12

148 15 3
                                    

*_💔JANNAH💔_*
   
_{A TRUE LIFE STORY}_

*E.W.F*

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

        🅿️.......12

Kamar yadda nayi ma momy alkawarin zan ringa gyara dakin yallab'ai khalid, gari na wayewa ka sancewar lahadi ce na tafi wajen babaah uwani harta fara kokarin shirya karin safe, na wanke hannuna na kama mata munayi muna fira Irish ne muka fere da doya, duka soya su za'ai da kwai sai nafara kokarin yin hakan, sai ta ce mun "karki manta yallab'ai Asaad baya son dankali da kwai a had'e ki fara soya masa nasa daban, sannan ki soya sauran doyar kuma sai anyi masa yar miya da ita yake had'awa"

Na amsa mata da to, ni nake soye soyen ita kuma tana had'a costand da kunun alkama da kuma kunun gyad'a, ga wanke wanke harya tasu maiyinsa bata zo ba gashi da Momy tafito ta ganshi fad'a zatai,

"Wai nikam babaah uwani meyasa shukra bata kwana ne? Tana makara wajen zuwa kinga kuma aikinta yana bumatar sabko"

"Uhmm murjanatu kenan hakan taga yafiye mata alkairi shiyasa,"

Sai ban sake maganar ba saboda dai daji kasan akwai wani dalili mai karfi a k'asa, ina gama soye soyen tace akwai kaji da za'ai farfesu, a k'age nake na gama na fara share sharena dana tuna zanje dakin yallab'ai khalid hankalin tashi yake, ganin duk a rikice nake ina ta sauri tace "kinga jeki kifara aikin zan idasa"

"Yawwa nagode sosai babaah ta"

Tana dariya na wuce nai cikin gidan falukan na fara gyarawa duk da kuwa babu abunda sukai, kawai dai tsabar tsafta ce irin ta momy, ko na nok'e ince nayi zata gane don har lakutowa take ko zataji kasa kasa, don ma Allah yayi ni mai hanzari dan danan na kammala da falukan, kamar an jefo hindu sai gata ta fito da kayan islamiyyar ta kalar nawa ta wurgo mun,

"Yanzu-yanzu nake son ki goge mun su"

Dauka nayi kurin na wuce d'akina, taga abunda Anty Aneesa ke mun dole itama zata koya ai, na shimfid'a kayan gugar na zauna na gogesu tas daman jiya ban bacci ba saida na goge nawa, addua nake kar Allah yasa a jinmu guda da ita don bazan sake ba sosai.

Don sai goma muke tafiya islamiyar aida bansan ya zanyi da ayyukan gidan ba, inayi ina tunanin tafiyar yallab'ai a gobe dana tuna sai inji jikina duk yai sanyi,Allah ya sani ban son ya tafi ina kallonsa a matsayin bango majinginata, shine nake dan jin dadi idan ina tare dashi amman bacin shi duka ni tsoro ma suke bani, kayan na dauka na wuce inkai mata sauki na yau shukra ce zatai gyaran dakuna dakin yallab'ai ne zan gyara shi kuma ance sai ten yake tashi, kenan dai saina dawo daga islamiyyata sannan.

Kwakwansa mata kofar nayi tace na shigo, tana ta wayarta na aje kayan zan juya tace, "waye zai gyara dakin?"

"Shukra tana zuwa itace da aikin yau,"

Ina gama fadar haka na juya na fice bazan bari ta rainani har haka ba, idan Anty Aneesa tayi mani ita wannan ta kusan haihuwata ma ita kuwa inma ta girman yan watannine don ko shekara banajin ta bani, shirya dining nayi don in weekend ne su duka sukeyin breakfast a tare sai idan wani bai tashi ba, na kammala komi kan lokaci naje nai wanka nazauna ina shiryawa, hatta kayan shafata na musamman yallab'ai ya siyo mun, duk da iyayen kayan kwalliyar da nakeda su a dakin banayi, bana make-up ko kadan daga mai sai farar powder saboda rage maik'on fuska, sai fa turare shima d'in kadan nake sawa yadda ni kad'ai zanji, doguwar rigace akai min da hijab iyakar guiwa sai safuna da nik'ab, naji dadin nik'ab din sosai yadda zan rufe fuskata ba tare da mutane sun ta yimun surutun kyauna ba.

Kayan sunyi mun kyau ainun murmushi nayi yadda naga ina canza wa ahankali, duk da ba wani dad'ewa nayi ba kalaci naje na dauko nazo nayi anan d'aki na gama nafita da kwani kan, sannan na nufi cikin gidan, duk suna dining har da Abba yallab'ai khalil ya tashi shima yana a wajen, sai kuma yallab'ai Asaad.

Cikin girmamawa na risina nake gaida Abba da Momyn yace mun, "kece jannah kenan"

Ina durk'ushe kaina kasa nace, "ehy Abba nice"

"To sannunki girki yayi dad'i, sai islamiyya ko"

"Ehy Abba"

Kud'i ya ciro aljihunsa yana mik'o mun yace "ki hau abun hawa tunda da nisa"

kasa ansa nayi ina cewa, "Kabarsu Abba zanje a k'afa ma"

Momy ce tace, "ansa mana ana baki"

Na mik'a hannu cikin girmamawa na amsa ina godiya, har na mik'e naji yallab'ai khalid yace "momy baki gaya mata ta ringa gyara mun b'angarena ba?"

Gabana ya fad'i momyn tace, "jannah ya mukai dake jiya?"

Hankalina ya tashi nace, "kuyi hkr don Allah, babaah uwani tace mun sai goma keke tashi shiyasa na bari dana dawo saina gyara...............momy na gaya miki wannan yarinyar ta fara samun gindin zama, har ta isa asata abu tace saita dawo"

Kaina k'asa bance uffan ba, hindu tace "nima ai yau bata gyara mun daki ba wai ai shukra ce zatayi,"

Jikina rawa kurin yake saboda yadda suke ta magana cikin masifa, yallab'ai asaad kamar baya wajen shida usman, Momy ta aje spoon din hannun ta tace,

"Mena gaya miki randa kikazo? Bance miki muddin bakiyi ida aikin ki ba babu inda zaki ba?"

Muryata na rawa nace, "kin gaya mun don Allah kuyi hakuri"

"Maza kije ki idasa aikin sannan kitai makarantar tun kafin ki fara ganin b'acin raina,"

Ina rawar jiki nai hanyar dakin nashi injin kuka na son zuwar mun ina dannewa,

"Abba Jannah ba zata ringa gyara masa daki ba, ai yana da mai masa aiki miye zai saka ace sai ita? Kuma a daidai lokacin tafiyarta makaranta a tilasta saitayi, duka awa biyuce sun tashi idan ta dawo ba sai tayi ba, to na hanata gyara dakin daga wannan ba zata kuma ba, wallahi idan aka sake sakata gyaran dakin wannan gardin duk abunda nayima mutum shiyaso"

Abba baice komi ba saida Asaad yakai aya sannan yace, "Momy ayi hakuri a kyale jannah da gyaran dakin khalid, tunda John yana yi masa ya cigaba dayi kawai"

Uffan bata ce masa ba hakan ya nuna ranta yai kololuwar b'aci, ba wanda ya sake magana a wurin har Hindu ta gama usman ma ya tashi,

Ba wata tsiya ke cikin dakin ba tsabar takurawa ce kawai, ban dad'e ba na gama na fito sannan momy ce da Aneesa a falon, gabana yana fad'uwa nace, "momy na gama zan tafi saina dawo"

Kallona kurin tayi sannan ta jinjina kai,nai waje ina ajiyar zuciya tsaye suke jikin mota suna magana shida usman, na rab'asu zan wuce naji ya kira sunana.

"Jannah"

Dawowa nayi ina sake gaidashi yace, "shiga mota mu saukeki"

Banyi musuba na shiga baya su suna gaba, usman yake jan motar suna cigaba da maganarsu wadda bansan akan me sukeyi ba, har cikin makarantar muka shiga muka nufi office d'in malaman, dukkan littatafan da sukeyin amfani dasu aka siya mun sannan ya had'ani da class master dinmu, bayan mun fito zan tafi aji ne ya tsayar dani.

"Usman gobe zan tafi, kuma zan bar amanar Jannah a hannun ka kai ne kake zaune kullin,kasanya ido akanta  abunda ya kamata ka tanka akanshi idan anyi mata kayi magana, idan kina bukatar wani abu ke kuma ki samesa karki ji komi ki masa magana, kai ne nasan baza'a samu matsala daga wajenka ba"

Yace"ok broth insha Allah"

"Sannan duk sadda zaka fita lectures inhar bata tafi makaranta ba ka tafi da ita, randa kuma bakaz fita saika bata kudin hawa napep"

"To broth noted insha Allah"

Ahankali na risina nai masa godiya sannan nan na tafix class, akai daidaitoni ajinmu guda da hindu ban nuna na ganta ba,na samu second sit na zauna ranar qur'an akai mana da hadith surar da muke tuni na gamata ni tuntuni, hadith din ma na gama shi duka banda wata damuwa anan, shabiyu da kwata aka tashi na hau abun hawa daker na gano unguwar.




Mom muhseen✍🏻

JANNAHWhere stories live. Discover now