ZAINAB

32 2 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

02

Zainab irin matan nane masu Kwalliya da San kyale kyale haka tana da iya magana,iya tafiya Kai komai nata Inka kalla ze burgeta musamman ga maza masu San mace wayayyiya,wani lokacin in baka zauna da ita ba,sai kayi tunanin girman kai da iyaye gareta,aa ita haka Allah ya halicceta komai nata tun tana karama haka take,duk da kuwa a karkara ta taso,haka bata da ilimin boko me yawa sai abunda ba'a rasa ba amma ta tsaya tayi karatun addini sosai Dan tana da kishi bata san taga wani ya fita ko cikin Yan Uwa bare abokai,shiyasa ta tsaya tayi karatu sosai Dan tafi kowa acikin kawayenta.

"Kinyi shiru bayan kinsan Ina zaune Ina jiranki ki bani amsa"
Aisha ta Kuma fada tana kallanta.

"Sorry,Ba wani bane sai Alhaji Muhammad Dollars"

Wata muguwar dariya Aisha tasa handa faduwa a kasa tana kallan kawar tata,sai da tayi me isarta,yayin da ita Kuma uwar gayyar taci gaba da danna wayarta tana basarwa kamar Bada ita suke hirar ba.

"Ke dallah bana san iskanci,kode kinyi gamo ne ban sani ba,kawai ki dena kwana kwana kice Auwal,wallahi zanyi miki Dariya ba,Dan nasan itace bakya so da tsokana"
Aisha ta fada tana kokarin daidaita zamanta kan katifa.

Banza Zainab tayi da ita kamar ma bata san abunda take cewa ba.

Dariya ce take San Kuma kwacewa Aishar ma tana kokarin dannewa Dan tasan in bata yi wasa ba ko zata mutu bazata Kara magana ba.

"Kawata Dan ALLAH mubar wasa,Auwal ne ko?"
Ta fada cikin nutsuwa Dan ta samu amsar tata.

Dago da manyan fararan idanun ta tayi Wanda duk girmanka Inka Kalli cikinsu sai kaji kasala ta kama ka,sannan ta lumshe su tana dadin,
"gama dariyar tukunna sai na baki amsa,nasan da saura"

"Ya kuri Zee Zee,Dan ALLAH gaya mun,kefa kikace inzo akwai magana Kuma yanzu zaki mun yanga"
Aisha ta fada sosai cikin nutsuwa da dakewa.

"Aa toh na gaya miki kin maidani mahaukaciya me Kuma kike so nace dake"

Tabbas a zaman da sukai da ZAINAB tasan bata taba mata karya,duk abunda zata fada kanta tsaye zata fada duk muninsa kuwa,wannan shine abunda tafi sani game da ita,in ta tashi magana bata shakka bata karya Kuma bata da tsoro,take gabanta ya fadi Dan tasan mundin bata taba karyar ba toh kuwa yanzu ma gaskiya ta fada,amma in hakan ya kasance ZAINAB ta cika babbar maciya Amana Kuma marar hankali.

"Wai Dan ALLAH kawata da gaske kike"
Ta Kuma kwantar da murya Dan tana san ta samu tabbacin zancan ta.

"Ai kinsan bana miki karya,wajan wata biyar kenan muna soyayya da juna yanzu yace yanasan yayi magana da Yaya shiyasa na kiraki ki bani shawara"

Da sauri Aisha ta mike zaune tana zagaye dakin cike da mamaki Dan ta kasa magana,wannan shi ake kira da karfin hali marawo da sallama, gaskiya ZAINAB bata da hankali,na farko mutumin Nan Baban kawayen tane, sannan mahaifiyar su ta dauke ta tamkar yarda ta haifa,haka zalika mutumin Nan ya haifeta Dan duka shekarunta bazasu wuce 18 ba ko autar gida ta girme ta balle manyan yayan sa,ko da yake komai yana yiyuwa a haka amma butulci da zatayi shine abun dubawa,aikuwa ta dauko ruwan dafa kanta,nannauyar ajjiyar zuciya ta ajje sannan ta kalle ta ,tana zaune inda take tana ci gaba da abunda take a waya tana jiran amsar kawar tata.

"Gaskiya ban goyi bayan wannan rashin hankalin ba,yo rashin hankali mana2,tayaya zakiyi wannan banzan tunanin Zainab"

"Toh dama ni ce miki nayi giyan bayanki nake nema,kawai na kiraki mutattauna kisan wanene Wanda yake San nawa nake sanshi,sannan insane ta hanyar da zanbi in sanar da Yaya"

"Toh meye amfanin zuwana kenan,ai kina da karfin gwiwa akan wannan"
Aisha ta fada ranta a bace tare da daukar hijab dinta da wayarta ta fita daga dakin.

Cike da mamaki kwance kan fuskar Zainab kamar Wanda bata fadi wani abu me girgizawa ba ta bi kofar da kallo,kafin ta tabe baki tana fadin cikin zuciyar ta,
"Kya dawo da kafarki,aikin banza ko ubanki nace zan aura kin Isa ki hana balle uban wasu,na rasa me yake damun mutane wallahi,shi wancan Dan iskan ji yake zan anshi wasu Dan tsiraran kudinsa handa kawo mun check bayan nida nake so nayi rayuwa da ainayin me kudin,da alama akwai baban yaki a gabana tunda har Aisha bata goyi bayana ba babu wanda ze goya,muzuba mu gani"

.............
Tunda safe ko tashi Sajida batayi a bacci ba Hilal ya fita,Dan haka koda ta tashi bata gansa ba ta kira sa ya sanar mata ya huce yana da aiki a gabansa sosai.
Ajjiyar zuciya tayi hannunta rike da wayar tana kallo,ta rasa me yake damunsa,tabbas tana kaunar Hilal kamar rayuwarta saide tasan ko lokacin da sukai aure ba wani Santa yake har can ba tamkar biyayar iyaye ce kawai tasa yake zaune da ita,amma koba komai yana nuna mata soyayyah da kulawa,haka bata taba neman wani abu ta rasa a wajan ta ba,mahaifinta kanin Maman Hilal ne tun bayan rasuwar sa ta dawo hannunta har zuwa sanda ta mata aure da danta, Mama uwace ta gari bata taba nuna mata banbanci tsakaninta da yayanta ba,haka duk wani abu nata itama bata biye mata,Dan da ta kira mahaifiyar ta akan Abu gwara ta kira mama,Dan haka yanzu ma number Mama tayi dailing Dan tana san ta gaya mata kwana biyu duk Hilal baya cikin hankalinsa.

Cikin sanyi murya tayi sallama tana me gaisar da Uwar rukon nata Kuma Surukarta,
"Lafiya qlau Sajida ya kuke?"
Maman ta fada cikin murmushi da jin dadi aduk sanda take tare da ita.

"Lafiya qlau muke mama,Yasu Ikram?"
Ta fada tana me Kara nutsuwa tana Kuma jujjuya abunda zata fada.
"Duk suna lafiya da jiya ma suka ce zasuzo miki sai dai yau dayake Maryam bata jin dadi ko school ma bata leka ba"

"ALLAH sarki, Allah ya bata lafiya a gaya musu Ina Nan Ina jiransu yau din"

"In sha ALLAH zuwa anjima zasu shigo,ta fada cikin jin dadi"

"Mama"
Sajida ta fada tana me tsuntse idanunta Dan tana jin kunyar Maman ainun"

"Naam" ta amsa mata itama tana me Bada hankali akan kiran da tayi mata.

"Ahm dama dama..Mama Yaya ne duk kwana biyun nan kamar akwai abunda yake damunsa,na tambayesa ya nuna babu komai,ni Kuma abun yana damuna shine nace ko zakiji menene damuwar bana san inganshi a haka"ta karasa maganar muryarta na rawa kamar zatayi kuka.

Ajjiyar zuciya Maman ta ajje Dan tasan halin Dan nata,kenan bear maganar ba duk irin lalashinsa da nasiya da tayi,
"Subhnallahi,ko a wajan aikin nasa ya samu matsala,ki kwantar da hankalinki,zan kirasa naji menene yake damunsa,karki saka damuwa cikin ranki kinji yar Albarka"
Maman ta fada tana me kokarin kwantar mata da hankali.

Gyada Kai kawai take tamkar tana kallanta,cikin gamsuwa ta amsa mata da "Toh Mama, nagode ALLAH ya Kara Lafiya"

"Ameen yata ki kula da kanki,akwai abunda kike so a kawo miki?"
Ta fada tana kokarin Kara nuna kulawarta a gareta.

"Aa nagode "
Itama ta bata amsa a sanyaye.

"Toh ki kula da kanki ajjima su Maryam zasu szo su tayaki hira, ALLAH ya miki Albarka"

"Ameen"
Ta bata amsa sukayi sallama.

ZAINAB Where stories live. Discover now