ZAINAB

12 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

08


Kamar yanda Abba ya saka lokaci haka ya sanar ma da Yaya Abubakar,sannan ya Bada kudi masu yawa Dan a hada ma Zainab lefe da Kuma kudin aure da sadaki duk ya Bada,sannan ya sanar masa in yana bukatar wani abu sai ya gaya masa.

Nan ya sanar masa ba'a kano suke San ayi bikin ba,zasu tafi garin su in biki ya rage sati daya Dan haka dole a Bali za'a daura auran.

Alhaji Muhammad be nuna damuwa ba,Dan dama daga tushenta ya kamata dauko ta Kuma yaji dadin hakan da zama da jimawa da sukai anan besa sun manta asalin su ba.

Koda Yaya Abubakar ya kawo makudan kudin da Alhaji ya Bada Aunty Farida taji dadin komai Kuma ta nemi Daya Bada aje a siyo wa Zainab din kayan lefan,beyi musu ba ya Basu kudi masu yawa domin su fara siyayya,haka ya ware wasu Dan yi mata kayan daki.

Nan da Nan Amarya aka fara shiga kasuwa domin yin siyayya yanda ya kamata,haka ta xage tana daukar kaya masu kyau na kece raini masu tsada,haka bata ji kunyar Farida ba ta xage tana zabar kayan bacci da Kuma kananan kaya da zata tsuke a gidan tsoho(a cewar ta)

Cikin kwanakin Nan haka suka dage da shiga kasuwa har da Aisha wani lokacin suke tafiya,sunyi siyaya me tarin yawa duk satin nan Basu zauna ba har ya rage saura kwana biyu su huce Taraba.

Ganin abun da gaske ne domin Alhaji har yayi wa Zainab order kaya daga waje,Dan dama tun farkon zuwan su garin sun kasance a kar kashinsa,tamkar yayansa haka ya dauke su,rudin zuciya ne da kissa irin ta Zainab yasa yaji ya fara sha'awar ta zamo matarsa,amma da ALLAH yasa Hilal ya shigo cikin abun yafi kowa farin ciki da Kuma jin dadi,Dan haka ya zage iya bakin aljihun sa Dan farantawa Dan nasa,duk da shi ba haka Hilal din yaso ba.

Da kansa yasa aka kira masa Sajida har gida,domin Mama tace ita bazata iya gaya mata ba sai de ya gaya mata da kansa Dan shi ya shirya abun,be saurareta ba ya kira Hilal domin ya kawo masa ita.

Koda ya dauko ta suka zo gida tana ta murna Dan ta kwana biyu bata zo ba,gashi tana so ta Kuma samun update akan maganar Zainab.

Daga Mama sai Abba sai shi Hilal din suka San da maganar auran Hilal din amma ko Yan mata gidan da samarin Basu sani ba.

Da sallama suka shigo falon Abba suka zauna kasan carpet suna gaida shi, Sajida cike da murna take hira da Abban har yakai ga gyara murya tare da fadin.

"Sajida ni nasa Hilal ya kawo ki gida domin Akwai muhimmiyar maganar da nake so muyi dake"

Cikin nutsuwa ta jinjina kanta tare da fadin,
"Toh Abba"

"Ywwah,Kinsan dama ko wani namiji ALLAH ya halarta masa auran mace har 4,sai de in bazaka iya adalci ba sai aka ce kayi Daya domin kaucewa azabar Ubangiji,sabo da haka mijinki ya Shirya wannan adalci yana san ya Kara aure Nan Bada jimawa ba"

Sosai hanjin cikinta suka kada,ba komai yaja hakan ba sai tunanin auran hadi sukai dashi,yanzu Kuma Kila zabin ransa ya Nemo,Nan ta fara jero duk addu'ar data zo bakinta Dan yanda zuciyar ta take bugawa kamar zata fito daga kirjinta,tasan dole watarana Hilal zai Kara aure,amma batayi tunanin Nan kusa ba,ta shirya wa hakan dama shiya ta dage da babuwan da dole zata saka soyayyah da shakuwa tsakanin su kafin wannan Ranar tazo.sai gashi ba'a dau lokaci ba Ranar tazo mata,
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun"take ta maimaitawa a zuciyar ta.
  Jin Abba yana fadin "kina jina"

Da ker ta tattaro dukkan nutsuwarta kanta a kasa ta furta,

"Eh Abba"

"Ywwah,sabo da haka inasan ki rike gaskiya da Amana kamar yanda kike kar ki canza,Kuma duk abunda kikaga ba daidai ba akan mijinki ko ita abokiyar zaman naki ki sanar dani,in Sha ALLAH zan dauki mataki,kuyi hakuri ku zauna lafiya nasan baki da matsala Kuma in Sha ALLAH itama bata da matsala,Ina fatan hakan ya kasance Alkhairi a gare mu baki daya"

ZAINAB Where stories live. Discover now