ZAINAB

8 2 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

21


Yau saura sati biyu bikin Hilal da Amaryar sa Hindu,shiru take bana wasa ba shi kuwa gogan Babu abunda yake shirya wa iyakaci da tayi magana ya tura mata abunda suke so,jiya aka Kai lefe ba gani na fada gidan su Hindu duk karyar su saida suka yaba kayan nan, Sannan anje anyi mata gere a gidanta na akfarma duk da itama part din Sajida yayi kyau sosai Dan komai saida ya canza mata,itama ya Bata kudi tayi siyayyar kayan da take so na fadar kishiya da kanta.

Yau tunda safe,Hindu tana daki dame gyara jikin da aka dauko mata Wanda zata gyarata na tsawan sati biyun nan ta koya mata abubuwan na Zamantakewa kamar yanda Mummy take so.

Ahaka ma in ka ganta bata bukatar wani gyara domin mayuka da sabulan da take shafawa sun amshi fatar jikinta ainun duk Wanda ya kallah sai ya Kara,amma duk da haka ta kawo kayan gyara na fata masu inganci, magunguna na sanyi da kayan gyaran gashi da turaruka masu kamshi na gaske.

Amira ce ta shigo dakin tana waya ta zauna,saida ta gama ta Kalli kawar tata dake zaune daga ita sai wani Brown din towel.

"Kawata in aka Kara miki wani gyara akan Wanda kikewa jikin Nan naki,so kike Hilal ya haukace haka?"

Dariyar jin dadi tayi tare da fadin,
"Ai so nake Ina shiga gidan sa ya manta da duk wata mace,ko a hanya ya Kalli mace sai de ya ganta kamar namiji"
Dariya sukai tare suna tafawa,yayin da Matar dake gyara ta kawai murmushi take tana aikinta.

"Babe bari zanje in anso mana wasu kaya sai in dawo,kafin Nan ta gama miki,Nima inaso in akra gyara jikina in Kara glowing"
Dariya sukai ta tashi ta fita daga cikin dakin.

.............
Zainab soyayya suke me tsafta it ta da Umar,tana gidan su Aisha ya kirata yana kofar gida.

Da suari ta tashi ta fita,yana kofar gidan su Aisha Dan sunyi waya kafin yazo ta sanar masa tana Nan,da murmushi a fuskarta ta fito daga cikin gidan zuwa inda yake a tsaye a bakin motar tasa,kasancewar yamma ta shigo layin Babu kowa shiru.

Da sallama ta karaso inda yake,
Murmushi Shima yayi yana amsa mata tare da gyara tsayiwar sa yana fadin,
"Barka da fitowa sarauniyar mata"

Waro ido tayi tana fadin,
"Ni din?"

"Sosai mana,kece sarauniyata acikin duniyata Kinga kuwa dole na fada ko aina ne"

"Nagode"
Ta fada tana murmushi,sannan ta gaida shi,amsawa yayi yana kare mata kallo.

"Menene sirrin naga kina ta Kara kyau kina glowing Anya zan iya hakura har a gama karatun Nan kuwa,masu Daya suna karawa wasu ma biyu garesu amma neman jari kike,nide a tausaya mun"
Ya Kuma fada yana kallanta cikin langwabe Kai.

Itade murmushi kawai take tana rufe fuskar da gefan hijab dinta.

"Da gaske nake Zainab,da zaki bude zuciya da a gobe zaki gabatar Dani ko yau dinan"

"Kayi hakuri ai kamar yau ne"
Ta fada Dan bata san yaci gaba da maganar auran Nan.

"Toh ya zanyi,Nima ai duk abunda sarauniya tace dashi za'ai aiki,yanzu ma kyauta na kawo miki"

"Kyauta Kuma?"
Ta maimaita tana kallansa.

"Eh mana"
Ya fada yana bude bayan motar tasa tare da dauko wani katon kwali da aka masa Kwalliya ya Mika mata.

Noke hannu tayi alamun bazata amsa bah.

"Aikuwa baki isa ba,da kaina na zauna na hada wannan kwalin Dan ya burgeki zaki wani Nike,toh bari na Kai miki har cikin gadi"
Ya fada yana nufar gidan nasu.

ZAINAB Where stories live. Discover now