ZAINAB

12 2 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

19


Kai tsaye Zainab dakinta ta nufa tana mamakin Wannan saurayin
"Wai Umar"
Ta fada tana ajje littafin nata,
"Toh ni Ina ruwana dashi,zezo ya kama yimun yanga Koji yake ni yanzu samari burgeni suke,sai wani feleke yake Allah yasa Aisha yake so danni bata soyayya nake ba ze wahalar da kansa a banza a hofi"
Haka tayi ta faman surutu ita kadai har aka kira sallar magriba,sai bayan ta idara da Sallah tana daki bata fito zuwa dakin Aunty Farida ba,taji muryar Aisha suna magana da Aunty Farida.

Da sallama ta shigo cikin dakin dauke da food flask a hannunta tana fadin,
"Bakin ki tsayawa kici abinci ba,shiyasa nace saina kawo miki duk dare"
Ta fada tana ajje mata a gabanta tare da zama.

"Gashi nan tuwo ne miyar danyar kubewa,nasan favorite din kine"
Ta fada tana bude mata flask din da yake ta turiri da kamshi, sannan ta rufe tana fadin,
"Kin karasa note din naki,nace miki gobe biki zaki rakani duk abunki sai kin rakani nama gayawa Aunty Farida Kuma zata fadawa Yaya ballantana ki kawo mun wani uzuri"

Murmushi Zainab tayi tare da mikewa tana fadin,
"Bari in dauko plate in juye mana tuwon kar ya huce kina zuba"
Ta fita daga dakin,bata jima ba ta dawo da ruwa da zobo da Kuma plate a hannunta,ajjewa tayi tana fadin,
Amma duk abunki ai ba da safe zamu je bikin ba"

"Ai nasan halinki da shegiyar nawa,yanzu shirin ki ma kadai sai zuciya ta ta kusan bugawa wallahi"

Dariya tayi marar sauti ta zauna tana saka hannu ta fara cin abincin tare da fadin,
"Dazu Ina fitowa daga gidan ku naga Wannan na jiyan Daya kawo mu gida ana ruwa"

Aisha da San gulma ta zaro ido tana ajje zobon hannunta tare da fadin,
"Karya"

Kallanta tayi tare da fadin,
"Muka gaisa wai yazo duba mu yaga ya muke,nace masa Lafiyar mu qlau,har tambayarki yayi,wai sunan sa Umar kiji iyayi"

Ido Aisha ta zaro tana fadin,
"Bana gaya miki ba kika ki yarda,dama nace wallahi naga yanda yake star kallanki,nasan dama za'a rina,ashe kinyi saban kamu, gaskiya kina da farin jini ki godewa Allah"

Zainab de bata ce mata komai ba taci gaba da cin abincin ta.

"Gaskiya gayan ya hadu Zainab,gashi Dan boko Dan gayu,kina ganin yanda yake maganar sa kinsan Dan gayu ne"
Aisha ta fada tana kallan Zainab din.

"Yanzu zakici Abinci ko kuwa"

"Keni na koshi ma,wannan labarin yasa yinwar ta tafi Yasin,ya baki number sa?"

"Inyi me da ita"
Zainab ta fada tana hade rai.

"Ban gane ba,me Ake da number mutum,wallahi dakin amsa gobe ki kira mana shi ya kaimu bikin"

Dama tasan Aisha zata fadi abunda yafi hakan ma,shiyasa bata Kara ce mat auggan ba har taci abincin ta koshi ta bar mata nata ta fita Dan wanke hannunta tana faman zuba.

..............
Yau Monday company sai hada hada Ake ,kowa yana abunda yake gabansa, Umar ne ya shigo cikin company yana ta gaisawa da mutane har ya isa bangaran su,har ze shiga office dinsa ya tsaya tare da tambayar secretary din Hilal ko ya shigo,jin be karaso ba yasa ya huce nasa office din.

Be jima da zama ba Hilal din ya shigo,gaisawa sukai Sannan yace masa
"yau akwai meeting da bakin da zasu zo,da fatan an gama shirya komai kasan na manta sai da na shigo na tuna"

"Ai dole ka dinga mantawa da abubuwa kana kera villa,aiki ya Mika"

"Wallahi kaide bari,ai Abba ya baro mun aiki,Dan ba yanzu nayi niyar hada gidan Nan ba,amma ga bikin nan ga Kuma aikin gida cikin Dan lokaci"
Ya fada yana fita tare da fadin,
"Ina jiranka"
Sannan ya rufo masa kofar.

ZAINAB Where stories live. Discover now