ZAINAB

12 4 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

34


Yauma tare suka ci abinci su uku cikin nishadi,bayan sun gama Sajida ta musu sallama ta tafi.

Tana tafiya Zainab daki ta koma tayi wanka da sallar insha'i ta kwanta Dan ita duk a takure take ganin Hilal a part din nata.

Bayan ya dawo daga masallaci part din Hindu ya nufa,ya shiga da sallama, Babu kowa yau tv ma a kashe take,Kai tsaye dakinta ya nufi,da sallama ya tura kofar ya shiga,tana kwance akan gado da kayan data saka tun da Rana.

Jin motsi shigowa yasa ta gyara kwanciya Dan gaba daya yinin Ranar bacci ta yini tanayi sai bayan magriba ta tashi taci abinci,tana gamawa ta dawo daki ta kwanta bata jima da kwanciyar ba ya shigo,

Karasowa yayi bakin gadon ya zauna tare da taba kafarta,da sauri ta janye Dan bata san masa magana har lokacin fishi take dashi.

"Ko baki da lafiya?"
Ya fada yana Kara janyo kafar tata,

Wannan karan mikewa tayi zaune tana kallansa kafin tace,
"Idan ma mutuwa nayi menene damuwar ka"
Ta fada tana hade rai tana kallansa.

"Ina da damuwa mana,tunda matatace ke kuma a cikin gidana kika mutu,Kinga kuwa dole in shiga damuwa"

Juyawa tayi zata koma ta kwanta batare data tanka masa ba,da sauri ya hawo gadon gaba daya yana mata magana.
"Karki kwanta muna magana"

Tsaki tayi ta jawo pillow ta kwanta tana lumshe ido,saida ya karewa fuskarta kallo sannan yace,
"Kiyi hakuri akan abunda ya faru jiya,raina ne ya bace amma bana fatan hakan ta Kara kasancewa in saka hannu in daki mace musamma matata"

Har lokacin bata bude idanta ba ballanta ta bashi amsa.

"Banasan Rigima,na gaya miki kamar yanda nake auranki haka itama Zainab,Kuma na riga auranta kafin ke,Kinga dole kiyi hakuri ku zauna lafiya tunda itace a gaba dake,bansan tashin hankali ki zauna Babu Rigima Kuma Sai kunfi jin dadin zaman"
Ya fada yana shafa fuskar ta da idanun ta ke rufe.

Mikewa zaune tayi tana fadin,
"Bana san wasan kwaikwayo ka tashi ka barmin daki,ko iyayena Basu taba daga hannu suka mare ni ba,sai Kai Hilal,abun haushin ko wata banyi cikin gidan Nan ba,sannan akan matarka ka mareni,inda ace fadane tsakanin nida Kai da sauki amma sabo da wata ka daga hannu ka mareni,Kuma kazo kana gaya mun wasu stories, wallahi saina rama marina,sai taji ciwon da Nima naji"
Ta fada tana kallansa.

"Amma ai ba ita ta mareki ba,Kuma bata san anyi hakan ba,ni zaki mara nida na mareki"

"Amma akanta ka mareni,sabo da haka akanta zan Rama wallahi kaji na rantse,yauma bana jin dadi shiyasa kaga ban dauki mataki akan hakan ba,amma dasai ka kasa gane gidan Nan wallahi"

"Me yake damunki?"
Ya fada yana kallanta.

"Ban sani ba,inda Ina da mahimmanci ai da safe kake zuwa ka ga ya na kwana,amma jiya sabo da na tabo yar Gold baka shigo ba in ma mutuwa nayi sai de kazo kaga mushe ba"

"Pls Hindu ki dena fadar wannan maganar,yanzu bagashi ba da kaina nazo na baki hakuri,ki rama marina Dana miki toh,tunda ni nayi Marin"

"Kanka Ake ji"
Ta fada tana juya masa baya ta koma ta kwanta.

"Shikenan duk inda na biyo miki kinki saurarensa do your worse"
Yana kaiwa Nan ya mike ya fita daga dakin nata.

Tana jin yaja mata kofar ta mike zaune tana bin bayansa da harara,sauka tayi ta shiga bayi tayi wanka ta gasa jikinta Dan yanzu taji karfi karfi,tazo tayi Sallah ta fita falo da wayarta atana dannawa.

ZAINAB Where stories live. Discover now