*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseenwattpad name
Humaira3461🅿️.......7
Bubbuga kofar da ake yasa nai firgigi na diro ina bud'e kofar tsaye yake duka hannuwan sa cikin aljihun wandon sa na suit din daya saka dazun, idonsa kurr akaina sai zare ido nake kamar an rik'e bakina na kasa cewa uffan, ashe wajen saukowa na baro kallabina acan, sannan da zan kwanta na cire hijabina kamar an tuna tar dani na juya da sauri ina figar hijabin na saka ina hadiyar wani miyau nace,
"Kayi hakuri yallab'ai bacci ne ya daukan"
Idonsa ya lumshe sannan cikin sassanyar murya yace, "kiyi salla sai mu wuce"
Harya ya juya ya dawo yace, "please kiyi sauri fa"
Kai na d'aga masa kamar wata sakara, ajiyar zuciya na sauke na je nayo alwalla na kabbara sallar, koda na gama saida nayi azkhar dina na yamma sannan na fito ahankali nake karema corridor din kallo, anbi an k'awata sa da abubuwa masu kyau, a falo na iske sa zaune computer ce yake ta dannawa sallama nayi masa sannan na risina yadda nake idan ina gaida babba,
"Yallab'ai ina wuni, na fito"
Sakin fuskarsa yai ya amsa mun cikin kulawa,naga alamar mutum ne shi mai son girmamawa rufe computer yayi yana cewa,
"OK muje daman ke kadai muke jira"
Binsa nayi har waje saida na fito ya rude k'ofar entrance din yana tilla ma driver makullin, ya cafe yana bude motar ya adana sa, kamar yadda muka zo dazun haka muka tafi yanzu ma.
Ko acikin motar wayarsa babba mai kyau yake dannawaa wani lokacin kuma yana ansa kiran waya, na fahimci normally nature dinsa ne wannan sanyin jikin, sa yin abu cikin natsuwa sosai bayada hayaniya ko kadan, ko magana yake silently yakeyi inyana waya saika natsu sosai inkana kusa dashi kakejin abunda yake fad'a, lab'e baki nai nace araina halan haka yan gayun suke?
Wata unguwa muka shiga har kofar wani babban shago wanda akai zane a kofar shagon ana make-up, ana gyaran kai ana wankin k'afa da gyaran jiki, mamaki nake jin motar ta tsaya anan me mukazo yi anan to???
Waya naji yana yi yana cewa, "muna waje fa, karkice baki nan bacin munxo"
Sauke wayar yayi yana kallona kamar yadda na keta kallonsa, saboda ina son karin bayani ganin munata kallon juna baice komi ba dole na kauda kaina wajen taga,can naji yace dani.
"Jannah"
Nikam na kasa sabawa sa wannan sunan wallahi,amman ya zanyi dole na amsa ba tare dana dubesa ba,
"Na'am yallab'ai"
"Za'ai miki saloon anan yanzu da wasu abubuwan, bana son naje dake gida aimiki abunda zai b'ata miki rai, shiyasa na jinkirta tafiyar zuwa gobe idan aka gama zan dawo na daukeki"
Rausayar dakai nayi inajin zuciyata na kerma,meyasa zai anyi mun duk wannan sannan zai kaini? Yar aiki fa zanje dole sai anmun wannan, jin nayi shiru ya sashi cewa.
"Jannah please"
Saurin kallonsa nai idona na son tara ruwa, ni duk ya sakani acikin ko kwanto yana samun zarginsa, yana samun rashin yadda akanshi, cikin rawar murya nace "yallab'ai aikatau fa zanje, meyasa sai anmun wani gyara???"
Lumshe idonsa yayi yana bud'ewa ya shafa kanshi sannan yace, "ba zaki gane ba, amman idan munje zaki fahimta kiyi mun alfarmar wannan wallahi babu cuta araina"
Na sadda kaina k'asa jin yadda yake mun magana cikin tausasawa da marairaicewa, ahankali nace masa "shikenan na amunce"
Fitowa mukai muka shiga shagon babbane sosai don ankillace ko ina da labule, ciki da falo ne ga kayan aikin su nan burjik,wata matashiya ce ta fito daga ciki bakinta a washe take cewa,
YOU ARE READING
JANNAH
FanfictionKaddara abuce mai nauyi, kuma mai zafin gaske,ayayin da ta kasance mai kyau alokacin take da dad'i a yayinda tazo akan akasin hakan lokacin kakejin duk duniya babu wanda ya kaika fuskantar kalubale, Ku shigo cikin labarin anan ne zakuji LABARIN KADD...