24

159 19 10
                                    

*_💔JANNAH💔_*
   
_{A TRUE LIFE STORY}_

*E.W.F*

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

        🅿️.......24
  
      *MAI AFKUWA!*

Bakina yayi mun nauyi balle har na iya bud'esa nace wani abu, yaud'in tazo mun amugun bazata meke faruwa damu? Duk kauce kauce na wannan ita ake kira *_SOYAYYA_* yah salam! Daman haka soyayyar take, tabbas babu abunda yakaita zak'i, hakan kuma ba abunda yakaita d'aci da k'unci saboda murzar yatsuna da nake har sun fara mun zafi sosai..............hannunwan sa kurin naga yasa ya rik'esu duka yana cewa cikin tausasawa, "karki jima kanki ciwo fa"

Tilas na kallesa shima yana kallon cikin idona duk yadda naso hana kwayar idona cigaba da kallonsa kasawa nayi, jinake kamar idan na daina kallonsa suma zanyi, yadda ya rungume hannun nawa kamar sune rayuwarsa numfashina kansa bana shakarsa yadda ya kamata, kamar wata maganad'isu ce take fizgata zuwa ga idonsa.

Tabbas idan bai amayar da abunda ke cikinsa ba zai iya ajalinsa, yana jin labarin soyayya kala daban daban amman bai san haka akeji ba saida ya d'ora idonsa akanta ranar farko, tunda zucuyarsa ta doka a lokacin har yanzu bata dawo masa yadda take ba, jin alamun zan anshe hannuwana yasa yaja wata ajiyar zuciya cikin disasshiyar murya yace,

"Please jann ki kasance dani har karshen rayuwata, duk randa na rasaki zan iya rasa rayuwata ganinki da wani namiji koba usman ba zuciyata ce take bugawa fiye da kima, inaji kamar na had'iyi raina! Yau d'in nan da ace bana tare dake bayan abunda ya faru zan iya zaucewa, please jann kice mun ba zaki sake sauraren sa ba"

Da fari kamar gizo idona keyi danaga kamar kwallace kwance cikin idonsa,sai danaji d'igarsu bisa hannuwan mu dake sarke yasa naji wani iri na runtse idona, har wani haki nake nace ina shafo ruwan daya d'iga kan hannuna,

"Yah Asaad minene wannan? Yah Asaad kamar kwalla kake fitar wa, don Allah kace mun ba hawaye bane ba karka saka na zargi kaina akan haka, Yah asaad ban cancanci haka ba nifa bakowa bace bakuma yar gidan kowa bace, meyasa zaka zubda hawaye akaina?...........nai idasa maganar inajin nima hawayen suna cika idona, makale d'ayan hannun nawa yai yana cewa.

"Ke kike ganin cewar ke ba kowa bace, sannan kin wuce duk yadda kike tunani azuciyana jann, tsoro nakeji ban tab'ajin tsoro irin wanda nakeji ayau ba,jinake kamar za'a rabani dake hankalina ya kasa kwanciya idan har ban amayar da abunda nake ta dakonsa ba yau bazan iya runtsawa ba kamar zai iya ajalina, ada ban shirya sanar dake halin da bake ciki akanki ba saboda burina kiyi karatu sosai zuwa lokacin zuciyarki zata iya daukar wannan nauyin da nakejin zuciyata dashi, sai naga ashe bazan iya hakuri ba,ashe *kaunar* da bake miki tafi karfin na iya sarrafata saidai ita ya sarrafani, inaso ki rik'e a ranki cewar duk runtsi bazan tab'a daina *Sonki* ba, don had'e yake da jinin jikina saidai idan nine na mutu..............zuwa lokacin hawaye har bisa hijabina sosai nake shashshekar kukan, girgiza kaina nake cikin tsananin firgicin sauraren kalamansa, ina cewa "kadaina ambatar mutuwa bana sonta, bana kaunar ta dauke ka saidai ni ta daukeni, bana fatan ganin ranar har abadan, Yah Asaad bana ji araina zamu kasance tare bana jin cewar *SOYAYYAR DA MUKE MA JUNA* zatai kai mu ga nasara tsoro nakeji, Yah Asaad tsoron nakeji sosai araina akan zan iya rasaka akowane lokaci, bansan meyasa nakejin haka ayau d'in nan ba amman ina fatan koma menene karya rabani dakai, ayau na tabbatar ma kaina dacewar da kaunarka numfashina yake fita, duk bugawar zuciyata tare da Sunanka take bugawa a yanxu danasan matsayin da nake dashi a zuciyarka sai nakejin kamar nafi kowa sa'a arayuwata, ina rok'on alfarma agareka karkayi jinkiri wajen cikar burinmu, kaje ga baba ka nemi aurena hakan shine zai katangemu daga nesantar juna.........."

Kukan nake sosai saboda abun yazo mun kamar daga sama, wai daman haka soyayyar nan take? Kuncin ta yafi dad'inta yawa, duk yadda baya cikin natsuwarsa bai hana shi lallashina ba, yana duba agogo yace "dare yayi sosai jann ya kamata kishiga ki kwanta, zuwa safe komi kenan zan sanar dake plz kimun alkawarin dakinje bacci zakiyi, karki saka dogon tunani aranki kinji"

JANNAHWhere stories live. Discover now