16

140 23 4
                                    

*_💔JANNAH💔_*
   
_{A TRUE LIFE STORY}_

*E.W.F*

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

        🅿️.......16

Tun daga wannan lokacin nida Hindu muka zama abokai sosai har dakina zata sameni muyi fira sosai, don mun ware ranar da zamu ringa tilawa asabar da lahadi da daddare, saboda bana samun lokaci yanzu shukra sai taga dama take zuwa kuma ba komi takeyi ba, baba azumi kuma tayi tafiya zuwa kauyensu dagani sai babaah uwani kamar zan mutu idan akace Friday tazo, Fareeda da yaranta nan suke weekend dinsu kuma fa acikin garin nan take, ba karamar wuya nake ciba Allah ma yasani, shiyasa na rame sosai kayana duk sun mun yawa.

yaya usy rannan naga yanata kallona saboda yadda yaga duk na fige na lalace, time din na kawo ma momy gasashen naman da tasaka na gasa mata, fareeda ce take cewa bayan na juya baya zan shige ciki "momy wai baki lura da mutuniyarki ba? Duk ta bi ta k'are shegiyar"

Idonsu ya rufe sun mance da usman a falon momyn tana danna waya tanaa cin naman tace, "tukunna ma"

Murmushi fareeda tayi tana cewa, "ko kefa momy haka nake so, amman dai kinyi kamar bakisan meke faruwa ba"

Aneesa ce tai gyaran murya duk suka kalleta a siyasance tai masu nuni da usman dake cikin falon, mik'ewa kurin yai ya bar musu falon baice komi ba, kitchen na koma ina ta kokarin dora girkin dare ga gugar momy can dakina tana jirana kayan sunkai kala ashirin da biyar, in ban gamasu daga nan zuwa safe ba na shiga ukuna..........."Jannah"

Atsorace na juyo saboda ban zaci wani anan ba, kuma daman irin wanan lokacin khalid ke matsanta mun, yaya usy ne nai ajiyar zuciya nace "yah usy kana son wani abune"

Lumshe idonsa yai kamar yadda yallab'ai asaad keyi, naga kuma sunyi wani iri fuskar sa daure babu walwala cikin cunkusasshiyar murya yace, "mekikeyi?"

Nace"dinner zan had'a cus cus ce da miyar kaza sai salad dazan yanka yallab'ai khalid kuma yace yana son nai masa wainar fulawa"

Runtse idonsa yai yana kallona ya duba agogon kitchen din yace, "kinci abincin rana?"

Na girgiza kai ina sadda kaina kasa, ya sake cewa "kinyi sallar magriba?"

Nace"so nake na dora sai naje nayi"

Ransa a b'ace yace, "aje ki fito nan"

Idona a warwaje nace, "yallab'ai momy zatai fad'a idan ban girkin nan ba"

Wani kallo yai mun yace, "umurnin momy yafi nawa kenan? Nace umurninta yafi nau kenan saboda ita ke biyanki?"

Na rufe bakina kamar zan kuka nace "na ratse da Allah Aa yaya usy kayi hakuri"

Hanya ya nuna mun yace, "to zoki wuce muje"

Na aje komi jikina a mugun sanyaye na fito gaba ya sanyani har d'akina ya tsaya wurin mirrow yana kallona yace naje nai sallar, toilet na shiga nazo nayita duk yana cikin dakin, hankalina duk a tashe yake na sallame ko addua banba naga ya dauko mun wata jikka dake cikin dakin, ya bud'e wadrope dina ya dauko kaya ba adadi yanata zubawa, idona a warwaje na ke kallonsa harya gama sannan ya dubeni,

"Ki biyoni, salan kuma kiyi mun gardama"

Yai waje a guje na bisa bayan na rufe d'akin na dauko yar wayata da kullin saina duba kozan samu kiran yallab'ai asaad, afalon mukai karo da khalid yai mun wata fizga yana cewa,

"Gidan ubanwa zaki? Ina wainar danace kimun?...........saidai yaji ankaima hannunsa bugu daga fizgar dayai mun yaya usy ne kuma yai hakan, idonsa kamar wuta yake nuna sa da yatsa cikin kakkausar murya yace, "karka sake tab'a ta, ita ba asharariya bace irinka, waina kuma ha zatai ba aiba jakarku bace"

Ya nuna mun hanya yace "zoki wuce muje"

Fareeda tai saurin tashi tana shan gabansa tace, "ina zaka kaita usman? Ai nan shine dolenta tunda ta fito neman kudi, kuma dole tayi aiki kamar jakka tunda kudi take so, ko a banza zata samesu...........karki gaya mun magana ki kama kanki nan gidan mune, kije kiyi wannan ikon agidan mijinki amman ba nan ba, akan me zaku ringa azabtar da yarinya ehy? Meta tsare ku dashi to ba abunda ya dameki da inda zan kaita matsa ban waje"

Sororo take kallon sa tana nuna kanta zatai magana momy tace, "fareeda zoki wuce ciki"

Har ta fara magana tace, "momy yazaki.........nace ki wuce ko"

Afusace tai cikin bangaren momyn khalid yace mun yana zaro mun idonsa, "wuce kije kimun abunda na sanya ki ko in karyaki anan wajen...........idon yaya usy jajawur jijiya tafito kansa sosai yace masa, "ba zatayi ba, ni nace ba zatai ba inka isa kai wani ne agidan nan don Allah ka tirsasata tayi.........kai ni kake gaya ma magana zan ci ubanka yau inga abunda za'ai"

Dasauri momy tataso ta shiga tsakani ranta amugun b'ace cike da tsawa tace, "khalid shiga hankalinka nace ko! da usman din zakai fad'a kamar wani abokin ka?"

Cike da bala'i yace, "ehy dashi zanyi, ki kyale inci ubansa in ballashi inga abunda za'ai...........bakai ba ko ita bata isa ta tab'a fatar jikina dasunan duka  ba, don Allah kaida ita inkun haihu bismilla"

Wannan tashin hankali tuni ya sanya ni kuka ba abunda jikina keyi banda rawa kamar mazari, fuskar momy kamar an aiko mata da sakon mutuwa bata tanka ma usman ba, ta figi hannun khalid tace "wuce kabar nan wajen inhar nina haifeka"

Kamar kubu buwa haka yabar falon, ta juyo da kallonta akansa suna ma juna wani irin kallo kamar zasu cinye juna, sannan tace "idan baka son jawo ma kanka tashin hankali ka aje wannan jikkar kabar wajen nan, Janna aiki tazo kuma dole tayi aiki agidan nan tunda ni nake biyanta ba kyauta take mun ba, idan kuma so kake tabar gidan nan shikenan ka dauketa ku fita kagani"

Ta juya zata bar wurin yace, "ke awa zaki koreta agidan nan? Idan abaya kin kori wasu ita wannan baki isaba, kuma aiki zata dawo ta cigaba dayi kamar yadda tafaro amman ba irin wannan ba da kuke sakata kamar baiwarku, wannan karon duk makircin ki karya kike.
Jannah zata dawo daram amman saita huta sannan"

Ya dubeni yace "tashi ke kuma"

Dole na tashi ina jan majina nabisa har compound, motarsa ya bud'e yana kallona "shiga"

Kukana ya sake dawowa sabo na had'e hannuwana alamun rok'o da magiya ina cewa, "yaya usy ka taimaki rayuwata don Allah kayi hakuri in koma, bazan so wani rikici ya barke agidan nan sabodani ba, banzo don na ruguza maku zaman lafiya ba don Allah............please ya isheni don Allah ki shiga mota nace"

Shigar nayi gaba ya bud'e baya ya aje jikkata sannan ya rufe bai shigo ba naji ya tsaya yana waya, duk abunda ya faru yake sanar da Abba wanda yakai sati biyu baya garin, ko kadan abunda ya faru bai mun dad'i ba Allah yaga zuciyata bana nufin kawo rikici acikin gidan su.

********

"A yanzu ne lokacin da ya dace na dauki mummunan mataki akan wad'anan yaran, daman shirun da nayi bayana nufin abun baya mun ciwo bane, na bari abun yazo irin wannan matakin don haka ku dukan ku ban ce wani yayi yunk'urin yin wani abu ba sai abunda na baku oda, ku sanya idanunku daga nan har sadda zai dawo da ita koma ina zai kaita, yadda uwarsu tabar gidan hai hata hai hata suma sai sun barsa har abadan abidina, uban da suke tak'ama dashi har suke izgilanci suke mun abunda suka gadama na rantse da Wanda ya busa raina saina rabasu dashi"

Wata dariya khalid da fareeda sukai yana cewa, "yanzu nakejin ki uwata mai kaunata, wannan shine abunda ya dace kiyi mu kuma zamu zauna dakon jiran umurninki"

Fareeda tace, "momy hankalina bazai kwanta ba muddin baki had'a da wannan jajakuwar yarinyar ba, tsanar da nake mata zai iya sani nasa aka kashe shegiya"

Murmushi momyn tayi tace, "yaro dai yarone, inkika kasheta aka ganoki kema kashekin za'ai, tunda nace ku saurareni ku jira lokaci."

"Banso tabar gidan nan ban lasheta ba, tunda na dora idona akanta banda wani buri sai ganin na lashi zumarta, kyawunta kadai ya isa yaja hankalin duk wani lafiyayyen namiji akanta...........khalid ka rufen baki marar kunya kawai, koda wasa karna sakejin wannan maganar bakinka ku tashi kuje na gama magana daku".................





*ina sake bawa masoyana hakuri akan wannan jinkirin, kun san komi saida lafiya ina fatan Allah yasa lafiyar ta dore na cigaba da muku posting, gashi nan dai babu yawa ayi hkr*

Mom muhseen✍🏻

JANNAHWhere stories live. Discover now