ZAINAB

9 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

31



Da sallama suka shiga,kallo Daya Zainab tayi wa gefan da Hilal ke zaune kallo shida Hindu suna zaune gaf da juna kamar zata shige jikinsa.

A tsaye a gefe Zainab ta tsaya yayin da Sajida ta nufi dinning Dan kokarin shirya abincin,daga can Sajida ta furta,
"Zainab ki karaso mu hada mana"

Jiki a sanyaye ta nufi wajan ,ta gefan ido Hilal ya kalleta ya maida kansa ga waya da Hindu take nuna masa,bayan sun gama gyara plate din Zainab ta zauna, Sajida ta karasa wajan Hilal din tana fadin,
"Yayana dinner is ready tana murmushi"

Ahankali ya mike yana kallan Hindu data hade rai ya furta,
"Zanci abinci in Kuma zakici toh"
Yana karasawa ya nufi dinning din ya zauna.

Ita kuwa Hindu zama tayi tana kallan TV Dan gani take in taci abincin Sajida ta fadi Kuma zata raina ta,shiyasa ta zauna danta kuntata mata,sai gashi ko yaushe bata nuna alamun jin haushi ko canji a fuskarta.

Zama sukai bayan kowa ya zuba abunda yake bukata suka fara ci,shiru dining din Babu magana,kowa da tunanin da yake Hilal kawai ke cin abincinsa cikin nutsuwa yayin da tunda ya karaso wajan kamshin Zainab ya hanashi sakat,ya kalleta yafi sau adadi amma komai nata yana burgesa fite da ko wacce mace da ya taba gani,yanayin shigar ta,skin dinta, idanunta, kamshin ta da yanayin jikinta da nutsuwarta,yanayin yanda take cin abincin ma kawai burgesa yake kamar su dauwama ahaka amma yasan hakan ba soyayyah bace yana ta faman yaudarar kansa.

"Yayana dadin girkin namu ya hanaka magana ko sai mun saka Maka waygi"
Sajida ta fada Dan shirun yayi yawa,dama tasan Zainab bazata taba furta koda kalma Daya ba.

"Uhm"
Kawai yace Dan baya San dogon magana.

Jin shiru wajan yasa Hindu mikewa ta nufo su zuwa inda suke zaune.

Hilal shine a kujerar tsakiga sai Sajida a gefansa na hagu ita Kuma Zainab na dama daga ko wani bangare na dining din.

Koda karasowar ta Zainab ta kalla Dan ganin ta sake ta zauna kusa da Hilal din,bayan be dace ba tunda bata da hadi dashi Dan tasan ba kanwarsa bace.

"Ke"

Hindu ta fada tana kallan Zainab,da ko dagowa batayi ba bayan taji Hindu a tsaye a kanta.

"Ke bakya ji"
Ta Kuma fada tana kallan Zainab din.

Sajida ce kawai dake rike da spoon a hannunta tana kallan ikon Allah yayin da Hilal be nuna yasan abunda yake faruwa ba.

Wannan karan hannu tasa ta zungureta tana fadin,
"Ke bakya ji ana miki magana ko ba'a koya miki tarbiya a gida ba"
Ta fada tana jin haushin banza da Zainab tayi mata.

"Dan ALLAH ki samu waje ki zauna sai a zuba miki abincin"
Sajida ta fada tana mikewa.

Ko kallan Sajida batayi ba Dan tana san sanin wata yar iskar ce wannan,shiyasa sai taga karshen iskancin ta yau.

"Baby wacece wannan ana mata magana tana jin mutane ko kurma ce?"
Ta fada tana kallan Hilal.

Ahankali ya dago da manyan idanunsa yana kallanta tare da fadin,
"Ki tambaye ta da kanki mana"

Wannan magana tayi mugun Bata nata rai da yasa ta dakawa zainab tsawa.

"Ke wai baki da hankali ne kizo gidan mutane kina nuna musu Isa da iko idan kin koma gidan ubanki sai kiyi wannan ikon amma  aa gidan Nan ba"

Wannan karan ma Zainab bata motsa ba Kuma bata da alamun yin hakan,wannan dalilin yasa Sajida fadin,
Zainab Dan Allah taso ki dawo kusa Dani,ki bata wajan ta zauna bana san tashin hankali"

ZAINAB Where stories live. Discover now