ZAINAB

16 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

15


...........
Hilal ya dawo nunawa Sajida soyayyah kamar yanda suke tun farko ta dena tunanin Zainab Dan a tunaninta sun rabu da Zainab Dan taga har tsawan wannan lokacin bata dawo ba, hankalin ta ya kwanta sosai.

Tun da safe da suka tashi yace ta shirya ze sauke ta gida wajan su Mama Dan ya faranta mata,Dan yasan Babu abunda take so kamar zuwa gida.

Bayan sun gama duk abunda suke suka nufi gidan cikin so da kaunar juna,da suka karasa gidan be shiga ba ita kadai ya sauke ta shiga da yamma inya taso zai zo ya dauke ta.

A falo ta iske Maryam kawai da muran ta tareta suka zauna tana tambayar Mama,nana take sanar mata sun fita da Ikram tunda safe zuwa asibiti bata jin dadi.

Suna Zainab suna hira Maryam ta saki hirar Zainab.

"Wallahi Yaya Sajida har aka gama case din auran Zainab da Yaya Hilal bamu sani ba,abun ya bamu mamaki,dama Yaya fa ya tsani Zainab ko ganin mu da ita yayi wlh baya amsa gaisuwata,amma kawai naje ance Yaya ya auri Zainab"

"Wallahi kuwa Maryam Nima nayi mamaki kam matuka,musamman da naji ance Abba zata aura,shiyasa ni abun ya daure mun Kai,gashi tun bayan da aka kawo Zainab dukkan ku kuka dauke kafa a gida"

"Tafdijan wanene ze je gidan Yaya ya karya sa,ai duk gulma irin ta ikram hakura tayi da tambayar Mama,karshe itace har gidan su Aisha,amma itama Aishar tace bata je gidan ba"

"Uhmm kede Allah ya kyauta ai abun yayan ku yana bani mamaki wallahi,gashi tun bayan da akai wannan maganar bayan ta dawo gida har yanzu bata koma ba,aure duka duka befi wata Daya ba amma babu zaman lafiya,wallahi dama naji dadin zuwan Nan da nayi Dan Ina san zuwa in duba Zainab,ni har ga ALLAH Ina jin tausayinta"

"Wallahi Zainab bata da matsala,ni nasan halinta,kinsan ko wani mutum da abunda yake so dama ai,amma wlh tana da kyawun Hali ga hakuri,Kuma nasan itama bata san Yaya Hilal da naji wannan abun Daya faru ko kadan banji dadi ba"

"Kinsan bari na dauko hijab dina mu shiga gidan nasu,Dan in Mama ta dawo cewa zatayi sai kin tambayi Yaya ki fita.

Nan da Nan ta dauko hijab dinta suka nufi Gidan su Zainab din.

Da sallama suka shiga, Aunty Farida amsa sallamar tana fitowa daga daki, cikin fara'a ta amsa musu tare da musu iso cikin daki,bayan sun shiga ciki suka kara gaisawa Sanna ta sanar musu da Zainab din tana cikin dakin ta.

Da sallama suka shiga cikin dakin nata,tana zaune kwance ta mike zaune ta gyara daurin Dan kwali ta da ya zame sabo da kwanciyar da tayi.

Cike da fara'a Sajida da Zainab suka zauna suna mata tsiya da yar gayu har lokacin bata tashi ba.

"Wlh Ina kwance Nan bacci ya dauke ni ban maji shigowar ku ba,sannunku"

."ywwah,ya gida ya kike,shiru shiru shiyasa nazo biko"

Murmushi kawai Zainab tayi.

Maryam ta kalle ta tana fadin,
"Ya Sajida tunda kinzo yanzu ai saiki dauke ta ku tattara ku tafi"

Mikewa Zainab tayi tana fadin,
"Bari na kawo muku ruwa"
Dan bata san maganar da suke mata.

Bata jima ba ta dawo dauke da zobo da ruwan sanyi ta ajje a gaban su cikin tray,bayan ta koma ta zauna.

Sajida ta kalleta tana fadin,
"Zuwa nayi in Kara baki hakuri a madadin mijin mu,kiyi hakuri ki yafe masa dukkan abunda yayi miki,sannan na Kuma duba jikin ki,kinsan ko wani mutum da irin kaddarar sa amma Inka amsheta hannu bibbiyu sai ALLAH ya kawo maka sauki.

ZAINAB Where stories live. Discover now