ZAINAB

10 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

29



A dare guda amma gaba daya Umar ya fita a hayyacinsa,yana San Zainab sosai Kuma tunda yake ita ce mace guda Daya kawai da yake so,yayi nisa cikin kaunarta ya gama tsara yanda zasuyi rayuwa sai gashi an zo ana gaya masa wasu maganganun da Basu da ma'ana, Babban abunda yafi komai Kona masa rai shine Zainab taki daga wayarsa balle yaji ta bakinta,haka ya kwana beyi bacci ba,bayan ya dawoa sallar asbah ya dauko wayarsa karo na Babu adadi ya fara kokarin kiranta.

............
Halin da Umar ya shiga Zainab ta fisar tashin hankali,duk da ta ruga ta tsaida magana da su Aunty amma ta kasa samun nutsuwa,bata san ta Ina zata fara rayuwa da hilla da Kuma matan sa ba,kwana tayi tana sallar tana kaiwa Allah kukanta akan zabi mafi alkawari ya Kuma saukaka mata akan abunda take ji,bayans sallar asbah tahau katifa tana kokarin yin bacci wayarta ta fara vibration, ahankali ta zaro ta daga kasna pillow tana duba me kira,dama tasan shine,zaune ta mike tana gyara hular kanta data zame tare da daga Kiran ta Kara a kunne yau tama kasa koda sallamar da take masa,dama ta gama yanke shawarar da safe zata nemesa suyi magana.

Shima shirun yayi na wani lokaci kafin yace,
"Nagode Zainab, nagode,wannan shine sakayyar soyayya ta a gareki ko?"

Shiru tayi tana jin idanta na cika da kwallah,rufe idon tayi hawayen suka zubo kafin ta bude muryarta na rawa ta furta,
"Kayi hakuri Umar,duk abunda zan fada maka bashi da wani amfani,Ina Maka fatan samun wacce ta fini Kuma Ina Maka addu'a Allah ya Cire Maka soyayya ta daga cikin zuciyarka"
Tana kaiwa Nan ta kashe wayar gaba daya tare da saka kanta cikin pillow tana wani irin kuka Dan gani take shi Umar nasa me sauki ne akan ita.

Shima kamar yanda tayi haka yayi,ajje wayar yayi tare da safe kansa yana furta,
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun"Dan shine kawai abunda ya dace yayi ta fada har zuciya sa ta dawo daidai.

............
Koda Hilal yazo office bega Umar ba,dama beyi tsammanin ganin sa ba, office dinsa ya koma ya zauna yana tunanin menene abunda ya faru har Umar yaji ainayin wacece Zainab a wajanta,haka Shima yayi ta tunani bayan 30mins da zamansa ya Kuma fitowa,har ze huce ya Kuma nufar kofar office din,yana shiga kuwa ya gansa,kana ganin fuskar sa kasan jiya beyi bacci ba.

Ciki ya shigo da sallama Umar ya amsa masa,yana zama a kujera batare Daya kalle sa ba.

Zama Hilal yayi yana facing din shi kafin yace,
"Kayi hakuri Umar, wallahi ban san Zainab kake dating ba,inda nasan itace taya zan rabu dakai ka dinga dating na matar aure,Kuma kasan Zainab a gidansu take ba zuwa nake ba balle insane abunda yake faruwa sai da na ganku wajan dinner ta,Kuma in da Wanda zakayi blaming ba kowa bane sai ita,tunda tasan nide ban sake ta ba,kaga kuwa tana sane take tarayyar da Kai"
Hilal ya fada yana kokarin fahimtar dashi.

Ajjiyar zuciya ya sauke kafin yace,
"Itama bata sani ba, Yayanta yace sune suka biye mata Basu gaya mata baka saketa ba,dataga ta shiga makaranta Kuma ba'a Maka maganarka tayi tunanin ka rabu da ita tunda dama abunda take so kenan, anyway ALLAH ya kaddara hakan,amma komai ya huce bani da abunyi Kuma"
Ya fada yana daga hannunsa alamun komai ya kare.

"Haba abokina karka cire hope mana,ga ayn amta Nan da yawa a gari,in kana so zan saki Zainab ka aureta"

Da sauri ya kallesa yana fadin,
"Haba haba karka fara wannan tunanin mun barwa Allah komai tunda shiya tsara mana Rayuwar mu"
  Shima ya basa amsa yana kwantar da murya.

"Shikenan idan ka huce ka zabi cikin Maryam ko ikraam na baka wallahi"
Ya Kuma gaya masa haka ko zeji dadi.

Murmushi yayi yana fadin,
"Abun har yakai a dinga neman Kai Dani"

ZAINAB Where stories live. Discover now