*MABARACIYAH*
_hakkin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
_sharar fage_
Ni halittace wacce take tamkar hawainiyah,da take fitowa a launi daban daban.
A wanni wajen ma inaga nafi hawainiyar saboda ita idan ta sanja launi bata bayyana a wata siffah ta daban.
Wasu na kirana da matsoraciya,wasu kuma azzuluma, yayinda a wani wajen nake amsa kiran saliha, wani wajen kuma ni mai daukar fansa ca,wasu garesu ni mayaudariyace yayinda wasu ke daukata majinginarsu, wasu kuma sukan kirani da shu'umar macijiyah,yayinda wasu kuma ke yimin kirari da jajirtacciyah.
A yanda ainihin sunan yake a zukatan mafi akasarin mutane har gani kaina shine MABARACIYAH mace daya ƙwall acikin taron maza na almajirai¡¡...........
Shin amma ku zaku yarda da hakan,anya kuwa duk ni kadaice nake amsa sunan,ko kuma akwai masu kamanni kai?
Wace amsa ku kuka bawa kanku???
_sadi-sakhnace_Free page
1••2_shekara ɗaya baya_
Wata matace zaune a cikin taron mabarata wanda suke zama a bakin gidan bamu kudinnan domin samun abinda zasu sakawa cikinsu,duk wani lokacinma mutuwar zuciyace take kaisu.
Karar wayar nokia ce tayi kara a aljihun wata yar matashiya,wacce kusan dukka wajen tafisu mummunar shiga sosai.
Fitowa tayi da wayar da'aka ɗaɗɗaure da zare,da kyar ta daga wayar yanda hannunta yake karkarwa sosai.
Can kaman na minti ɗaya tasaka wayar a kunne amma batace komai ba,da alama wani abu ake faɗamata.
Sakin wayar tayi ta fadi a kasa tareda jera salati kala kala,
"Talatu mai ya faru kike wanann salatin lafiya kuwa?"
"Ahah kursiyyah,makwanciyata ce ta haya ta kirani wai ɗana bilyaminu dayake asibiti wai ciwonsa ya tashi,ance inbankai kudin aikin da wuri ba zai rasa ransa"
Wata ce daga gefe kana ganinta kaga jarababbiyah,
"Miye na damun kai oho,kefah kika ce yaronma shegene uhm"
Talatu tana jinta bata kula ta ba,karisawa tayi inda layin gaba suke ta faɗa musu abinda yake faruwa,ƙin yadda sukayi da ita saida na baya sukace da gaskene tukunna.
"Dan allah kuyi hakuri,ance idan ban kai da wuri ba zai rasa ransa,ku taimakeni na shiga gidan wajen alhaji dan allah,iya yaune kawai yake ganin mutane,inba hakaba bazan ganshi ba"
Kuka tafara wiwi,wanda hakan yasa na gaban jikinsu yayi sanyi suka barta ta shiga.
Securitynne suka bude mata kofar ta shiga tareda wasu masu neman taimako suma guda biyu da suke gaban layin.
Bayan kaman minti biyar da shigarsu sukaji danger alarma ta gidan ta buga.
Sauran masu neman taimakon hargitsewa sukayi,yayinda sauran masu tsaron kuma suka afka gidan da gudu.
Duddubawa sukayi inda karar ta fito,wani hayaki aka saki wanda duk da hasken rana ta allah amma mutum baya ganin gabansa.
Wani security ne ya kalli wata ƴar matashiya a cikinsu wacce bata wuce shekara sha takwas ba,ta fito daga cikin hayakin sai tari take.
"Lafiya khamriyyah naga kin fito ina yallabai ɗin"
"Ahhhh uhmm ban ganshi ba Ahamd,masu neman taimakon ma bangansu ba a ciki,inaga akwai matsala"
"Oh shitt,duk mai muke haka tafaru,akan haka zamu iyah faɗuwa jarabawarmu tazama SSS fah,duk da muna matakin karshe,barina ƙira Dec. Sadeeq yanzu nan"
Radio waya ya danna na security domin shaidawa headqauter su,
Can komai aka faɗamasa sai ya kashe wayar yana kallon ta.
"Yess wannan karon inaga zamuyi nasara khamriyyah,dasuka tashi guduwa da shi sun ɗauki mota a cikin gidan,kuma akwai na'urah mai bin diddigi a jiki"
Saurin hawa mota suka yi,ahmad na tuƙawa da mic a kunnensa ana faɗamasa inda zasubi.
**_____**_____**
Tafiya suke motar cikin matsanancin gudu,kayan jikinta yagygygye tafara cirewa tana zubarwa a motar,ta kuma yiwa wacce take tuƙin magana,wacce itama yagaggun kayanne a jikinta.
"Ki taka da sauri,mukai akan lokaci,sonake kowanne tafiya da motar nan zata yi ta dungayi ta barazanar ƙarewar numfashinsa na karshe a duniyah"
A bakin wani kogi suka tsayah bayan sunyi tafiyah mai nisa a cikin jeji.
Fitowa akayi dashi kansa a rufe da wani buhu,durkusarshi tayi a bakin ruwan dake gaban ta,tana sanye da baƙaƙen kaya sun yayyage kaman na mahaukata ,wanda tasamu damar sakasu a motar.
"Safiyyah,miƙomin buhun nan yanzunna"
"Toh shugaba"
Cirewa buhun dayake kansa tayi tareda tsugunnawa suna kallon juna.
"Ka ganeni Brr. Shehu ko kuma na tuna maka"
Jikinsa ne yafara karkarwa kaman an jona masa shocking.
"Dan .....al Allah kiyi hakuri na tuba,ki tunafah inada iyali dasuke jiran komawa ta gidan,mai yasa zaki zalunceni akan wata buƙata taki?"
"Hhahahah zalunci shine abicina brr. Shehu,kuma yanzu kaima zan ciyar dakai shi "
Karbar buhun tayi daga hannun matar sai motsi yakeyi,
"Kasan menene a cikinnan?,nasan baka saniba,to macizaine masu mungun dafi da aka tunzurasu na tsawon sati guda,neman inda zasu huce sukeyi,......yanzu zamu saka kanka a ciki su samu abinda zasu juye dafinsu a ciki"
Ihu yafara kan gari ya gari jin abinda take faɗamasa yana cikin buhun,saidai ko a jikinta saima ƙara nishaɗi da hakan yabata,
"Kasam menene Brr.,ina son naga na kama mutum babba yakusa haifata inayimasa abu yana ihu yana neman taimakona,sannan inason yin basaja a cikin masu nemana ko wanda nake nema,wanann duk yafi bani nishaɗi,naga kana nemana ko kuma kana tsorona amma ina gabanka,a matsayin bakowa ba batareda saninka ba,hhhh wannan shine aikin MABARACIYAH ,matsoraciyah kuma abar tsoratarwah,....ohh ina ta baka labari,ashefah kai lokacinka yayi na manta ma kwata kwata,shine kai kuma baka tunamin ba ?"
Duk shaƙiyancin datake yi shidai ya zuba mata ido,banda karkarwa da kuma gumi babu abinda yakeyi.
Mata biyune masu matukar karfi,jikimsu daga gani suna ɗaga ƙarfe,rirriƙeshi sukayi tamau,yayinda ta buɗe bakin buhu ta cusa kansa a ciki babu alamar ɗanɗanon imani a ranta,saima murmushi da takeyi jin yanda yake ihu sukuma macizan suna saransa.
Karar bingane yasaka ta tsayawa cak daga kallon wanda kansa yake cikin buhun,yayinda idonta ya sauka akan gefen kirjinta wanda jinin yake zuba ta wajen.
Sakin buhun tayi tareda miƙewa tana dafe kirjin ta kalli wanda yayi mata harbin.
Khamriyyah ceh wanda bayan tayi harbin hannunta sai karkarwa yake,abinka da wacce yinta na farko kenan.
Haɗa ido sukayi ta ida suna kallon kallon,buɗe baki tayi duk da harbin dayake jikinta tafara magana cikin taurin zuciya,
"Me kike nufi kenan da hakan,dan kin kawo karshena zaki iyah goge wanda nayi a baya ko kuma wanda zai faru a gaba,babu abinda xai fasu ƴar bincike,saima nace miki yanzu aka soma wasan................zamu haɗe masu bincike a salon daban"
Dariya ta saka jini yana fita ta bakinta kafin ta faɗa cikin ruwan dayake gabanta.
Ganin hakanne yasa suma sauran mabiyannata wanda suka sanye da kayan baran suka cikawa wandonsu iska saidai nasu jajayene ba baƙaƙe ba,daga ganidai idan zasuyi wami aikine suke sakawa.
Kallon khamriyyah dec. Sadeeq yayi tareda cewa,
"Aikin ki yayi kyau khamriyyah,duk da ke sabuwar shigace amma jarumtarki tana birgeni,daga yau nasakaki cikin sahun ƴan rukunina"
Murmushi tayi na jin daɗi kafin ta saramasa,
"Nagode sir,zan kasance mai cigaba da jajircewa,bazaka taba samun matsala daniba"
Da gudu masu bada taimakon gaggawa suka zo da ambulance aka ɗauki brr. Shehu,wanda cikin ƙanƙanin lokaci har kansa yayi tulele kaman randa dan azaba.
Asibiti aka wuce dashi da gaggawa saboda ƙoƙarin ceto ransa.
Tare suka wuce asibitin duk da su dec. Sadeeq ɗin,yayinda wasu kuma aka barsu a kogin su nemo gawar mabaraciyah a ruwa,dan harbin da aka yimata a saitin zuciya ba lallai ne takai iyanzu ba da rai.
A tsaye suke shida khamriyyah a ƙofar asibitin kowa yayi jugum da abinda yake sakawa a ransa.
Wayar Dec. Sadeeq ce tayi ƙara wacce yake amsa kiran dayashafi rayuwarsa,hayatee yagani a jikin screen ɗin,wanda hakan yasashi yin murmushi.
"Hello Amrah zan ƙiraki ina kan aikine yanxu haka mai muhummanci"
Har zai sauƙe kiran tace
"Tsayah baby,kasan dai kaine farin cikan koh?,sannan kuma kaine nutsuwata ,nasan dama kana aikin ai,yanzunnan naji wani batu,wai kun samu nasarar kashe wacce take kidnap ɗin manyan mutanennan"
"Uhm Amrah a ina kikaji keda kike cikin gida"
"Oh tambaya ma kake,ina matar shugaban masu bincike na jiha har ace a ina naji,yanzu dai ba wanann ba,kana lafiya babu abinda ya sameka koh?"
"Lafiyata kalau,kefah ykk ya gidan"
"Uhm babu ƙalau har sai ka dawo,koyaushe kace wani baka da time ɗin ƙirana,amma kullum kuna tareda wanann sabuwar ɗalibar taka,watan mu shida da aure har an fara maƙala maka abokiyar aiki mace,ni banasonta batayimin ba kwata kwata"
Gyaran murya yayi tareda kallom khamriyyah wacce ta maze tareda kawar da kanta kaman bataji mai matar tasa ta faɗa ba.
Ganin hakanne yasashi saurin komawa gefe kaɗan"
"Kai Amrah wani abun ki daina faɗamin a wayah mana,yanzu kashi taji abinda kika faɗa,kimga ai bazata ji daɗi ba koh?"
"Oh taji daɗi? daɗima zataji?,dama nasan kafara sonta ai,nibaka damu dani ba shikenan"
Ta faɗa tana saka masa kukan kissah,lumshe ido yayi yana sauraron rigimar matar tasa,indai akan watane bata ɗaga masa ƙafa bare ta fahimceci,takasa gane cewar ita kaɗaice a ransa babu wata daban.
"Kinga kiyi shuru haka,kinsan kukanki na ɗagamin hankali,yanzu barina koma dan iyalan sa sunzo asibitin,idan na dawo zamuyi magana,kimin massage ɗin abinda kikeso na taho miki dashi kinji"
Yana gama faɗa ya kashe wayar tareda sumbatar wayar,iyah dasafe yabar gidan amma har yayi missing ɗin soyayyarta.
Komawa wajen asibitin yayi,wanda shigowar wasu mutane kenan asibitin,babu abinda suka sai aikim kuka,musamman ma babbar macen,wanda da alama matarsa ce.
"Innalillahi,yanzu bawan allah abinda yafaru da alhajin kenan?,ina gida sainaji mummunan zance kuma,da safe fah mukayi sallama dashi akan za'a kawomasa rahoto,sannan kuma zai gana da masu neman taimako,shikenan sai a yimasa haka,kowa yasan halinsa na kirki da dattako na mijina a garinnan,bai ci wannan ɗanyen aiki ya hau kansa ba,wannan yarinya akwai ƴar tsinanniya,inshallah baxata gama lafiyaba sai taga karshenta itama,yanzu duniya ta zamo babu dama mutum yayi taimako sai an kawar dashi,ni inada tabbacin cewar wlh duk yanda akayi abokan adawa ne suke aikata take wadannan ayyukan,kuma bilahillazi sai asirinsu ya tonu suma,Allah ya isah wlh bazan taba yafewa ba,haba wanann zalunci har ina"
Dec. Sadeeq ne ya matso kusada ita tareda bata baki,dan duk sauran wanda suke wajen suma buƙatar wanda zai lallashesu suke,ita kaɗaice ma tasamu damar faɗar abinda yake cikin ranta.
"Kiyi haƙuri mrs. Shehu,haƙiƙa abin da ciwo,saidai maganganun suma basuda amfani a yanzu,dan mun samu kawoshi asibitin da gaggawa inshaallah babu abinda zai faru...."
"Abinda zai faru kan ai ya riga ya faru,malam naga fah yanda kamanninsa suka tashi daga yanda suke da aka dora a wayah,banda zalunci ta bushashshiyar zuciyah,ko wanda yayi mummunan aiki ban ta'ba ganin wanda akayiwa horo da macizai ba,wanann yarinyar duk yanda akayi ba mutum bace inaga shegiya tsinanniyah kawai,wlh itama sai anyi mata fiye da haka"
Ƙara gunjin kukanta tayi tana bubbuga kirji,
"Kiyi haƙuri hajiya,wacce kike magana akai ma ta mutu yanzu haka,ɗaya daga cikin abokiyar aikinmu tayi nasarar harbinta a kirjinta na hagun"
"Ina gawar yarinyar take?"
"Uhmuhm har yanxu ana kokarin nemota a cikin ruwan"
Idonta ta tsayar akan fuskar khamriyyan wanda dec. Sadeeq ya nuna mata.
Saurin karisawa wajen khamriyyah tayi tana kallonta ƙasa da sama.
"Kkkece Dec. Khmariyyah wacce ta harbeta?"
"Eh nice ranki ya ɗaɗ......."
Tun kafin ta gama maganar hajiyan ta ɗauketa da wani bahagon mari,zata ƙara mata Dec. Sadeeq yayi saurin riƙeta.
"Hajiya lafiyarki kuwa haka"
"Tamabayata ma kake meyasa na mareta,to dayafi mari zanyi mata,ka duba irin azabar data gallazawa mijina,wanda yake cikinta yake shan ta har yanzu, bai ci kuɗin kowa ba bai kashe uban kowa ba.
Amma ita data aikata hakan shine ta kasheta cikin sauƙi da salama,kuma wai gawar dazan gani ma nayi mata wani abu ko zan huce wai ba'aganta ba?"
Dec. Sadeeq yana cikin riƙe da itah wani likita ya fito daga ɗakin da brr. Shehun yake.
Saurin fincike hannunta tayi daga riƙon da Dec. Sadeeq ɗin yayi mata tareda nufar inda likitan yake.
"Likita ya ake ciki,yatashi ina koh,ina ya tashi koh,ina so ka faɗamin yanzunnan"
"Hajiya kiyi,haƙuri tukunna,mun samu nasarar ceto rayuwarsa,saidai kuma gaskiya babu alamar zaiyi tsawon rai,daga nan zuwa kowanne irin lokaci zai iya tafiya,dan gabaɗayah ƙwaƙwalwarsa ta cuɗanya da dafin macizai,munyi mamaki ma da bata narke ta zubeba dan gas......."
"Ya isa haka likita da wannan mumummunar maganar taka,da bata zubeba kai ai saika je ka zubar da itah,yanzu dai zamu iya ganinsa ko yaya?"
"Eh to hajiya a yanda yake bai kamata a bari wasu suje kansa ba,saidai kuma duba da halin dayake ciki,na mutuwa ko rayuwa bazamu iyah hanaku ganinsa ba,saboda idan muka hanaku ma har yanzu babu wani cigaba sosai"
Tun kafin yagama bada bayani hajiya Delu ta nausa cikin ɗakin,turusss tayi a bakin ƙofah ganin yanda aka sossoka masa wayoyi a kansa masu yawa,ga kuma kannsa yayi suntumeme kaman na mutum uku,kuma yayi bakikkirin ya tashi daga kalar jikin mutum.
Mutuwar tsaye tayi a wajen takasa karisawa,duk son ta da takarisa wajen abin gagararta yayi,dan karfim kuriwarta baikai yayi hakan ba sam.
Hannunta ƴar ta taza mai shekaru sha biyar,babu abinda yake tashi a cikim ɗakin sai sautin ƙarar injin rayuwar da aka manna da jikin brr. Shehu,wanda bai san inda kansa yakeba.
Takawa tafarayi a hankali yayinda karar injin ma yake ƙara sauti a kunnenta dadai da yanda take kusantarsa.
Saida taje daff da inda yake kwancen kafin taja ta tsayah tana karemasa kallo.
Waye zaice wanann halittar ta mutum ce kuma wai wanda da safema lafiyarsa ƙalau inba wanda yasani ba,gaskiya makashiyar bakaramin ƙwarewa tayi ba a harkar kisa.
Zama tayi a bakin gadon dayake kwance tareda riƙe hannunsa ciki nata,
"Mijina!,kaga yanda ta maida kai cikin abinda bai fi awanni ƙalilan ba,anya kuwa wanann mutum ce,mai kayi mata dazata yimaka haka,kuma wai abin takaicin ita ta mutu cikin saukakkiyar hanya,amma kai kuma kana shan wahala,wanann ba adalci bane sam,ka tashi ka amsamin kaji,ga ƴaƴanmu ma suna buƙatar ganinka,ka tashi kacemu su babu komai kaji barister nah......."
Dukkansu kallon na'urar suke yanda layin rayuwarsa yake sauƙa da sauri sauri.
Yarimyar ce ta tashi da sauri ta nufi ƙofah domin kiran likitan yazo ya gani.
Hannunnasa da take riƙedashi taji ya kankame,wanda hakan yasa ta bashi hankalinta.
Buɗe idanuwansa yayi da kyar,wanda kwayar idon ma tayi luhu luhu jajur,abun babu kyan gani,buɗe bakinsa yayi kaman mai son yin magana.
"Mmmmmm....bbbbraciyah........."
Daga haka taji hannunsa ya shika,daga gani yanason faɗan wani abu,ɗaga ido tayi ta kalli likitan wanda ya sunkuyar dakai alamar tafaru ta ƙare.
"Likita ya kake tsaye,kazo ka dubashi mana,likitaaaa"
"Kiyi haƙuri hajiya brr ya amsa ƙiram mahaliccinsa,kiyi duba da injin dayake gabanki"
Juyawa tayi ta kallah,sai a sannan taga ashe injin ya tsayah cakk,
"Ahah bahaka bane,wannan injin ƙaryah yakeyi,mijina bai mutuba bai ......"
Tun kafin ta gama magana luuuuu ta faɗi ƙasa mataciyyah..
Saurin yin kanta likitan yayi shida yarijyar wacce itace ƴar babba a cikin ƴaƴan.
Saurin ɗauƙarta akayi zuwa wani ɗakin a cikin asibitin.
Yayinda shikuma marigayi brr. Shehu aka turashi zuwa ɗakin ajiye gawawwaki.
Khamriyyah ce ta kalli dec. Sadeeq tareda cewa,
"Gaskiyah abin ba yanda muka tsammaceshi bane,yanzu ogah ya zamuyi da gawar,da kuma ita hajiyan,dan yanda mutuwar ta zamo da kuma binciken"
"Wane binciken za'a sake bayan an riga ansan dalilin mutuwarsa,saidai kuma saboda babban mutum ne case ɗin bazai mutu nasan a iyah haka.
Yanzu abin da zamuyi shine muƙara tsananta binciken nemo gawar ita makashiyar tunda har yanzu sunce basu gantaba,kuma dama ga ruwan yana ambaliyah sosai,nemota zayyi wuyah sosai.....ahhh idan baki mantaba naji kaman yace mmmm....mabaraciyah koh,kafin ya mutu,shin ko zaki tuna wannan suna?"
"Eh to yallabai lokacin da mukazo kaman kuna wani bincike akan case ɗin kisan wata ma'aikaciyar asibiti,wacce aka sameta anyi mata allurah da dafin macizi,kuma an rubuta mabaraciyah a duk jikinta da reza"
"Tabbas hakane ashe kin tuna,kuma wannan ma haka muka karishi duban mu bamu gano hujjah ko ɗaya ba,dan hatta shatin hannu ɗaya na mutum babu a jikin gawar.
Akwai lauje cikin naɗi gameda kisan guda biyu,waccar an ruvuta mata sunan mabaraciyah a jikinta,shikuma wanann yayinda yake gabar mutuwa ya ambaci sunan mabaraciyah,tabbas akwai kamanceceniya tsakaninsu.
Inkuwa hakane to lallai kin cancanci karramawa ta musamman,wajen nasarar da kikayi na harbinta khamriyyah"
"Nagode sir"
"Karki damu,ki tsaya a wajennan tunda mrs shehu da kuma gawarsa suna ciki,zanje wani waje ina dawowa yanxunnan"
"An samu wani abune har yanzu?”
"Eh sargent umar ya ƙirani wai an ga gawar wata mata da harbi a ƙirjinta a can wani ƙyauye da nisa,to ina kyautata zaton itace,dan yanayin shaidun da alamar sunyi dadai,ki tsaya nan yanda nace miki,in case ko za'a buƙaceki"
"Bakomai sir sai ka dawo"
Ta ganin ƙulewarsa ta jawo wata ƴar karamar wayah a aljihunta ta kunnata,saida taga babu kowa a wajen kafin ta danna ƙira.
"Hello shugaba Viper-lady"
Aka faɗa daga ɗaya bangaren.
"Yeess Vl3 ykk komai lafiyah dai koh"
"Eh komai lafiyah,muna nan a tare iyah Vl1 ce kawai bata nan tana kan nata aikin ita ma"
"Okay good,aikinku yana kyau da kuka taimaka min na kashe mabaraciyah,nayi nasarar kashe tsuntsu biyu da dutse ɗaya,na kasheta na shafe aikinta,sanann kuma ni nasamu yarda da kuma ƙarin matsayi daga cibiyar bincike,yanzu aiki da salo zai soma daga yanda yake.
Mataye a shirya, Viper ta fito daga cikin raminta bayan tsawon ɗaɗewar datayi a ciki tana dakon jiran ranar fitowa,yanzu matar datayi mata kanainai ta hanata fitowa ta matsa.
Lokacine ita ma daya kamata ta fito tayi nata sunan sanann tabawa zuciyarta abinda take muradi.
Mun shiga episode 2 na wasan,bansan kozanyi wasan dayafi nata ko ahah"
Tana kashe wayar ta zefata a aljihu tareda gyara ɗamararta da kuma hularta,wani mungun shu'umin murmushi tayi tareda cewa,
"Micijiya zata shiga cikin rigar mai kamata,yayinda shikuma bai san tana ciki ba,yayi zaton mai taimakonsa ce,inda zaiyi ta faɗamata sirrin yanda zai kamatan.
Mai zai faru?...shin tunda ta riga tasan ta inda zai kai farmaki zata barshi kuwa yayi nasarar.
Salon Viper lady shima daban yake da na mabaraciyah._sadi-sakhan_
YOU ARE READING
MABARACIYAH
ActionDuniyah juyi juyi abubuwa da dama sukan faru amma haka zasu zasu wuce kaman ba'ayi ba. Idan anyi maka abu sai a ce kayi haƙuri watarana zai wuce meyasa?. Ban yadda da wannan maganarba,madadin na barshi ya wuce saidai na ajiye domin neman fansa. wan...