*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseenwattpad name
Humaira3461🅿️.......10
"Ka dauke ta kubar gidan nan tun kafin na fito ma na sameta, na gaji da kwaso yara agidan nan kazamai dasu sai sunci sunyi girma sun gyagije sannan suyi mana butulci, bazan sake daukar yar aiki inba tsohuwa ba ai na gaya maka tun wancen karon ko?"
Momyn ce take ta fad'a tun sadda ya shiga b'angarenta sanar da ita zuwan jannah, kasa cewa komi yayi saboda shi baison fad'a ko kadan, dagula masa lissafi yake.
"Momy Mai zai hana kiganta idan ta miki ba shikenan ba, kawai dai k
Matsalar a samu yar gidan talakawa kazamai suyita mana kazanta agida, bayan haka kuma waccen matsalar kuma sai adauki mataki"Kallonta momyn tayi tana cewa, "watau don Asaad ne yasa kike wani lauye baki kina tayasa begin ko?"
Cikin shagwab'a tace, "no momy babu dad'i kazo da mutu kuma ace ka maidasa"
Tashi yayi zai fita bai ce uffan ba harya bud'e k'ofar momyn tace, "yar inace? Inma daga kauye take tashin farko bazan dauketa ba gaskiya"
Atakaice yace, "kizo ki ganta saiki ida yanke hukunci"
Ya fice rai b'ace yana banko kofar, "jarabebben banza da wofi, ke kuma saina ci ubanki in kina samun baki idan ina magana"
"Momy duk kinsaka ransa ya b'aci don Allah, kefa kiketa complain akan yan aiki sun miki kadan, yanzu yaje ya samo miki ko ganinta bikiyi ba kinhau kushewa, taya zaiji dad'i"
Afusace ta dauki abu zata maka mata tatashi aguje ta fice daga d'akin.
Ina nan zaune zuciyata nata bugawa naga fitowarsa hada ido mukai cikin sigar kwantar da hankali ya lumshe mun idonsa, na rausayar dakai kurin wuri ya samu ya zauna yana dora d'aya kan d'aya ya cigaba da danna wayarsa, babu jimawa kamar daga sama saiga wata matashiya ta fad'o falon kamar anbiyota, tunda muka had'a ido da ita ta kafeni da ido kamar zata cinyeni, mamaki da rud'ani ya bayyana akan fuskarta araina kuwa addua kurin nakeyi, cikin rudewa take cewa "Asaad ina yar aikin? Wannan kuma bakuwa momy tayi ko kawar hindu ce?"
Batare daya kalleta ba yace, "itace wadda zatai aikin ai...........wannan kyakkyawar? Tabdijam ke kinganki a madubi kuwa? Ki rasa abun yi sai aikatau?"
Nidai uffan bance ba na maida kaina k'asa facing dina ta dawo kusa dashi ta zauna tana cigaba da magana, "Asaad Ina ka samota don Allah?"
Cike da kosawa yace, "pls Aneesa........karki samun ciwon kai"
Harararsa tayi tana maido idonta kaina tace, "kar Allah yasa ka fad'a idan momy tazo ai kayi magana, ke ya sunanki?............*JANNAH* sunanta"
Ya katse mun magana don harna bud'e baki zanyi magana kenan ya rigani,
"Wow sunan ma kansa mai dad'i..........wata budurwa ce ta fito daga wani corridor ba jimawa saiga momyn da ake magana,
Su duka kowa bakinsa asake yake kallona kamar an hura usur saiga sauran yan gidan suna fitowa daya bayan daya, jikina ya hau tsuma saboda idanun sun mun yawa............."wow she is so beautiful and cute, mommy is she her friend daughter? don bantab'a ganinta nan gidan b.................momy itace yar aikin da muke magana akai, Sunanta JANNAH makociyar su sagir ce bayan layinsu take, she is 21 years and she is in ss2 class, tana zuwa makaranta yanzu haka kuma tana zuwa islamiyya, munyi yarjejeniya da mamanta zata ringa zuwa makarantar ta duka, sannan after 3 months zata ringa zuwa ganin gida albashinta kuma ke zaki yanke in kuma ni zan biya saiki fada mun"Asaad ya tsine maganar khalid dayaketa santina da alama ya girmesa sosai, amman kuma baiyyi kama da mutum uku dana gani a wajen ba,
"Kai! Ni kake katsewa magana?"
YOU ARE READING
JANNAH
FanfictionKaddara abuce mai nauyi, kuma mai zafin gaske,ayayin da ta kasance mai kyau alokacin take da dad'i a yayinda tazo akan akasin hakan lokacin kakejin duk duniya babu wanda ya kaika fuskantar kalubale, Ku shigo cikin labarin anan ne zakuji LABARIN KADD...