14

174 25 5
                                    

*_💔JANNAH💔_*
   
_{A TRUE LIFE STORY}_

*E.W.F*

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

*FAUZARH ORGANIC SKINCARE*
            _PRESENT_

                   *5️⃣ DAY'S SKINCARE ONLINE TRAINING*

*💗ABUBUWAN DA ZAN KOYAR💗*

*da farko zanyi bayani akan ƙurajen fuska da abun da ke kawosu, da hanyar da za a bi wajen magance su*

*WHITENING BLACK SOAP*
*LIGHTENING BLACK SOAP*
*NATURAL BLACK SOAP*
*FACE AND BODY SOAP*
*BODY CREAM*
*SABULUN GYARAN AMARYA*

Wannan training ɗin tamkar gara6asa ne🤩 da naira ɗari ukun ki kacal za ki koyi sana'a.👌
*Zamu fara training din 5 ga wannan watan ne insha Allah*

*DUK GARIN DA KI KE ZAN SANAR DAKE INDA ZA KI SAMU KAYAN HADIN*

*Domin neman karin bayani a tuntu👉🏼http://wa.me/+2347065012071*

        🅿️.......14

Tilawar karin da akai mana na qur'ani nakeyi amman zuciyata duk ta kasu kashi-kashi, yar mitsilar wayar da yallab'ai ya ban tun randa nazo naji tana ta burrrr burrrr karkashin filona da nake sata, saurin tashi nayi na daukota bani da mai kirana sai shi kuma shima tunda ya ban ita yaune ya kirani.

"Assalamu alaikum"

Nai masa sallama da siririyar muryata,

"Yunwa zata lahantani Jann, ki kawo mun abincina, da abunda nace ki had'a mani"

"To yallab'ai gani nan"

Na aje wayar da hanzari na rufe qur'anin hijabin danai salla na saka da yake ba babba bace iya guiwa take, na had'a masa abincin sa da komi a cikin wani kyakkyawan dogon tire,bakin k'ofa mukaci karo da hindu ta dalla mun harara tanajan tsaki, uffan bance mata ba nai kamar banji ba na wuce wata kurin.

Allah yasoni falon babu kowa nai zuruf na shige bangaren nashi na kwankwasa kofar falon, kamar yana bakin kofar naji ya bud'e,usman ne mukai four eyes dashi ya sakar mun murmushi, wanda tunda nazo bamu ma tab'a had'a ido dashi ba.

"Shigo mana"

Ya tsinke man mamakina da na shiga, ahankali na rab'ashi na shigo falon yana kwance cikin doguwar kujera kamar marar lafiya, na aje tiren k'asa sannan na durk'usa ina gaidasa.

"Yallab'ai ina wuni? Ga abinci"

Bude kyawawan idanunsa yai akaina sun lumshe sosai sun rage girma, kasa dauke idona nai daga kallonsa yace calmly,

"Toki zuba mun pls"

Cikin sauri na zuba masa tuwon shinkafar don cikin kwanakin nan na lura yana son sa, miyar ina bud'eta tafara kamshi na zuba masa komi sannan nace,

"Na zuba yallab'ai"

Usman yana falon wayarsa kurin yake faman dannawa, saukowa yai k'asa kusada inda nake durk'ushe, duk yai wani kala dashi kamar na tambayesa meke damunsa amman sai nai tsit,
Tuwansa yafara ci cikin natsuwa lokaci zuwa lokaci muna had'a ido dashi, saidai in sunkuyar dakai kasa kawai kulli biyu yaci anan na tabbatar da yunwa yakeji sosai, ruwa ya dauka yasha sannan ya dauki bowl din fruit salad din yana sha ahankali, sannan ya dubeni cikin sassanyen kallo........."zanyi missing abincin ki"

Na sadda kai ina murmushi bance komi ba, yayin cikin raina ya fama mun inda ke mun ciwo don har bana son yin tunanin yadda zan kasance bayan tafiyarsa, wani iri nakeji a raina sosai.

JANNAHWhere stories live. Discover now