amsawa.
"Hello khaleel ya aiki da kuma kasar china?"
"Lafiya ƙalau,amma babu daɗi ko kaɗan,na gama karatuna Allah Allah nake nadawo gida nima,saidai naga kaman da alama so suke suce nayi aiki anan kasar,nikuma hankalina gaba ɗaya yana kanku.
Kayi kewata ma kuwa?"
"Hmmm kajika da wani zance,kasan a duk ranar duniya sainayi kewarka ai"
"Nasan da haka shugaban masu bincike,ya wannan aikin dakukeyi ne,har yanxu baku samu nasarar kamata ba?"
"Har yanzu dai da saurah,saidai yanzu munkama ɗayah daga cikin yaranta"
"To karfa kuyi wasa ta gudu irinna wancan lokacin,ni nayi zargin ma ina ga fah akwai wanda yake musu aiki a cikinku,shiyasa suke samun labaranku da shirin ku cikin sauƙi"
"Eh nima nayi zargin hakan,yanzu inshaallah zamuyi yanda ya dace,yaushe zaka dawo kenan"
"Hhhh inga nan da wani satinma idan nayi nasarar ƙar'bar takardata to zaka ganni a gida nigeria,barina kashe karna dameka da surutu kana kan bincike,sai anjima ko mai bincike,a gaishemin gimbiyah,kace mata tashirya ganin ƙaninta lokacin farko"
"Hmmm ƙaninta kuma,yau kuma abinda ka ɗauko kenan,kowa ya ganka ai yasan ka girmeni"
"Hakadai kace,sai anjima"
Ƙitt yakashe wayar yabar dec. Sadeeq da kallon screen yana murmushi.
Shukarah ce tazo da file a hannunta da sauri tareda miƙawa masa,
"Ogah intargilent section sun bada shawarar ayi mata scaning ko akwai na'urah a jikinta,saboda duk wani abu da muke yanuna suna saneda hakan,wannan binciken ID ne da'akayi yafito,ansamo komai datayi yunƙurin 'boyewa"
Da farinciki Dec. Sadeeq ya ƙarbi file ɗin tareda buɗewa bayan yagama jin bayaninta.
Sunan dayayi arba dashi a jikin ID ɗin da'akayi amfani dashine yayi matuƙar girgizashi.
KHAMRIYYAH,mai kuma ya hada khamriyyah da wanda ake zargi toh.
Tsawon kusan shekara biyu duk da ID ɗinta ake amfani ana yi musu kutse,sun bi diddigi amma sun gagara gano waye yakeyi,saidai suga blank,wancan satin suka sanja computocinsu na tsaro babu wanda ya sani,gashi. Sun gano mai yake faruwa,hatta takardar da khmariyyah tatafi ƙarin karatu da ita wancan satij aka turata,gashi har ta shiga sahun masu tafiya a satin,kuma duk da tambarin viper akayi amfani wanda sune suke kasha kashen da'akeyi.
Cire glass ɗin fuskarsa yayi bayan yagama tattara bayanan waje ɗaya,kenan duk tsawon lokacin daya yarda da khamriyyah zagon ƙasa takeyimasa,kai hakan yake nufi,bata tunanin yarda zai ɗauki abin.
Baiyi wata wata na ya nufi sashen binciken nasu na na'urah dan har yanzu yagagara tantance bayanin.
Har yazo dab dazai shiga wajen saikuma ya fasa ya nufi inda khairiyya take a ɗaure.
To idan yaje wajenta ma mai zai cemata,faɗa mata zayyi yakasa gano wacce take yimasa zagon ƙasa na tsawon shekara biyu sai yanzu yagano ko me?
Hannuwansa yasaka tareda murza cikin kansa,dan ji yake kaman ƙafafuwansa ma sunyi masa nauyi,share tantama dai yayi tareda nufar wajen horon.
A ɗaure yasameta kaman ko yaushe kanta yana kallon ƙasa,motsinsa ne yasa ta ɗago ta kalleshi,ita kanta mamaki abin yabata ganin yanda kamanninsa suka sanja lokaci ɗaya,kaman wanda aka cemasa an yashe masa asusun banki.
"Kee inaso ki faɗamin bayan khamriyyah wacece kuma wacce take yimana bin diddigi,inaso ki faɗamin tsawon wane lokaci kuka ɗauka kuna wannan shirin,dame dame kuka kitsawa "
Cikin tsawa da tashin hankali yake maganar da alama hankalinsa baya wajensa.
Ƴar dariya khairiyyah tayi kafin ta ɗora da cewa.
"To danƙari,daga gano gaskiya ɗaya harka birkice haka,inaga inkagano wani daban,ina faɗa maka tun wuri zaifi kyau ka bar wanann binciken,dan ba'a kan kowa zai ƙare ba sai kanka,bazaka'iya jurar gane gaskiyaba idan ka cigaba da tonota nan gaba.
Hmmm dan kagano khamriyyah ba ma'aikaciya ce ta gaske ba babu abinda zaka iya da hakan,kawai dazai fimaka kyau kasan akalar bincikenka kan wani waje daban ba nan ba ,wannan shawara nake baka mai kyau"
Mari ya sheƙamata a fuska iya ƙarfinsa,dan daga gani yafara fita hayyacinsa,ga kuma ransa daya 'baci sosai.
Wata macece daga cikin ma'aikatannsa tayi saurin dakatar dashi ta hanyar bashi wayarsa da take ringing.
"Yalla'bai ga wayarka madam tana tana ƙirah"
Tun kafin ya ƙar'bi wayar har ta katse,bai bi ƙirannata ba sai ya shiga wayar ya nemo number khamriyyah,kallon sunan yayi yana tuna masa abubuwa dayawa kafin ya daure ya danna ƙiran.
Riniging ɗaya ,biyu tayi ya ɗaga.
"Salam ogah barka da rana ya aiki"
"Lafiyah ƙalau kin fara karatunne?"
"Eh na fara ogah yauma nashiga aji fitowa ta kenan"
"Okay toh ki dawo gobe inason ganinki"
"Ogah lafiyah zan dawo?,ko sati ban cika ba fah da tafiyah"
"Eh kidawo umarni nake baki,akwai wani abu mai muhimmancine da baxayyiwu a wayaba"
"Ogah zancen kama khairiyyah ne dakayi ko kuma zancen gano cewa nice nake haɗa komai?,wannne daga ciki zamu tattauna oga.
Karka damu oga inaga basai nazo bama,indai khairiyyah ce matuƙar zaka cigaba da bincike bazaka tsaya iya haka ba to ina mai tabbatar maka dakanka zaka jawo kanka abinda ƙwaƙwalwarka bazata ɗauka daidai ba,inada abinyi ogah a gaida madam saina dawo"
Lokacin data kashe wayar yana jin dariyar ta ƙasa ƙasa,lallai wannan matar ta wuce inda yake tsammani.
Wayar ya buga da tiles ɗin wajen,ta bada kara tatssss,duk abinda yake khairiyyah na kallonsa tana ɗaure,itadai ido nata kawai.
"Fareedah inaso keda ahmad ku shiryah min body scanning yanxu,ina tunanin akwai na'urah tabbas a jikimta wanda khamriyyah takejin mai ake faɗa,zan je office kafin sannan ku shiryah komai"
"Okay sir zamuyi yanda kace"
Fita yayi daga ɗakin horon da sauri yabar khairyyah itada fareedah a wajen.
Matsawa tayi gaban khairiyyan tareda cewa
"Sis sannu ya jikin?"
"Babu komai fareedah karki damu komai zai zo da sauƙi,tashin hankalin ɗayah shine ina tsoron su gano gaskiyar abinda muke 'boyewa fareedah,dan dukansu babu komai zan jure"
"Ahah bazai yiyu kiyi ta jurewa ba khairyyah,dolene musan abinyi kafin lokacin,da inada damar yi da yanzu zan fiddaki daga nan wajen,saidai hakan bazai yiyu,duk wani matakin tsaro yanxu akanki yake,fitar bazayyi yiyu ba,dole sai anyi scanning ɗin babu yanda zamuyi"
"Niba kaina nakeji ba idan anyi fareedah,sabriyyah nakeji bansan yazatayi ba,naga kaman anty khamriyyah tasan komai dayake faruwa,kece kika faɗamata koh?"
"Eh nice na faɗamata shikuma yayi zaton wai camera ce a jikinki,sai naji daban faɗamata da wuri ba"
"Ahah gwara dakika faɗamata ɗinma,kinga da yanzu tadawo dayace ta dawo ɗazu"
"Hmmm tun jiyah taso dawowa ai,wai a dole saita ƙwatoki daga hannunsa,su anty nawwarah ne suka bata baki dakuma shawara,saboda idan ta dawo abin 'baci yayi,inaga yafima da bata garin,da abin sai yafi haka 'baci sosai.
Kiyi haƙuri kinji khairiyyah inshaallah gobe muka tsara zaki fita anan wajen,barina je na shiryah scanning ɗin karyah zargi wani abun"
Tana gama faɗan hakan ta juyah da sauri tabar wajen,tana tafiyah tana waiwayen ƴar uwartata,da alama bataso barinta a wajen ba,saidan babu yanda zatayi da al'amarin.
Shuru dec. Sadeeq yayi a office ɗinsa tareda zuba uban tagumi,yarasa ma mai zayyi akan wanann abun.
Tukun takardun dake gabansa ya kallah wanda ya gagara taba su bare yin wani aikin,karar buɗe ƙofar yaji amma bai ɗaga idonsa yaga mai shigowa cikiba,dan ba ta wanann yakeba a yanzu.
Muryar ahmad yaji daya yimasa sallama.
"Sir an gama shirye shiryen ascanning ɗin kaman yanda ka buƙata kai suke jira su fara"
"Okay kace ina zuwa yanzunnan."
"Kayi haƙuri da abinda ya faru"
"Inbanyi haƙuri ba isaka zan tayar toh,haƙurin ai na dolene"
Tashi yayi yabiyo bayan ahmad din suka fito daga office ɗinnasa.
Wajenda ake scanning ɗin suka shiga wanda za'a gano wani abu a jikinka daka 'boye,
Har lokacin da za'a fara idon khairiyyah yana kan dec. Sadeeq,da alama batason abinda za'ayin,saidai kuma idan tace kar ayi hakan bazai tasiriba saima ƙara musu ƙaimi,dan zasu gano da 'boye wani abin.
Zaunar da itah akayi akan wata kujera sanye da wata doguwar riga wacce kalar ta bazai shafi aikinba
Na'aurar scaner ce tafara daga ƙasa wajen ƙafartah,a hankali zuwa saman ta.
Runtse idonta tayi lokacin dataji hasken na'urar a kan kirjinta,wanda hakan yaƙara sautin bugun ƙirjinta daga yanda ainihi yake.
Ƙarar da na'urar tayine yasa ta tabbatar tafaru taƙare kawai,babu kuma sauran wani komawa bayah.
Buɗe idonta tayi akan na'urar wacce ta nuna alamar ja akan saitin fuskarta,wanda hakan yake nuna kenan akwai abinda ta 'boye a fuskar.
Sauran mutane kowa kallon fuskartata yakeyi,dan da alama babu wani abu ba daidai ba,saidai kuma ruwa bayah tsami banza,dole akwai dalilin hakan.
Masu kulada binciken wajenne wata ta matso kusa tareda ƙarewa fuskar khairiyyah kallo,ɗan murmushi tayi da alama ta harbi jirgin abinda yake faruwa.
"Ƴar da alama kaman fuska kika sa,kika 'boye ainihin fuskarki ta zahiri,koba haka bane?"
Cikin sauri kaman wani zai rigata tabawa matar amsa da "ahah"
Faɗaɗa murmushinta tayi jin da alama hasashenta yazama gaskiya.
"Dec. Sadeeq mun gama maka binciken dazamuyi,yarinyar tana ɗauke da fuskar roba wanda ta 'boye ainihin tata fuskar,to yanzu aiki yarage naka ka gano shin ya ainihin fuskarta yake"
Duk abinda suke dec. Sadeeq kallonsu yake,yama rasa abin cewa akan lamarin,mamakin sa ɗayah shin suwaye su,suna mata amma suka san irin wanann hanyoyin,hadda wani shirin na rufe fuska,da ba'ayi ascanning ba kenan haka zai ɗauka wanann ce fuskarta,tana fita saita wuce ya wuce ta maidashi wawa,allah yasa ma uwar gayyar itama fuskarta kenan.
Musamman yanzu data san yaganota zata iyah cire fuskar tasake zuwa a matsayin wata daban.
Kai gaskiyar amrah ne daga yanzu bazai ƙara ɗaukar mace aiki ba har ya jawota jikinsa irin yanda yayi wa khamriyyah,anyi na farko baza'a sake kumawa ba k....
Ƙarar yatsun da ahmad ya kyastah a saitin fusarsane ya dawo dashi daga makahon tunanin daya tafi,kallonsa yayi na ɗan sakanni ya tariyo mai yafaru kafin yayi magana.
"Ahmad ku kaita izuwa ɗakin sirri,ban yadda wani yashiga ba bayan kai da kuma ma'aikatan wajen"
Amsawa yayi tareda fara aikin da'aka umarceshi,a randa yana tausayawa shugabannasu yansa ya rasa nutsuwar sa akan case ɗin gabaɗaya.
Ɗakin haske ne dashi sosai saikuma kujeru guda biyu kacal da tebur a tsakiyansu.
Na ciki baya ganin na waje,amma kuma wanda yake waje ta gaban glass ɗin yana kallon na cikin.
A zaune take ta sunkuyar dakai lokacin daya shiga ya zauna a kan kujerar da take kallonta,har sannan tana sanye da doguwar rigar da'akayi mata scanning da itah.
"Har yanxu bazaki faɗamin gaskiya ba duk da nagano kusan rabin gaskiyarki"
"Ai ba iyah rabi ka ganoba ma,ka gano babbar gaskiyar wanda nake jiyemaka ganota,yanzu idan nace karka sakani buɗe fusakata kaga wacece ni zaka yarda da zancena?"
"Hhh kin fara yanzu tsorone saboda kar aga ke wacece,da hankalinki kwance saboda idan kin fita zaki cire fuskar dakika yaudaremu da itah,yanxu kuma kina jin tsoron mu buɗe asirinki ya tonu koh,to kisani alƙadarinki ke ya karye yau kuma anan wajen zai ƙarisa karyewa,kokina so ko baki so saikin cire abinda yake kan fuskarki kowa yasan ke wacece"
Shuru khairiyyah tayi ta rasa abin cewa,saboda duk yanda zatayi masa bazai fahimta,ina amfanin baɗi babu rai dan haka kawai tasaka hannunta ta ɗaye gam ɗin daya haɗa fuskar da ainihin tata fuskar.
Idan taƙi cirewa ma zasuyi mata ta ƙarfi.
Duk abinda take dec. Sadeeq yana kallon ta har ta cire fuskar ta ajjye akan table ɗin.
Ɗago idon da tayine shikuma yayi dadai da zaburarsa ya miƙe a tsaye,dukkan jikinsa rawa yake lokacin dayake nunata da yatsarsa,magana yake son yi amma kuma bakinsa yagagara furtawa.
"Meye kake nuna ni toh yanxu,ka razana ne da ganina,saida nace karka tilastani cirewa amma kaƙiji na,toh yanxu ya kace sirikina?........"
"Amrah......"
"Hmmmm ji wani zance,amma dai kasan ka barta a gida koh,miye kuma kake ƙirana da sabriyyah,ohhh ashe da amrah kasanta kai bada ainihin sunanta ba.
To bari nayi maka gwari gwari kafin kaje tayi maka kyakykyawan bayani,wannan ƴan biyun(twin)sabriyyah ce khairiyyah,tun lokacin daka aureta fita da ainihin fuskata ya haramta min saboda kai,duk da wani lokacin nice a gidanka ba ita ba idan zan saka camerah ko kuma nemo bayanai,sannan kusan duk taron da kake zuwa da itah nice nake binka ba itaba,shiyasa kayi ta mamakin ya akayi bana magana idan munje wani waje,saidai nayi ta komawa gefe,kokuma na nemi uzurin zuwa wani waje.
Wanann shine dalili toh,yanzu kaji daɗi ka gano gaskiyah? Ko kuma har yanxu kawai gaskiyar da baka ganoba kake son sani.
Gaskiyar ɗayace khamriyyah ce take shiryah komai wato babbar ma'aikaciyar ka,yayinda matarka daka fi so kuma itace ta biyu,nida ka kama kuma nice ta uku,sai wasu kuma da dama.
Nasan yanxu ba tani zakayi ba ta matarka zakayi,kafin ka gama da itah nasamu na huta"
Tana gama faɗan hakan ta murza ƙofar ta fita ta barshi a inda yake a tsaye kaman robot.

MABARACIYAHWhere stories live. Discover now