*_💔JANNAH💔_*
*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseenwattpad name
Humaira3461🅿️......2
Tun da muka iso asibitin tun karfe takwas, amman har anyi sallar isha'i babu wanda ya dubemu a wajen, saboda kuka jinake har ban gani innamu tun tana kukan harta hakura, yayanmu kam in kafafunsa basuyi ciwo ba Allah na sonshi, zaryar da yake tsakanin wajen nurses da metrori kadai ta isa ya sik'e, wannan rayuwar ace idan baka da galihu ko asibiti kaje babu mai kulaka, munata hauka bamusan baba ya sume a wajen ba, karar dana daddage na fasa itace ta janyo hankulan mutane da yawa akanmu, duk wanda yazo saiya dad'e hancinsa saboda warin da kafar baba keyi, mun dauka ya mutu muka hau koke koke da kururuwa saida wani likita yazo ya duba shi sannan ya kwatsan tsawa yana cewa,
"Dallah malama kiyi mana shiru, ubanwa yace daku mutuwa yai?"
Innamu na kuka tub'uran tace, "haba likita ku agaje mu mana, tun takwas muke nan ank'i saurarenmu, ya zamuyi da ranmu? Bawan Allah nan yana bukatar taimakon ku"
Tashi yayi yana kiran wasu nurses suka kawo wheelchair aka dora baban yace yayanmu kad'ai zai biyosa, godiya makai tayi ma Allah da taimakon da muka samu,shirun da mukaji yasa mukatai waje wurin wani famfo mukai alwallah muka dawo nan harabar mukai sallolin da bamuyi ba, muka d'uk'ufa rok'a ma baba sauki.
Yayanmu bai dawo ba sai wajen goma da rabi yana sharce gumi, yace "gwaje gwaje mukaje akai mashi, anci rabin kudin nan fa innamu gashi yanzu an shiga dashi wani daki an bani wannan takaddar zanje in nemo duk abunda suka rubuta"
"Babu komi sale kaje asai duk abunda ake buk'ata muga abunda Allah zaiyyi"
Haka ya juya yana tambaya ka nuna masa pharmacy,ya sai komida ake buk'ata sannan yaje yakai ya koma gefe yana jiran tsammani.
*bayan awa uku*
Likitan ne ya kira yayanmu suka wuce office d'insa bamu san me suka tattauna ba abunda muka gani kawai shine yayanmu ya fito yana kuka, tunda nake ban tab'a ganin kukansa ba jarumin mutum ne mai dakiyar zuciya, tun daga haka naji zuciyata ta buga naji jikina yana sacewa inajin kamar xan fad'i, saurin tarosa innamu da zainab sukai silalewa k'asa yai yana zaman dirshen yana cewa,
"Shikenan innamu zamu rasa baba! Domin baba yana cikin hadari"
A rikice innamu take dukta fita hayyacinta tace, "kai sale ka natsu ka gaya mana abunda yake samun malam, don Allah natsu karka saka in zare"
Ya kamo hannun innamu yana kuka sosai yace, "innamu likita yace ciwon daji ya samu baba, kuma yai masa mugun kamo wanda idan ba'ai gaggawar yimasa aiki ta hanyar yanke kafarsa ba ba tantama zamu rasashi, innamu kudin aikin kadai daya gaya mun yasa na sadakar baba mutuwa zai, innamu wai.......wai......mil.....miliyan biyu zamu kawo, innamu ina zamu sameta? Bamu tab'a ganin ko dubu dari ba sai yau da muka bada jinginar gidanmu, ta ina zamu nemo miliyan har biyu"
Innalillahi wa inna ilahir raju'un Allahumma ajirni fi musibati wa'aklif li khairan minha!!!
Abunda na keta fad'a ina nanatawa kenan yayinda na silale k'asa dab'as ko ciwo banji ba, hawaye ne suka k'afe mun miyan bakina ya dauke, kukan innamu da zainab kurin kakeji yana tashi yayin da halin da nake ciki bai misaltuwa.
Bamu san iyakar lokacin da muka kwashe anan ba saida mukaji ana korar mu wai ba'a zama anan, farfajiya muka fito mukai cirko cirko cikin shakakkar murya innamu tace,
"Yanzu a wane hali yake ciki?"
Jikinsa ya mugun saki yace, "yana dakin gaggawa ana bashi treatment, yace zasu kula dashi na kwana uku idan bamu kawo kudi ba zasu koremu tare dashi"
Na sharce hayawane nace, "innamu miye amfanin gonakin ku keda baba, asaida mana muga idan zasukai yawan da ake buk'ata"
Girgiza kai tayi tace, "tunanin da bake yanzu kenan, duk da nasan ba zasukai ba ko rabi basuyi amman kila idan sukaga mun kawo wadannan din zasu tausaya mana su ansa"
"Yanzu ya zamuyi ina zamu kwanta, idan asuba tai zan sabko inje inga yadda za'ai d'in"
Innamu tace, "ga wasu bayin Allah can nasan suma jinya suke, zamu tambayesu ko zamu rab'a gefensu, saidai kai bansan ina zaka kwanta ba"
"Aa innamu naga masallaci waje zanje na kwana acan, kuyi amfani da tabarmar hannunku kuyi maleji zannuwan da kuka dauko saiku rufa dasu akwai sanyin sosai"
Hakan ce ta kasance kuwa basu hana mu ba muka shimfida yar madaidaiciyar tabarmar muka rufa da zannuwan, zuwa can saiga yayanmu ya dawo yace,
"Naga ba wanda yaci wani abu cikinku shiyasa naje na siyo mana abu da yan canjin da suka rage"
Nace"yayanmu kaida zaka koma gezawa gobe? Kana bukatar kudi"
Murmushin karfin hali yayi mani yace, "zasu isa kanwata"
Duk da bamuda natsuwa haka mukaci muka sha ruwa sai bacci ya sacemu, don akwai gajiya da rashin isassar natsuwa muka dunkule waje guda daka gan mu dole mu baka tausayi.
**********
Ana gama asuba yaya ya tafi gezawa mu kuma muka tafi ganin jikin baba, Allah yaso anbarmu mun shiga saida bamu dad'e ba akace mu fito, tabbas ana bashi kulawa ina kyautata zaton inhar akai aikin zai warke da iznin ubangiji, don babu cutar da bata da magani.
Ba wanda bai kuka ba ganin baba kwance an saka mashi abun shakar iska,kafar kuwa an zaizayeta duk ta koma wata iri alamun jiya an tsotse ruwan an fitar an masa gyara saboda ya samu sauki,ga drip nan an mak'ala mashi bacci yake sosai.Fitowa mukai muka samu wajen hantsi muka zauna, da yake yayanmu ya bamu kud'in kalaci mutanen da muka kwana kusadasu naga yarinyar zata fita waje nace, "innamu bari na bita na siyo mana koda kunu da kosai ne"
"To ki kula dai"
"Kuma babanku ne baida lafiya ko?"
Inji yarinyar da bata wuce sa'ar zainab ba, murmushi nai mata nace"Ehy, kefa"
Sai naga zatai kuka tace, "muma babanmu ne muka kawo,ya samu lalurar shanyewar barin jiki saka makon faduwa dayai"
Cikin jimami nace, "Ayya Allah yabashi lafiya kibar kuka,duk zasu samu sauki kinjiko"
Ta d'aga kanta kurin mukaje muka siyo muka dawo, akan hanya ne take cemun.
"Kinsan me baiwar Allah, yayarmuce duk ta jawo wannan abun, saurayinta ta bari yai mata ciki taita b'oyewa ba asani ba daga karshe aka gane yanzu haka wannan watan take haihuwa, abunda ya jefa baba cikin wannan halin kenan...............
Mom muhseen✍🏻
YOU ARE READING
JANNAH
FanfictionKaddara abuce mai nauyi, kuma mai zafin gaske,ayayin da ta kasance mai kyau alokacin take da dad'i a yayinda tazo akan akasin hakan lokacin kakejin duk duniya babu wanda ya kaika fuskantar kalubale, Ku shigo cikin labarin anan ne zakuji LABARIN KADD...