*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseenwattpad name
Humaira3461🅿️.......11
Kamar wasa na fara sabuwar rayuwa a inda ko amafarki ban tab'a tsammani ba, idan na tuno kauyen mu na kuma kalli inda nake zaune sai dai ince ma Allah Alhamdulillahi, sai yanzu nake ganin yallab'ai Asaad baida wata manufa ta kawoni gidansu face cigaban rayuwata, domin daga sadda nazo zuwa yanzu ni kaina naji na d'an canza ba takurawa ko kadan, idan kaga an zageka kai kayi ba daidai ba ina fatan Allah ya bani ikon yimunsu daidai bakin kokarina, dakina kamar dakin amarya haka yake single room ne mai dauke da madaidaicin gado 6by6, ga wadrope mai guda biyu ta gadon sai madubi da toilet, babu abunda babu acikin dakin, har Ac dai akwai sannan sutura gasunan an aje sai dai ja zab'i wanda nakeso na sanya, wasu sun mun yawa saina ware su na aje idan na samu dama naje ga tela ya gyara mun,b'angaren aikina kuwa na saki jiki bakin rai bakin fama ina koyo don ma Allah yayini mai saurin fahimta, idan naga kuma abun zai mun wahala saina rubuta yadda bazan mance ba, inajin dadin aiki da babaah uwani matar akwai kirki ta daukeni kamar yarta, nima haka nakejin ta kamar innamu, kwana na biyu da zuwa mukaje da yallab'ai makarantar da zan cigaba da zuwa yai mun dukkan abunda ya kamata aka bani A class ss2, duk daukata makarantar gwamnati zai kaini sai na ganni wata Private ta had'u makatantar sosai gaskiya, a ranar kuma yai mun register a wata islamiyya dake nan cikin unguwar ba nisa sosai amman duk da haka sai na hau abun hawa kafin naje, washegari kuma saiga uniform dana bokon dana islamiyyar ina kitchen lokacin da daddare ne abunda zanyi ma Abba tuwon alkama da miyar danyar kub'ewa, shiyasa babaah uwani ta sakar mun aikin saboda ganin nayi masa ranar danazo ba asamu wata damuwa ba, miyar nake had'awa lokacin tasha naman karamar dabba sai k'amshi take sai naji kamar mutum tsaye bayana, gabana yai mugun fad'uwa saurin juyawa nai a firgice har ina yadda ma burkin hannuna,
Wannan sarkin ikon ne yallab'ai khalid ga isa da shegen fad'a, sannan ya faye kallo da yawa."Ohhh I'm sorry na baki tsoro ko?"
Ajiyar zuciya na sauke ahankali ina risinawa wajen ce masa,
"Ina wuni yallab'ai"
Wajen frig ya wuce yana bud'ewa yace, "lafiya, me kike girkawa?"
Cikin rashin sakin jiki dashi nace, "Abba nake ma tuwo na gama miyar nake kad'awa"
Jinjina kai yayi yana zuba ruwan a cup yana sha, so nake yabar kitchen din na cigaba da aikina, ina juyawa zai cigaba da kallona hakan yana samun faduwar gaba........."ki cigaba da aikin ki mana"
Jikina a amace na juya ina cigaba da aikin amman tabbas inaji ajikina kallona yakeyi, Allah ne ya ceceni ya jefo yallab'ai Asaad kitchen d'in, yana ganin sa yaja wani dogon tsaki yana wuce wa ya fice binsa da kallo yallab'ai Asaad yai harya fice, kashe gas din nayi ina juyowa muka had'a ido fuskar sa babu annuri yake kallona, sai na sadda kaina k'asa ina risinawa nace,
"Ina wuni yallab'ai"
Kin ansawa yai ya juya yana cewa "ki sa meni part din"
Dafe kirjina nayi ina ambaton sunan Allah, wadannan mazan suna son haukatani, shirya tuwon nai cikin wormers miyar ma na juye ta cikin cooler na jera su cikin wani dogon tire kayatacce sannan na dauka na nufi can bangaren momy saboda da dare acan yake dinner,
Knocking nayi daga bakin k'ofar, bud'ewa akai naga Anty Aneesa na gaidata tana yatsina ta amsa mun,"Daman Abincin Abba ne na kammala"
Hanya ta bani na wuce cikin falon momyn tana zaune kafa daya kan d'aya, na isa inda nake ajewa na ajiye ina risinawa na gaidata,
"Momy ina wuni"
"Lafiya lau jannah sannu da kokari"
Na amsa mata da "yawwa nagode"
YOU ARE READING
JANNAH
FanfictionKaddara abuce mai nauyi, kuma mai zafin gaske,ayayin da ta kasance mai kyau alokacin take da dad'i a yayinda tazo akan akasin hakan lokacin kakejin duk duniya babu wanda ya kaika fuskantar kalubale, Ku shigo cikin labarin anan ne zakuji LABARIN KADD...