*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseenwattpad name
Humaira3461🅿️.....1
Duk'e nake na tusa mahaifina gaba ina kuka saboda banda kukan banda wani abunyi, haka mahaifiyata itama tana kusadani sai hawaye take sharewa, yayanmu Sule na tsaye gefe ya dora kanshi jikin tagar dakin Innamu sai kanwata zainab.
"Asabe wai nace daku mutuwa zanyi ne? Kun taru akaina sai kuka kuke mun bana son wannan koke koken,ba yau na fara wannan ciwon ba ya kamata ace kun saba dashi"
Baban ya fad'a cikin wahaltuwa muryar tasa kanta daker take fitowa, innamu na kukan take cewa, "malam ciwon ka ba shine yake samun kukan nan ba, rashin gata da galihun da muke ciki da zamu taimakeka mukai asibiti shine ya damemu, da kuma irin wahalar da kake sha aduk sadda ciwon ya tashi,kuka dole ne saboda ana cikin halin da ya zama wajibi ayisa"
"Ayi amfani da abunda ya samu mana asabe, ba naji sale ya zo da wasu kud'i ba"
Innamu na zubar da hawaye tace, "tun safe ya fita nema daker ya samu dubu uku, acikin dubu uku malam ko isa asibiti ba zata ishemu ba, tunda dole sai mun shiga cikin gari anan sun riga sun tabbatar mana bazasu iya mana komi akai ba"
Huci kurin baba keyi na zafin ciwo ina wajen kanshi ina shafa masa addua ina hawaye, cikin disashiyar murya nace "Baba sannu kaji,insha Allahu zaka warke zaka samu lafiya"
Ya sauke numfashin wahala yana mun murmushin karfin hali yace, "Allah yai maku albarka MURJANATU keda yan uwanki, ku cigaba da mun addua Allah ya kawo sassauci hakika ina cikin rad'ad'in ciwo, nikadai nasan me nakeji"
Kuka muka sake rushewa dashi nida zainab saboda yadda yake maganar kadai abun tashin hankali ne, yayanmu ya juyo idonsa jajur kamar an watsa masa yaji yace a dame,
"Innamu zanje na samu dillali anemo mai siyen gida mu bada gidan jingina abamu kudin da zamu kai baba asibitin cikin gari, wallahi tsoro nakeji mu sake kwana dashi a wannan halin da yake ciki, idan muka samu kudin ko nawane sa muje asibitin"
Innamu na sharce hawaye tace, "tun tuni ban kawo wannan shawarar ba sale, maza jeka hanzarta Allah ya taimakemu asamu maiyin wannan aikin ladar,"
Aguje yayanmu ya fita yana haki muka duk'ufa addua da neman rangwame wajen Allah, tun baba na iya magana har takai baya iya cewa komi saidai ido, tun azahar yayanmu ya fita amman har akai sallar la'asar babu alamun sa, ga jikin baban sake rikicewa kurin yake, wannan k'afa tashi mai wani irin rub'eb'b'en ciwo sai zubda ruwa mai wari take, kowa hankalinsa ya tashi kuka kau da hawaye na k'arewa da sun k'are saida ana gabda kiran mangaruba sannan sai ga yayanmu da mai siyen gida da dillali,gidan mu ba wani gida bane na azo agani gidane na k'asa duk ya zaizaye, abunda kawai zai saka yai d'an mutunci shine fad'in gidan duk wanda ya siya rushesa zai ya tada sabon gini, so zai samu isasshen fili dazai wadacesa, kasancewar cikin buk'atar kud'in muke da akai ciniki daker mutumin nan ya bada dubu dari da hamsin,ba yadda yayanmu baiba akan ya kara su cika dari biyu amman ya rufe idonsa yace idan bamu son hakan shizai fasa,
"Aa bata kai ga haka ba yallab'ai, mun siyar hakanma mungode Allah yai albarka"
Inji innamu shi kuma yayanmu ya anshi kud'i sanan akai rubutu saboda halin rayuwa, mu duka muka kwasa muka tafi saboda duk wanda aka bari hankalinsa bazai kwanta ba, daker aka samu motar daukar taki ta nan cikin kauyen namu muka shiga mu duka aka shimfid'e baba bisa tabarma,da yake harda yan kayanmu muka dauko don ba makawa sai an kwantar damu asibitin.
********
Sunan garinmu *GEZAWA* karamar hukumar kano state ce, haka na wayi gari na ganmu acikin wannan gari mai cike da mutane ma bambanta, masu kirki da marasa kirki rayuwar da ake a kauyen gezawa rayuwace dai ta kak'ani kaye, talakawa ne zuryan acikin wannan garin amman zan iya cewa ba wad'ada talauci yaima katutu irin gidanmu, tunda nai wayau haka ja tashi na samu baba baida lafiya sannan abinda zamuci yana mana wahala,duk da wannan ciwon nashi haka yake fita yana nemowa ko yayane aci duk da bakullin muke cin abinci ba, muna iya yini mu kwana bamu ci ba.
Har gona baba garesa innamu ma amman basu da halin noman saboda noma sai kana dashi kakeyi,basu ajeba basu ba wani ajiya ba.
A bakin innamu naji cewar su d'in yan gudun hijirane sukazo wannan garin, ankai ma garinsu hari aka kashe masu dangi da yan uwa dole suka gudo suka taho nan,tace acikin wannan gayyar suka had'u da babanmu sukai aure anan garin, su y'an Cameron ne innamu don ita d'in shuwa ce sadakar yalla shiyasa takeda mahaukacin kyau, takeda gashi indai akace maka shuwa to angama magana,babanmu kuwa su yan libiyane asalinsu tun kaka da kakanni amman shi daga wani gari dake cikin baushi sukayo gudun hijrar har suka had'u da innamu,shi fulanin bauchi ne shima babanmu badai kyau ba wannan had'in shine ya jawo mani ruwan kyan da nake dashi, duk gidanmu nafi kowa kyau a cikin gari saboda kyauna na tara makiya da dama,shiyasa banda qawa ni saboda sunajin haushina duk samarin su ni suke so, ni kam bana ma biyewa saboda yadda naga suna nuna mun.
A haka muka taso cikin gezawa nida zainab munyi primary da secondary amman ni na tsaya ne Jsce ban koma ba, duk da karatun kyautane hakan baisa na koma ba saboda halin rayuwa, kayan duk sun yage bana iya fita dasu a haka.
Zainan ce take aji biyu yanzu yayanmu ya samu ya kammala secondary dinsa kusan shekara biyarce tsakanin mu, sannan babu laifi munyi karatun allo littatafai duk mundan tab'a babu laifi don yanzu haka inda izu talatin da biyar akaina zainab ashirin yayanmu kau yai sauka, a shekarun mu kuwa yayanmu zaiyi shekara ashirin da bakwai ni kuma ashirin da d'aya zainab na bata shekara biyar itama yanzu tana cikin sha shidda kenan, wannan shine asalin mu.Banyi alkawarin posting kullin ba, haka zalika duk abunda kukai ci karo dashi kuyi hkr haka labarin yazo dole a haka zai tafi ngd.
Mom muhseen✍🏻
YOU ARE READING
JANNAH
FanfictionKaddara abuce mai nauyi, kuma mai zafin gaske,ayayin da ta kasance mai kyau alokacin take da dad'i a yayinda tazo akan akasin hakan lokacin kakejin duk duniya babu wanda ya kaika fuskantar kalubale, Ku shigo cikin labarin anan ne zakuji LABARIN KADD...