Chapter 7-8

82 6 0
                                    

🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️

*NI DA YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

Zainab Habib/Mom Islam

P 7-8

Farfesun kaza ta gani yaji manja ,waro ido tsohuwa tayi kana tace "Ramatu a gidan wa kika samu nama ?"naga kinje nemo min saurayi ne ,shine farinciki ya kamani nakeson nima in saki farinciki shine nace wani almajiri ya yankamin wanan babban zakaran naki "rakwab tsohuwa ta mayarda murfin kwano ta ajiye har idonta na ruwa tace "dan kutumar uwarki dan bazan zagi uban ba tunda nawane mun haɗa kuɗi da Lami ne ?"Ramu dai tana ta kallon tsohuwa tana ɗura mata zagi, tsohuwa ta ɗauko cinya ta lashe romon dake shirin zubewa a ƙasa tana cin naman tana faɗa , bayan ta cinye na hannunta ta kurma ihu ,Ramu tace "tsohuwa mai ya faru ?tsohuwa dake ci gaba da cin nama tana kuka tace "wlh Ramu kin taƙaitani wlh kinci bashi ,duk inda zanyi dan bikinku ya kan kama sai nayi ,saboda inje in maido kuɗin zakarana a gurin Zaiyyanu "ita dai Ramu babu bakin magana tana gudun ta cika magana tsohuwa tace "zata fasa shige mata gaba akan saurayin , sai da tsohuwa ta cinye na kwanon tass ta shanye romo ta suɗe hannu sanan ta kalli Ramu tace "ina ragowar ?"Ramu dake shirin miƙewa tsohuwa ta bita da ido , Ramu na fita tsohuwa tace "ai duk wanda fito daga tsatson Lami dole sai yayi kwaɗayi ,badan kwaɗayi irin na Lami ba da tuni Bashir ya gina gidan sama mai hawa dubu "shigowar Ramu ne yasa tsohuwa yin shiru da maganarta ,sakamakon tukunya data gani an ɗauko , ajiyewa a gabanta Ramu tayi ta buɗe ,tsohuwa da kwaɗayi ke tunzurata ta leƙa tukunyar abin data kuma gani a karo na biyu ne yayi matuƙar firgitata har sai da nunfashinta ya ɗauke ta ɓingire a gurin sumammiya ,salati Ramu ta doka tana shirin kuka taje ta ɗibo ruwa a randa cikin kofin silba irin manyan nan ta sheƙawa tsohuwa duka a jikinta tana cewa "sannu "ajiyar zuciya tsohuwa tayi kana ta kalli kofin silban gabanta ta tureshi gefe tace "wanan ruwan ko mutuwa nayi ai dole na farfaɗo sbda wanka da kikayi min "murmishi Ramu tayi ta nemi guri ta zauna , kwararo amai tsohuwa ta fara kamar ,zata amayar da kayan cikin nata ,sai da tsohuwa tayi mai isarta sanan ta jijiga kai tace "naci wahala Ramu zaki kasheni "Ramu dake tsaye me zatayi banda dariya ,ta dinga ƙyal ƙyalewa tana tafi , kwanciya tsohuwa tayi kan ledar tsakar ɗakinta tana murƙususu alamun ciwon ciki ,sbda bata yarda da wanan abin da taci ba kuma a tarihin rayuwarta bata taɓa cin wanan abin da Ramu ta dafa ba sai yau , ganin tsohuwa na shirin margayawa yasa Ramu zaro ido tana shirin kuka ta fice da gudu , kai tsaye kemis ta nufa ta samu shi kaɗai ne a ciki , ko sallama batayi ba ta faɗa tare da cewa "dan Allah kazo ka duba tsohuwa wlh ciwon ciki ke damunta "Zaiyyan dake sarrafa system ɗinsa ko ɗagowa baiyi ba bare ya kalleta yadai ji ance tsohuwa , ihun data kurma ne yasa shi ɗagowa idonsa yana cikin siririn farin gilashi mai kyau yace "ku kullum damuwoyi sunyi muku yawa ita me taci kuma ?nama mana "Ramu ta bashi amsa idonta shaɓe shaɓe da hawaye ,Zaiyyan da mamaki ya kamasa a fili yace "ikon Allah ku kuma nama ne ke lalata muku ciki to lu daina ci mana dole ne "kai naman Mage ne fa nayi mata farfesu saboda taje nemomin...sai kuma tayi shiru ta juya da gudu , komowa gida tayi ta sami tsohuwa kwance tana ta mutsitsikuwa ta shiga uwar ɗakinta ta ɗauko wayat tsohuwar ta danna number babanta , ring ɗaya baba ya ɗauka yace "baba ina yini ?Ramu dake shirin ƙara fashewa da kuka tace "baba nice tsohuwa babu lafiya "waro ido baba yayi kana yace "to gamu nan tahowa ".
Da sauri baba ya fito tsakar gida ya sami Lami tana haɗa wutar da zata soya waina , cikin firgici yace "Lami baba babu lafiya maza tashi muje "cikin ko ɗarr Lami tace "jeka ina nan biyoka kana gani wutar taƙi kamawa "baba bai jira jin mai zata ƙara cewa ba ya fice , sauri yake kamar zai tashi sama ,tsabar ruɗewa gani yake mashin bazai fishi sauri ba shiyasa ma bai hau ba , cikin ikon Allah ya iso gidan ,tura ƙofar yayi kana ya faɗa gidan ,yana shiga ya sami Ramu a zaune a tsakar gida ta rafka tagumi , baba dake mayar da nunfashi yace "ina take ?Ramu ta nuna ɗakin tsohuwa ,baba na shirin buɗe labule yaji sallamar likita ya dawo da baya ya miƙawa likita hannu suka gaisa ,likitan ya shige ciki .

Da shigarsa yaga tsohuwa na kwance ido ya kakkafe ,ya nemi guri ya zauna tare da ciro abin gwajinsa ,zai gwadata ta kamo hannunsa ta riƙe muryarta bata fita sosai ta ɗaga kai ta kalli baba tace "Zaiyyanu ka riƙemun amanar Ramu ko bayan raina kaine mijinta ,kai kuma Bashir ban amince a aurawa Ramu wani ba inba Zaiyyanu ba wlh inko ba haka ba banyafe b...baba yai saurin rufe mata baki idonsa ya kaɗɗa yai jajur yana ganin kamar tsohuwa bazata tashi ba , wani irin tari ne ya sarƙeta cikin ƙanƙanin lokacin jikin likita yai sanyi dana baba , hannun tsohuwa dake riƙe da likita yaji ya faɗi ƙasa ,a razane ya ɗago kai ya kalli baba ,baban ma shi yake kallo yace "ta mutu "ta mutu?"baba yace " innalilahi wa inna ilaihir raji'un "baba ya rushe da kuka ,Ramu dake waje ta kurma ihu tana shure shure tace "wayoo tsohuwata na shiga uku "irin kukan da takeyi...

MOM ISLAM

NIDA YARINYA Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin