ZAINAB

16 2 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

24

.............
Dole Zainab ta hakura sai da aka tashi daga wajan Sannan suka huce,lokacin da suka Isa gida 11pm,tana sauka ta nufi gida, Maryam tayi tayi su kwana a gidan amma taki yanda,dole suka tafi gida,a kofar gida ta tsaya ta kira Aunty Farida a waya sannan tazo ta bude mata ta shiga.

Kai tsaye dakin ta shiga ta cire kayan jikinta ta canza wasu,tana kokarin fita Dan yin alwala Dan batayi sallar magriba da issha'i,kira ya shigo wayarta dama tasan za'a rina Dan kashe wayarta tayi tunda aka gama mata makeup.

Dauka tayi tare da fadin,
"Kayi hakuri zan kira yanzu"
Kawai ta kashe Dan inta biye masa ko Sallah bazatayi yanzu ba ga gajiya da bacci da take ji.

Bayan ta idara da Sallah tana zaune tana addu'a ya Kuma kira, murmushi tayi kafin ta daga hadi da sallama.
 
Ajjiyar zuciya ya sauke kamar Wanda yayi shekara beji muryarta ba.

"Ina kika shiga haka saura kadan zuciya ta ta buga wallahi"
Ya fada yana gyara zamansa.

"Kayi hakuri munje unguwa ne Kuma bamu dawo da wuri ba,wyaata Babu chaji"
Ta fada tana mikewa tare da cire hijab din jikinta.

Zama tayi gefan katifarta tana sauraransa,
"Dan Allah ki dena barin wayarki Babu chaji,kinsan kira nawa nayi miki switch up"

"Kayi hakuri in Sha ALLAH bazan Kara bari Babu chaji ba,ykk"

"Dade bana jin dadi Amma yanzu lafiya ta kalau,Kun dawo lafiya?"
Shima ya tambaya.

"Lafiya qlau"
Ta bashi amsa.

"Kin anso dinkin naki kuwa?"
Ya tambaya Dan yana San yaje da ita wajan Nan baya so a samu matsala tace bazata bah.

"Eh tun jiya ma,mantawa nayi in fada maka"

"Ok,Ya Aisha amma tare zamu tafi da ita ko?"

"Gaskiya ba lallai ba ,wata friend din mu ta gayyace mu biki,so in mu duka bamu he ba,bazataji dadi ba,shiyasa muka raba ni in raka ka ita Kuma take na friend din ta mu"

"Yayi hakan,Babu damuwa zaki bini kenan"

Murmushi tayi kafin tace,
"Me yasa ka tambaya?"

"Nasani ko tsirona kike ji Dan nace zaki rakani"

Yar Dariya tayi kafin tace,
"Me yasa zanji tsiranka toh?"

"Babu"
Shima ya fada yana jin dadi.

Sun jima suna hira kafin suyi sallama ta kwanta Dan ta gaji sosai.

...............
Yau Ake mother Eve Kuma gurin ya tsaru sosai Dan yama Fi na jiya kyau, Amarya tayi kyau har ta gaji yau ma kamar ka sace,amma zainab bataje ba, Aisha ce kawai taje,Dan tayi musu karyar ciwon Kai take yau tunda ta tashi,Kuma Lafiya qlau take bikin ne bata san zuwa nasu.

.............
Bayan an gama taro ya watse kowa ya tafi gida, Ango da abokansa hotel suka kama,Dan yau sun akra yawa sabo da har na nesa sunzo Dan halarta dinner da za'ai gobe,su Umar sune manyan abokai Dan haka sosai suke hidima da baki basa zama Basu Nan Basu can.

.............
Yau Basu bari an tashi daga dinner din ba suka dawo Dan haka suna sauka wajan 9da wani abu Aisha ta shiga wajan Zainab Dan bata labarin yau din.

Tana dakin Aunty Farida suna Kallo ta shigo da sallama cikin kwalliya kamar juya.

Bayan sun gaisa da Farida Zainab ta jata zuwa dakinta.

ZAINAB Where stories live. Discover now