ZAINAB

8 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

23



Da sallama suka shiga gidan,Babu kowa da alama Farida ta fita,amma dakin zainab a bude yake,Kai tsaye Nan suka nufa suna daga labulan,tana kwance tana karatu,ta mike zaune tana musu barka da zuwa tare da mamakin ganin Maryam din.

Zama sukai suna mata tsiya da sarkin karatu,Dan ko kafin suyi sauka Zainab duk ta fisu maida hankali a islamiya,Dan haka dukkan su sun Santa da San karatu.

"Wallahi bacci bacci ma nake ji yanzu nake shirin maida littattafan in kullo gidan in kwanta, Aunty ta gida unguwa"

"Ya gida ya kwana biyu,duk ku biyun Kun guje mu"
Maryam ta fada tana nuna su.

"Haba de meze sa mu guje ku Maryam Kuma dena fadin,haka,kawai sch.ke boye mu"
Zainab ta fada tana kallan Maryam din.

"Nide ban anshi wannan uzurin naku ba,Dan ba haka na sanku ba,yanzu ne de kuka canza"
Itama ta maida mata,tana me gyara zaman ta.

"Iv ta fito dashi guda biyu yasha ado da Kuma gate pass hudu ta Mika musu tana fadin,gayyata na kawo muku kinsan ni bani da wasu frnds da suka huce ku,biki gare mu ga IV ga Kuma gate pass na kamu da dinner"

Ansa Aisha tayi, Zainab na fadin,
"Bikin wa za'ai a gida haka zamu Sha shagali"
Ta fada tana murmushi tare da ansar IV din Daya a hannun Aisha.

Kafin ta gama bude wa Maryam tace,
"Mutuminki ze Kara aure Yaya Hilal"

Da suari ta Kalli Maryam tare da fadin,
"Aure Kuma?"

Su duka kallanta sukai Dan basuyi tunanin zataji mamaki ba,sai Kuma ta basar tare da fadin,
"ALLAH ya Sanya Alkhairi ya nuna mana lokacin"

"Ameen" duk su biyun suka amsa suka ci gaba da hira Maryam na basu labarin matar da ze aura da irin hidimar data musu da ya kaisu gidan su.

Sosai jikin Zainab yayi sanyi,itama bata san dalili ba,tasan ita de ba San Hilal take ba amma ya akai maganar auransa ta tsaya mata arai,toh kode Umar abokin Hilal ne,amma Kuma bata taba ganin su tare ba,haka tayita Saka da warwara a cikin zuciyar ta,har maryam tayi musu sallama ta tafi.
Tana tafiya Aisha ta dawo da gudu tana fadin,
"Ke wannan Hilal din mugun Dan iska ne,wai aure ze Kara duka duka yaushe kukayi aure kuka rabu har ze Kara aure"
Kallanta Zainab tayi kafin tace,
"Aure fa zeyi menene abun iskanci yana da bukatar hakan,menene namu a ciki,ni Babu inda zani ma"

"Amma me yasa tun agaban Maryam baki fadi haka ba sai yanzu,Kuma menene naki a ciki ai ba wajan sa zaki ba"
Aisha ta fada tana zama kusa da ita.

"Koma menene ai bikin sane,ke baki San yanda na tsani mutumin Nan ba ko,toh wallahi inaga tsanar Dana masa ko rabinta baya mun,banasan ayita cecekuce shiyasa ban gaya mata bazani ba,amma ba inda zani sai ke kije"

Ta fada tana juyawa ta kwanta ranta babu dadin ta rasa dalili.

Kallanta Aisha tayi tare da fadin,

"Bari na ajje mana,koda zaki canza shawara bari naje gida Ina da aiki,bari na ja miki gidan inna fita"

Ko kallanta batayi ba balle ta bata amsa harta fita,sosai jikin Aisha yayi sanyi Dan batayi tunanin Zainab zataji wani abu game da auran Nan,tasan dama ba lallai taje ba amma batayi tunanin zataji haushin auran ba.

.............
Yaune Ranar farko na bikin Wanda Yan mata da samari zayi event na farko wato cocktail,gidan su Amarya cike yake da Yan Uwa da abokan arziki tuni Zahra ta iso daga London Dan guda de ya cika yayin da Amarya da friends dinta aka ware musu waje guda suke zaune da masu yi musu hidima,yau zasuyi event na farko Dan haka Yan amtan duk sun tafi wajan kwalliya tun da huri.

ZAINAB Where stories live. Discover now