ZAINAB

9 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

11

Zuwa wanna lokacin Zainab ta gama jigata da yinwa,gashi exotic din data Sha ya sakar mata ciki gudawar ta uku,wannan karan data dawo gama da ker ta fito daga toilet din tana dafa bango, Ahankali ta karasa kan kujera tare da shafa cikin nata da yake faman kuka ga faman Murda mata da yake ta tabbata Nan da lokaci kadan bazata iya Kai kanta ban dakinta,runtse idanunta tayi tare da fadin,
"Ya ALLAH ka kawo mun dauki"

Bayan fitar Hilal office, Sajida na zaune ta rasa abunda yake mata dadi,kamar an tsikare ta ta mike ta shiga kitchen ta hada tea me kauri ta debo soyayan dankalin da Kuma bread din ta nufi part din Zainab din tana waiwaye.

Koda ta karasa duk a ride take,ta fara knocking, Zainab na kwance rai a hannun Allah taji anan knocking da sauri sauri,da ker ta furta,
"Waye"

"Nice Zainab zoki bude ki amshi abinci,nasan kina jin yinwa"

Kamar tayi kuka ta karaso bakin kofar tana fadin,
"Ya kulle kofar ban san ta ya zan bude ba"
Ta bata amsa.

Da sauri ta zagaya bakin window tace,
"Zo tanan ki amsa"

Da sauri ta yace labulan ta bude glass din tare da Mika mata cup din tea din,ta amsa ta zuro mata plate da Kuma bread din,
"Gashi nan anjima zanzo na amsa Dan ALLAH karki fada masa na zo wanjanki"

Kamar ta fita ta window ta rungume Sajida take ji tsabar farin ciki,tabbas Allah yana kaunarta da aka kawo su gida Daya da Sajida badan ita ba tasan bazata Kai safiyar gobe ba,wannain tsinanna mijin nata Daya kulle kofar tasan kasheta yake shirin yi.

Godiya ta mata,yayin da ita Kuma tayi sauri tabar wajan Dan ganin take kamar zai shigo ya ganta.

Da sauri ta zauna anan wajan ta fara kurbar shayin da zafi zafi yana gasa mata ciki da bakinta,sai da ta shanye TAs Sannan ta kwanta akan tiles din gumi yana yanko mata, zuciyar ta na bugawa da mugun karfi.

Sai da ta kusan mintuna 30 tana sauke numfashi sannan ta dawo daidai, ahankali ta mike ta ci dankalin kadan ta dauko ta maida kitchen sai lokacin taji ta dawo hayyacinta,wanka ta kumayi ta koma daki ta gyara jikinta,kallan inda wayarta tayi taga yanda ta tarwatse tasan bazata tashi ba Kuma.

Tana daki Sajida ta dawo Dan amsar plate da cup dinta kar Hilal ya gansu.

Nan ta fara knocking tana kiranta kasa kasa,

Da sauri ta mike ta karasa kitchen ta juya a wani wajan ta wanke ta Mika mata tana Kara Mika mata kafin tace,

"Dan ALLAH Sajida ko zaki ara mun Aran wayar ki"
Shiru Sajida tayi kafin tace bari na dauko miki.

Tana Nan tsaye shiru shiru Babu Sajida Babu alamunta,da taga shirin yayi yawa tayi tunanin ko wannan masifaffan mijin nata ya dawo kawai ta hakura tunda Allah yayi ta samu taci wani abu.

Abu kamar wasa sai da tayi kwana goma cif tana kulle cikin daki,Babu me zuwa wajanta sai Sajida dake Kai mata Abinci a boye amma har lokacin batasan batasan a karkashin wa take ba.

Da dare tana daki a kwance tana faman tunani,sai ganin mutum tayi a tsakiyar kanta da uari ta mike tana kallansa cikin mamakin abunda ya shigo dashi har cikin dakinta.

"Ke bakyaji ana miki sallama bazaki amsa ba Dan baki da ilimi baki San me kike ba"
Ya fada yana wani hade rai.

Itama hade rai tayi tana kallan gefe batare data basa amsa ba,

Matsowa yayi zai kamata yajata zuwa falo kamar yanda ya saba ,da sauri taja da baya tana boye hannunta a baya.

Da karfi ya sabeta zuwa falon ya wurgata kan kujera,

ZAINAB Where stories live. Discover now