ZAINAB

12 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

*ZAINAB*

_not edited_

18

Lokacin da suka iso yayi mamakin ganin layin gidan su Hilal suke amma be taba ganin koda giftawar Daya daga cikin su ba,bayan yana yawan zuwa gidan nasu,gaba da gidan su Hilal kadan suka ce zasu zasu sauka.

Lokacin da suka karaso gida ruwan ya takaita kadan kadan yake zubowa,godiya suka masa suka nufi gida, Zainab ta fara tura gate din su ta shiga sai Aisha,saida yaga shigar ko wacce gida sannan ya ja motar sa yabar layin.

.............
Kamar yanda Abba yayi alkawari anje an gidan su Hindu anyi amagan da iyayanta,sun Kai kudin aure sannan sun tsaida lokacin biki wata biyar,Dan ya samu ya Ida gidansa a nutse.

Murna wajan Hindu ba'a magana,domin yanda ta jima tana da burin aure musamman da abun kaunarta,yau kuwa ALLAH ya cika mata burinta Dan haka sai abunda aka gani.
Hi du bata da tarkacan kawayen kawarta Daya Amira,itama yar gidan masu hannu da shuni ce amma tafi Hindu wayewa,sabo da ita bata da kamun Kai,mace ce me nuna Isa ki da Kai da Kuma karyar kudi duk da suna dashi,haka tana da Tara samari yara da kanana,sannan bata da kunya ko kadan tana da kyau iya kyau shiyasa take abunda taga dama,ita kadai ce wajan mahaifiyar ta domin tun tana karama iyayanta suka rabu da juna,Dan haka hannun uwar ta ta taso,Kuma gogahgiyar yar kasuwace Kuma yar siyasa kullum gidanta cike yake da mutane mata da maza da ban da ban,shiyasa tarbiyar Amira tayi karancin,gashi duk sanda ta kella ido ta ganki da saurayi hadadde sai tayi yanda tayi ta Rabaki dashi ko ta halin Yaya ne,Kuma mahaifiyata tana daure mata Hindi akan duk abunda taga damar yau,amma duk da wannan Hali nata ,tata tazo Daya da Hindu,duk cikin tarkacan kawayenta Hindu ce kawaii Amira bata yiwa snatching din saurayi,haka bata mata iskan da take yiwa sauran kawayenta Dan tasan kar tasan kar ce Kuma hindu ta fita kyau ilimi Uwa Uba gayu,tun da can Hindu tasan Amira bata kaunar Hilal domin baya sakar mata fuska aduk isancinta tana shakkarsa shiyasa bata kaunar tarayyar su da Hindu,koda suka dawo suka Jone bata taba bata labarin suna tare ba Dan tasan zata iya zugata ko ta bata muguwar shawara akansa shiyasa saida ta tabbatar maganar auransa ta dedeta yau ta shirya da yamma Dan ta ziyarci kawar tata domin su tsara dukkan wani abu daze gudana da bikin nata.

Gidan su Amira a unguwar sharada yake,saida ta shiga mota har ta fito daga gida ta tuna ashe bata kira Amira ta gaya mata zuwanta ba,Kuma ta tabbata zata iya zuwa bata gida,dauko wayarta tayi ta kirata tana driving kafin ta fita daga layin gidan nasu,tana kira ta Kara a kunne tana jira me wayar ta daga,daga can bangaran aka furta.
"Babe ykk"

"Lafiya qlau,kina gida ne?"

"Eh,Ina gida ko inzo,yanzu nake tunanin fita saiga kiranki"

"Aa ganinan a hanya zanzo wajanki akwai news"
Hindu ta fada tana dariyar jin dadi.

Itama Amirar Dariya tayi tana fadin,
"Sai kin karaso"

Hanging tayi taja motar ta fita daga layin zuwa gidan su Amira.

Lokacin data Isa kofar gidan cike yake da motoci tasan cikin gidan ma haka yake,duk da tasan harabar gidan nasu zata dauki mota biyar zuwa shiga,amma kullum kazo gidan baya rabuwa da mutane kamar gidan government,gefe ta samu gaban wani gida tayi parking ta fito cikin riga da wando ta saka kimona a sama da dankwali a kanta Babu vail sai jakar dake hannunta da keys dinta ta nufi gate din gidan tana takunta cikin kasaita.

Me gadin gidan ya riga daya Santa,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa ta shiga,tayi tafiya kadan ta huce duk motocin cikin harabar ta shiga Babban falon gidan da yake cike da manyan mata da Kuma maza,gaida su tayi a tsattsaye wasu na binta da kallo wasu na abunda ke gabansu,ta shige wani falon karami kafin ta nufi wajan dakin Amira da yake karshen falon.

Ahankali ta tura dakin,kwance take kan gado tana danna wayarta,da riga me siririn hannu a jikinta iya cinya.

Tana ganinta ta tashi zaune tana fadin,
"Welcome Babyna"
. Dariya Hindu tayi ta zauna kan gadon tana daka mata duka a cinya tare da fadin,
"Kina jin dadinki,Kinga yanda kukayi wata uwar kiba"
Hindu ta fada tana zere kimo din jikinta.

ZAINAB Where stories live. Discover now