ZAINAB

10 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

28



Lallashinta Farida ta fara tana fadin,"kiyi shiru to menene na kuka"

Cikin kuka me tsanani ta Kalli Farida tana fadin,
"Aunty taya ze fadi haka,nace bana sanshi kinaji yanzu yana fadin dole saina koma gidan sa,wallahi ni na yanda ya aura mun koma wanene amma Banda Hilal"

"Toh shi Hilal din uban me yayi miki ko ya tsare miki"
Ya fada cikin bacin rai yana kallanta.

"Yaya baya sona fa Shima,Kuma wallahi mugu ne baka ga muguntar Daya yimun ba,taya zan koma gidansa ya kasheni Kuma wallahi har shaye shaye yana yi"

Banza yayi da ita yama tashi ya fita daga cikin dakin.

Farida ce ta ci gaba da kwantar mata da hankali tana fadin,
"Toh duk kukan Nan da kike kin san baze hana shi ya canza ra'ayinki ba,ki nutsu ki kwantar da hankalinki sai ayi magana a nutse amma jingo kinata famn kuka ba gyara Babu dalili"

Duk fuskar ta bace da ruwan hawaye idanunta sun kumbura Dan kukan da tayi yanzu,
"Aunty to ki masa magana, wallahi ni da in zauna da Hilal gwara in koma Bali ko Dan canne in aura da zama gidan Hilal"

Cikin lallashi da kwantar da murya Farida ta fara fadin,
"Haba Zainab kar ki bani kunya,kin san wanene yayanki Kuma kin san irin San da yake miki tamkar daga cikinsa kika fito,Shima ba ze so abunda ze cutar dake ba,yanzu sabo da ya aura miki mutumin da yake ganin ya cancanta har kike fadin zaki koma Bali,da da kina cin dadi baki ce zaki koma can ba sai yanzu da yake kokarin Gina miki rayuwa zaki guje amsa,toh na tabbata ko wajan su Baffa kika koma wallahi bazasu goyi bayan kiba,gwara shi koma menene yasan halin da kike ciki,Kuma duk kan mu munsan Hilal yayi kuskure amma yazo ya Bada hakuri Kuma yayi alkawarin hakan baze Kara faruwa ba,haka mahaifin sa ya Bada hakuri ba iyaka,sabo da kina San karatu kin matsa Alhajin da kansa yace a barki na Dan wani lokaci amma dama can Hilal be sake ki ba,mune muka boye miki Dan ki nustu kiyi karatu,Kuma da kaina ko sati ba'ai ba na yima yayanki magana akan ya fada miki gaskiya sabo da zuciya bata da kashi zaki iya zuwa kiyi soyayyah da wani bamu sani ba,tunda kema ba sanin halin da Ake ciki ba kikai,gashi kuwa har kuna shirin yin aure,ki tuna wanene Alhaji Muhammad a rayuwar mu gaba daya,sannan ki tuna wa nenen Yayanki a Rayuwar ki kar San zuciya yasa kiyi butulci koda bakya san shi sabo da halacci da Kuma biyayya da kikayi sai Allah yasa hakan ya fiye miki Alkhairi,wallahi nayi miki alkawari idan har kika koma bakiji dadi ba,ki kira ni da kaina zanzo na maido ki gida Kuma har abada bazaki Kara komawa ba,kuyi mun wannan akfarma ki koma badan niba kiyi hakuri wata Rana sai labari"
Farida ta fada tana lallabata.

Sosai zuciyar ta tayi sanyi Kuma ta samu nutsuwa akan da,amma tana ganin har abada bazata taba San Hilal ba,Kuma gaba daya rayuwarta shikenan ta lallace Babu uta Babu farin ciki,tayi matukar nadama da tun farko taso mahaifin sa tasan da Babu abunda zesa ya aureta sosai kuka me cin rai ya Kuma kwace mata,saida tayi me isar ta Farida bata hana ta ba sannan ta dago tace,
"Amma Aunty kina gani Shima ba sona yake ba,aure ma ya Kara ko wata biyar banyi da auransa ba"

"Na sani Zainab,matar mutun kabarinsa,ko mata nawa Allah ya kaddara ze aura ko kika gidan ko bakya Nan ko kina mace ko kina Raye sai fa ya aura,Ina ruwanki dasu tunda ba aknki suke ba,iya kaci kiyi abunda ya kaiki ibada"

Farida taci gaba da fahimtar da ita tare da mata nasiha me ratsa jiki har ta sauko Kuma ta yanda zatayi biyayya.
Sosai Farida taji dadi tayi ta mata addu'a tana Kara Karfafa mata guiwa kafin tace,
"Aunty yanzu taya zan iya yiwa Umar wannan maganar, gaskiya Ina jin nauyinsa sosai Kuma gashi abokin Hilal ne"

"Abokin Hilal?"
Farida ta fada tana kallansa Zainab da mamaki.

"Eh"
Ta bata amsa.

"Shikenan ki gaya masa yayanki yana nemansa in yaso sai yayi masa bayani a bashi hakuri Kuma"

ZAINAB Where stories live. Discover now