ZAINAB

10 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

07

Cike da farin ciki ta shiga dakinta tana me godiya da Allah Daya sa Yayan ta ya Amince,dama shine tasan tana shakka Wanda ze bata matsala amma yanzu hankalinta ya kwanta,yanzu ne wasan ze fara.

..............
Gaba daya Ranar hajiya Bilki bata samu tayi baccin kirki ba sabo da tunanin maganganun da sukai da me gidan nata,ko lokacin Daya sanar mata yana san auran Zainab hankalinta be tashi ba kamar yanzu, Baban abunda yafi daga mata hankalin shine,shin da gaske Hilal din yana san Zainab kamar yanda mahaifin nasa ya fada ko kuwa akwai wata a kasa,
  Haka ta kwana tana tunane tunane har garin ALLAH ya waye,tun da safe ta Kuma Kiran layin sa ta Kuma sanar masa da tana san ganin sa kafin ya huce office,be mata musu ba ya amsa mata.

Mislain 7:30am na safiyar Ranar ya shigo cikin falon nata,Dan motar sama a waje ya barta.

Zaune ya tanda Maman nasa kasan carpet tana karyawa ita kadai a falon,zama yayi kusa da ita yana gaida ta.
  A yanayin yanda ta amsa masa yasan akwai damuwa,amma beyi tunanin akan Zainab bane kum.

Sai da ta gama cin abincin ta,ta kallesa cikin kulawa yanda yaga fuskarta Babu annuri yasan seriously magana ne.

"Menene hadinka da Zainab?"
Ta fada tana kallansa.

Ko kadan beyi tunanin wannan tambayar daga gareta ba,hakan yasa ya rasa abunda ze fada sai da ta Kuma maimaita masa cikin tsawa.

Tabbas inya fadi dalilinsa na cewar ze aure ta ne Dan baya San Abban da ya aureta Mama bazata taba amincewa da wannan haukan nasa ne hakan ne yasa ya tattaro nutsuwa ya furta,
"Mama Ina sonta,Kuma Ina son auranta,jin Abba ze aure ta yasa han..."

Be Kara da ba ta daka masa tsawa tare da fadin
"Karya kake yi Hilal,Nina haife ka Kuma nafi kowa sannan halinka,yaushe kuke soyayya da Zainab din harda zaka fadi wannan maganar in yarda"
Ta fada cikin macin rai.

"Mama inasanta ,amma ko ita ban taba gayawa Ina Santa ba,sai yanzu da naga Ina kokarin rasata na fada,Dan ALLAH kar kice A'a tunda Kinga shi Abba da kansa ya Amince"
Ya karasa maganar tana marairaicewa da Kuma nuna tsantsar gaskiya a fuska Dan ta yarda.

Shiru tayi tama rasa amsar da zata bashi Dan daga shi har uban nasa ta gaji da wannan rashin hankalin nasu.

Numfasawa tayi tare da Kara maida hankalinta garesa,
"Kana santa,ubanka yana santa ko?"
Ta karasa tana harararsa.

Shiru yayi Dan bashi da amsar daze bata,Shima inda zata duba zuciyar sa da sai ta dena masa magana akan wannan banzar yarinyar,dama ta mutu kowa ya huta,ya fada cikin ransa.

"Ina Maka magana ka mun shiru,toh dole Kai ka hakura ka barwa uban naka ya aure ta Dan bazan iya da wannan rashin hankalin naka ba wallahi Hilal,in bama iskanci ba yaushe zaka fadi wannan maganar Dan ka raina ni"

"Dan ALLAH Mama kiyi hakuri,wlh insane auranta karki hanani,dama ita nake so kika ce saina auri Sajida na hakura na aureta Dan bana san na mata miki"
Ya Kuma fada.

Sosai taji Babu dadi domin tasan baya San Sajida,dole ta masa ,amma tana ganin kamar bazata iya hakura ta barshi ya auri Zainab ba,tasan danta be iya San abu ba haka be iya kiyaya ba,tana kaunar Sajida kamar yanda take kaunar su ikram,bazata so a musguna mata ba,gwara in Alhaji ya auri Zainab Babu abunda ya shafeka da ita,amma Sajida bazata iya dauka ba,dadin da dawa Zainab tafi Sajida wayo tabbas zata iya juya Hilal yanda take so tunda har ta iya daukar hankalin ubansa bare shi,
numfashi me zafi ta fisar tare da yin kasa da muryarta sigar lallashinsa ta furta,
"Nasani amma ka daure zuciyarka ka rabu da wannan yarinyar ka Nemo ko wata yarinya kake so,ni Kuma nayi Maka alkawarin ko wacece zan shige Maka gaba ka same ta,Kai ni ko mata biyu kake so zan yanda ka aura amma ka hakura da Zainab"

Shiru yayi yana nazari kafin yace,
"Shikenan Mama zanyi shawara, ALLAH yasa hakane yafi Alkhairi"

"Ameen"
Ta fada tana me jin babu dadi,amma tasan hakan shine ya dace.

Sallama yayi mata ya tashi ya nufi office dinsa,haka ta mike tana binsa da addu'a harya fita daga falon.

Komawa tayi ta zauna Saman kujera tana sauke ajjiyar zuciya domin gani take ta shawo kan matsalar.

............
Tunda ya shiga motar yake sauke ajjiyar zuciya yana shafa fuskarsa,haka kawai yana zaman Zaman sa ya zubar da mutuncisa ya Kuma mata ransa a banza akan wata yarinya, wallahi Babu abunda ze hana sa auranta domin duk wani digin haushi da yaji cikin zuciyarsa sai ta biya shi,tamkar bashi ta dauko Kuma ko ragi baze mata ba sai de ma ta biya da ruwa,wani murmushi yayi na gefan baki yana fadin,
"Zaki shigo hannu Yan mata.

.............
Daga yaran gidan har ita Sajida Babu Wanda yasan abunda ke faruwa,haka itama Uwar gayyar bata san dawa take shirin agwancewa ba.
  Yayanta ya sanar mata sai ansa lokacin daurin aure zasu tafi Bali,a Daura acan su tawo da ita zuwa gidan ta,Dan ahaka dama ita bata shirya wani taron biki ba irin na zamani da Ake duk bashi bane a gaban ta.

Dan ahaka ta sanar da Aisha duk abunda yake faruwa,ko kadan batayi murna ba hasalima kawai tausayin Zainab din take,Dan gani take kamar zata lalata kuruciyar tane,kullum cikin bacin rai zata kasance,Dan bata ga wani abun farin ciki a irin wannan auran ba.

Kwana biyar da wannan magana Alhaji ya tuntubi Hilal akan maganar Lokacin da yake so asaka,tunda yace baya son a dau tsayin lokaci,
Ya sanar masa shi ya fasa ze nemi wata,be tsaya sauraransa acikin waya ba yace ya same sa a gida.

Lokacin Daya shigo dakin Abban nasa suna tare da Hajiya Bilki,ganin Hilal ya shigo bayan ya gaida su ta mike da niyar barin dakin,Kai tsaye Alhaji ya dakatar da ita,badan taso ba ta nemi waje ta zauna tana kallan Hilal din da kansa ke kasa.

"Me ka fada mun dazu,Kara maimaitawa"
Ya fada yana kallansa.

Shiru yayi Dan beso Abban ya tsada Maman ba.

"Ko baka jina"
Ya Dan fada a zafafe.

"Abba kawai Ina ganin Abar maganar Zainab din,zan Nemo wata"

"Menene dalilin ka?"
Ta tambaye sa.

"Naga kamar yanzu bata sona ne Kamar..."

"Dallah rufe mun baki,ni zaka yiwa wasa da hankali ka mayar karamun mutun,oh baki isa ba wallahi,idan ma Akwai Wanda yake zugaka nafi karfin ku duka,bansan da magana ba kazo kace kana so,naje na tambaya Maka,yanzu Kuma kace ka fasa,idan na aura Maka ita ranar da aka kaita ka sake ta idan ka cika Dan halak,tashi ka bani waje,Kuma na saka sati biyu Ranar juma'a za'a daura auran ya rage naka kaje ka same ta"

Ahankali ya Mike yana me jin dadin abunda Abban ya fada a gaban Mama da tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta,ya musu saida safe ya fita.

Yana fita ta juya ga Alhaji ranta a mace tana fadin,
"Haba Alhaji Wannan wani irin Abu ne,yace baya so ya fasa mu fa muka masa alkawarin zamu aura masa duk Wanda yake so"

"Da Kara da Allah Bilki,inda be shirya ba,baze zo ya same ni inje in yiwa mutane magana ba,yana da lafiya yana da kudi,bayan na aura masa Zainab ko mata biyu ze Kara su cike hudu bani da damuwa,amma wannan sakarcin Bada ni ba"
Shima ya Bata amsa yana kallanta.

Shiru tayi Dan jayayya da mijinta ba dabi arta bace,zata saka musu ido daga shi har Dan nasa raga gudun ruwan su,amma babu ita babu wannan auran wallahi ko tsinke bazata saka ba,suje suyi yanda suke so.



*Zeenaseer*😘

ZAINAB Where stories live. Discover now