chp 15_16

166 2 0
                                    

*(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)*

             *MABARACIYAH*
           (mai harshen damo)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε.
          

_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)

                                       

Paid book #400
3131951977
Auwal sadiya
First bank

Mai turo kati kuma ta wanann number MTN
09035784150

Mutanen niger su tuntubi wanann number
+227 97 21 16 15

Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a.

      _____________________
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃



15••16













Abun ne nake jinsa tamkar a mafarki,shikenan khamriyyyah ta tafi,bazan sake ganinta ba,duk da tace zata dawo amma ban yadda da wanann zancen ba,duk yaron da'aka tafi dashi baya dawowa,nasan ta faɗaminne kawai dan na saki raina.
Ina cikin tunani khairiyya ta dafani,ɗagowa nayi na kalleta ganin itama damuwarce a ranta.
"Sabrah nasan kina kewarta koh,nima ina kewarta sosai,zata iyah komai damin mu,duk da ƙarancin shekarunta amma zata iyah tukarar abinda yafi ƙarfinta domin masoyanta."
"Hakane khairi,muna mata fatan alkhairi a duk inda take"
Bayan tafiyar khamriyyah da sati ɗayah inno tasamu baba shehu tayi masa magana akan ya kaimu makarantar kwana,nasan tana tsoron muma ta rasamune,ko kuma tana so murage kewar da muke ciki.
Bayan tayi masa bayani kuwa ya amince da hakan,akan xai kaimu makarantar su anty juwairah wanda ita paper suke suna aji ƙarshe na matakin secondry.
Munyi murna sosai amma ba kaman idan khamriyyah da maryam suna tare damu ba.
A satin akayi mana shriri muka tafi,dan har an fara karatu.
Ikon allah mai yadda yaso,da farko muna tunanin mu uku zamu tafi,sai gashi ashe mu biyune zamu tafi kawai.
Kaya dayawa inno ta haɗa mana,su sukari,gari,ƙarago,da kuma ƴar madara,saboda in mukaji yunwa mu ɗan saka a cikinmu,duk da bamu san makarantar kwana ba amma kuma muna jin labarin wuyarta.
Saidai duk da haka abinka da yaro mai son tafiyah makarantar kwana,munason zuwa.
Baba shehune ya kaimu har makarantar da kansa,tundaga bakin ƙofar makarantar muke ƙaremata kallo,finally yau gamu a makarantar kwana zamu shiga cikinta,waiwayawa nayi na kalli khairyyah,itama niɗin take kallo tana dariyah.
Office ɗin principle ya shige damu tareda kayanmu,muna zaune suka gama magana da malaman,aka bashi wasu takardu,yasaka hannu da sauransu,mudai namu idone kawai.
Bayan sun gamane aka aika a ƙirah Juwairah usman,daga baya kuma mai aiken tadawo wai bata nan suna paper.
"Toh kuna son makarantar kwana gashinan na kawoku,sai ku dage kuyi karatu,dan kun fi kowa sanin shine gatanku a yanzu.
Yayartaku tana ɗakin jarabawa,idan ta fito zata zo ta ɗaukeku ku jirata a nan,ni zan tafi sai nazo muku visit.
Kuka khariyyah tafara tana ƙiran inno,tsayawa yayi yana kallonta tareda rarrashinta,amma ganin zata bata masa lokaci yafa yi mata faɗa.
"Jimin sakaliyar yarinyah,idan bazaki zauna a makarantar ba kizo mu tafi toh,duk uwarku ce ta lalata ku"
Gani ya balbaleta da masifa tayi gum da bakinta,dariyah nayi ƙasa ƙasa.
Haba dama khairiyyah ta iyah sakalci da kuka,inba hakan yayi mata ba bazatayi shuru ba.
Sai can wajen ƙarfe huɗu anty juwairah ta fito daga paper,duk da muna son zuwa wajenta amma munsan kwanannan zata tafi ta barmu mu kaɗai.
Da gudu ta taho inda muke tana ware mana hannu,muma da sauri muka tashi muka tareta muna dariyah.
Rungumemu tayi dukkanmu,
"Iyeee yaran inno sun girma sun shigo makaranta,ina sauran to naga ku kaɗai"
Tafaɗa tana dudduba bayan mu.
Murnar da muke muka daina muna wawwara idanuwa,dan bamu sam ma mai zamuce mata ba,raahin daɗi kam dole tajishi.
"Uhm.....anty juwairah dd..dama wasu sun ɗauki maryam da kuma khamriyyah,wancan watan"
Sakin mu tayi tareda yin jimm,idonta ne yayi ƙwal ƙwal kaman mai shirij kuka,sai kuma tayi saurin kawar dashi tareda jan hannuwanmu.
"Ssshikenan kuzo mutafi ku huta kafin gobe ku tafi aji koh?"
Bin bayan ta mukayi tana tafiyah,shuru babu wanda yace komai,kowa da abinda yake saƙawa a ransa har muka isa hostel ɗinsu.
Shiiya mana kayanmu tayi a kwanar ta,tareda kaimana ruwan wanka da kuma abinci.
Ƴan riguna ta fitar mana a kayan muka saka da daddare,anata hira tana nuna mu ga ƙawayenta,cewar ga ƙannenta sun zo.
"Hmmm naji kunyi shuru baku bani labarin abinda ya faru ba,ina bakin surutun koh ya mutu kai?"
Dariyah nayi tarede 'boye fuskata,tunda muka zo kam mun kasa cewa komai.
Labarin abinda ya faru na bata,tareda sanar mata yanda za'a tafi da khairiyyah amma khamriyyah tace ita ta yarda a tafi da ita
"Inno tayi ƙoƙarin cewa ta zauna,amma taƙi amincewa,a cewarta bazata juri rabamu da inda muka tashi ba,sannan bataso a rabani da ƴar uwata,itace ya kamata ta tafi ba muba"
Dafa ni anty juwairah tayi idonta ya kawo ƙwallah tacd
"Allah sarki maryam,kusan ni nayi rainonta,yarinya ce mai hankali sosai,ina addu'ar allah yasa ta samu gidan kirki dazasu riƙeta da amana.
Khamriyyah kuma nakasa cewa komai,yarinyar tasha wahala a rayuwarta da take buƙatar wanda zasu tallafeta,duk da ita mutumce da bata nuna wahalarta,burinta kullum ta 'boye tace babu komai,saidai ma ta tallafeka.
Duk da ɗaukar mutum a gidanmu kamata yayi a masa murna idan yasamu gidan kwanciyar hankali,saidai har cikin raina ina fatan khamriyya ta dawo garemu,amma kuma ina mata fatan allah yabata farin ciki,allah yasa su inganta rayuwarta ta manta da abinda yafaru da rayuwarta a baya"
Sake rungumo mu tayi muna ƙara yin kukan rashin ƴan uwannamu.
Hankalinmu kwance muke rayuwa da anty juwairan,babu wanda yake dukanmu ko kuma saka mu aiki,saboda muna ƙannen ta,rayuwar daɗi sosai.
Satinmu biyu da zuwa ita kuma anty juwairah ta gama makarantar,bayan an ga jarabawa anyi bikin candy da komai.
Sabon kuka muka kafa lokacin dazzata bar makarantar,khairiyya kam ma cewa tayi zata bita su koma gida,saida taga dole sai ta zauna kafin ta haƙura.
Tun a daren muka fara ganin sanji a makarantar,ashe dama sauran ɗaliban da su anty juwairah suke ƙasansu haushin mu suke ji sosai.
Kasancewar kowane ɗalibi yana punishment mu bama yi,da daddare muna kwance sai jin zubar ruwa nayi akaina mai shegen sanyi,zaburah nayi na tashi tareda sauƙe ajiyar zuciyah,wanda ashe itama khairyyah haka tayi.
Wata bufurwace zata kai anty juwairah a haife da bulala a hannunta.
"Hhhhh wato ku ga ƙannen sister juwairah koh,kowanne yaro zayyi aiki amma ku kuna zaune,dan ubanku wa kuka fi a makarantar nan"
"Kiyi haƙuri" shine abinda na samu damar faɗa.
"Haƙuri,naibishi da gudu ba wando,ƴam bantan ƙaniyah,ke Lawisah kwantar minsu yanzunnan,kowacce sai na yi mata bulala sha biyu,sannan kuma idan ku dawo daga aiki gobe akwai wankina yana nan zakuyimin shi"
Duk haƙuri damuke bata haka tayi biriss damu aka kwantar mu kaman yanda ta umarta.
Bulalar take ɗagawa tana zambaɗa mana muna ihu,bata daina ba har saida tayi mana adadin yanda tace tukunna.
Fita sukayi daga ɗakin bayan sun gama zagemu tass,yaran dasuke ɗakin babu wanda yayi tari,duk da idonsu biyu sunga mai ya faru,saidai babu mai ikon cewa komai.
Ajiyar zuciya muka cigaba dayi har bacci yasake ɗaukemu.
Da safe da wuri muka tashi,jikin mu yayi tsami saboda dukan da muka sha a wajen sister Lubabatu,da mukaji ashe itace labour ɗin lokacin.
Gugu gugu haka mukayi wanka da ruwan sanyi kafin muka saka uniform ɗin mu zuwa aji.
Bayan mun taso kuwa hostel ɗin sister lubabatu muka wuce,yin wankin datace zamuyi jiya da daddare,haka babu imani tasaka mu kneeldown a rana na kusan awa guda kafin ya bamu wankin.
Lokacin babu ruwa a makaranta ya ƙare,haka muka yi tafiyah mai nisa a inda aka kwatanta mana kafin muka samo muka wanke mata,duk jikinmu a tsorace yake karmu sake wani laifin.
Lallai lokacin da anty juwairah take nan ba'a makarantar kwana muke ba sai yanxu tukunna.
Watan mu guda babu itah har mun saba da duk wata wahala da ake gallazamana,mun bi sahun yaran wajen muma.
Kwannan baba shehu yazo mana visit,ji mukayi kaman mu bishi gida muce mun fasa karstun,amma babu halin yin hakan,tunda muka fara toh dole sai mun ƙare.
Sannan kaman yanda kowanne yara suke jurewa muma dole mu jure mu saba da hakan.
Lokacin da mukayi hutun zango na farko murna kaman zata kashemu zamuje muga gida,kowa ranar kasa bacci yayi ana gobe hutu.
Kaman yanda baba shehu ya faɗa mana kuwa ƙarfe sha biyu tayi masa a makarantar mu,kasancewar dole sai ya taho daga garinmu zuwa cikin katsinan,mudai sunan muna cikin birni,amma bama zuwa bakin get sai ranar dazamu bar makarantar zuwa gida.
Tundaga mota da muka tsayah khairiyya bata tsayaba tayi cikin gidan da gudu tana ƙiran inno,nice ma nayi ɗan dauriyar ɗaukar jakata..
Ganin khairiyyah ta ɗale inno nikuma na ɗale anty juwairah wacce itama taji muryar khairiyyah ta fito.
Dariyah aka dungayi tareda bada labarin yaushe gamo,inno ce ta katsemu ganin labarin bazai ƙare ba,
"Kunga ya isa haka,muje kucire kaya kuci abinci ku huta tukunna,kafin koma menene sai ku faɗa"
Wayyo gida daɗi rahama,kowa yabar gida gida ya barshi kam,can ayita dukanmu ana samu aiki,nan kuma yimana komai za'ayi.
Result ɗinmu muka fitar daga jakar,tun kafin na gama cirewa naji anty juwairah ta fizgeshi daga hannuna,tana dariyah.
Kallona tayi tareda dagani sama lokacin data nawa naci.
Nice nayi na biyar 5,khairiyyah kuma tayi na bakwai 7.
Saidai tafini cin math da computer,don ranta yana son subject ɗin sosai.
Murna inno tayi sosai itada sauran iyayen mu ganin mun maida hankali mun dage sosai a karatun.
Toh fah da hutu ya ƙare aka ce mana wani satin komawa duk sai muyi wani iri,dan shi deen har ya koma jiyah,shikam dai to ba ƙoƙari gaskiya,dan na kusan hamsin yayi a cikin su sittin.
Haushi maman yara taji sosai,dan har dukansa tayi.
Haka babu yanda mukayi muka tattara muka koma aka cigaba da gashi.

MABARACIYAHWhere stories live. Discover now