*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseenwattpad name
Humaira3461🅿️.......18
Kafin lokacin da yace zaizo yayi gaba d'aya ja rasa sukunin zuciyata, na kasa samun matsaya akan inje ko kar inje, gashi dai na amsa masa cewar zanje d'in to amman inajin tsoron binsa, bana zargin sa cin amana amman kuma wannan rawar k'afar da yake akaina fa?
Sannan a matsayin wa zan bisa Kanwa? Ko kawarsa? Kome...........rufe idona nai na kwanta kan gadona ina ta tunanin abunda ke faruwa dani, yah usy ya kasance mai kyautata mun da abunda nake so da wanda ma ban nuna inaso ba yimun yake, da karfin sa da kuma aljihunsa duk da nasan yallab'ai yana tura masa dukkan wasu kudi da zai mun hidima dasu, amman nasan wani abun da nashi yakeyi, don ma sun kammala exams dinsu ta final kwanakin baya shiyasa yake samun lokacin kulawa dani, aganina kulawar kamar taso tayi yawa amman idan na tuna kalaman yallab'ai kafin tafiyarsa sai inga yana yin abunda ya dauki alkawarinsa ne,..............shigowar Anty munirat yasa nai saurin tashi zaune tace,"Kina son zaman daki Jannah bakijin komi"
Murmushi nayi nace "hutawa dai nake Anty, naga ba abunyi shiyasa"
Zama tayi tana cewa "ramma ta gama komi ai karki damu, yau nake koma wa night duty na usy yace zakuje party birthday dinsa ko?"
Na sadda kaina cikin sanyin murya nace, "dazun yake gaya mun, ni dai bana son zuwa Anty gashi na riga na amsa mashi"
Murmushi tayi tace, "ba wani abu insha Allahu karki damu, na yadda da usy sosai kije d'in idan yazo gashi yace na baki yanzu ya shigo ya fita,"
Jikina a sanyaye na anshi ledar da take bani nace, "Anty yah usy duk ya canza mun wallahi"
Dariya tayi tace "mekika gani ke?"
"Anty da ba haka yake ba, abu kadan indai akaina ne yanzu karki so kiga yadda yake rawar jiki akansa, sannan yaita yin wasu abubuwan da ni bana ganewa ni bana son hakan"
Kamar zan kuka nake maganar saboda har zuciyata bana son ya canza wannan alak'ar,
Rik'o hannuna tayi cikin lallashi tace,
"Karki tada hankalinki, ke amanace hannunsa kisama ranki babu wani abu tsakaninki dashi face matsayin yayanki ke kuma kanwarsa, da ace baki ansa masa zakije ba zan hana ki zuwa ne amman kin ansa idan kika ce baki zuwa yanzu zaiji babu dadi, ki dai kame kanki kinjiko wannan gown ce da zaki sanya, yace in tambayeki size din takalminki"A sanyaye na amsa mata da cewa "36 or 37 duk ina sawa"
Saida ta sake kwantar mun da hankali sannan tatafi, na bud'e kayan ina dubawa kyawunta ya dauki hankali ainun red and black GE gown din, tashi nai na kangata ga jikina tsaf kuwa naga tsawon yai daidai dani, nai mamakin yadda ya san size din tsawona haka saina tuna rannan dana rakosa zai tafi gida har na juya ya tsaidani, inda nake ya karaso ya daidaita tsawonsa dani alokacin naji tsoro sosai yadda kusancin namu yai yawa haka, duk tsayina iyakar kirjinsa nake banma karasa ba kadan, yai murmushi yana cewa "Ashe ma ke yar gajerace na zata kinfini tsayi ai"
Ashe daman don ya gane tsayin rigata, harda wani net ajikinta hannun ma net ne ajiki ana ganin fatar jikin, har da veil acikin ledar sai wani dan box na sark'a silver mai dauke da sarka da yan kunne harda zobe,kayan sun burgeni sosai da sosai ainun dagani kuma zasuyi kudi sosai, maido kallona nai ga zoben azurfa ta da yallab'ai ya bani alokacin da muke bankwana, lumshe idona nayi sannan cikin sassanyar murya nake cewa a fili, "yallab'ai ban san iyakar lokacin da zan dauka wajen tunanin ka da kewar ka ba, zuciyata kullin da sabon abu take tashi akanka, har yau na gaza tantancewa na kasa sanin inda zuciyata ta nufa akanka, sannan ga kuma wani sabon abun makamancin irin naka daga d'an uwanka, ina fatan zaka mun uziri banda wata hanyar tserewa lamurransa, amman alk'awari na ne bazan tab'a bujire maka ba"
YOU ARE READING
JANNAH
FanfictionKaddara abuce mai nauyi, kuma mai zafin gaske,ayayin da ta kasance mai kyau alokacin take da dad'i a yayinda tazo akan akasin hakan lokacin kakejin duk duniya babu wanda ya kaika fuskantar kalubale, Ku shigo cikin labarin anan ne zakuji LABARIN KADD...