ZAINAB

14 3 0
                                    

Zeenaseer *2023*

            *ZAINAB*

_not edited_

25


Tana zama Umar ya kalle ta tare da fadin,
"Ina zuwa"

Ya juya ya shiga cikin mutane, ajjiyar zuciya taja ta saci kallan wajan da Hilal da Amaryar suke,aikuwa ita yake kallo da sauri ta dauke kanta tare da zaro wayar ta ta shiga Kiran Aisha tunda tasan tana Nan,amma har ta katse bata daga ba,sau uku tana kira amma shiru,dole yasa ta maida wayar jaka ta Sakin jikinta tana kallan wajan da mutane dake ta harkokin su.

Amma Sam ta kasa sake wa sabo da tana jin idanun Hilal a kanta,Kara daga ido tayi aikuwa kallan nata yake,tsaki taja ta juya kanta gefe tana faman tsine masa acikin zuciyar ta sai kace maye sai kallo na yake.

Ta jima bata juyo ba inda yake har Umar ya dawo,zama yayi kusa da ita yana fadin,
"Babyna bakya jin yinwa?"

Tasan Hilal yana kallanta Dan haka ta langabe Kai salon shagwaba tare da fadin,
"Ai ka manta Dani kayi tafiyar ka"

Shi kuwa Umar ganin saban salon da Zainab ke masa,ga hi dama yana San mace me shagwaba yayi saurin Kara matso da kujerar sa kusa da ita yana bata hakuri.

Hilal da tun zuwa Zainab yake kallan duk wani motsi ta ji yayi a duniya Babu abunda yake da bukata kamar yaji abunda suke tattaunawa,gaba daya hankalinsa baya ko ina sai wajan Umar da Zainab,haushin su ya cika shi ji yake kamar yaje ya janye Umar ita Kuma ya maida ta gida.

Nan take zuciyar sa ta fara fadin,
"Me kake haka Hilal,bade kishin Zainab kake ba ko,kasan de kishi yana nufin soyayyah in baka Santa Babu yanda za'ai kayi kishinta"
Da sauri ya canza zancan da ba wani kishinta da nake kawai be kamata tana da aure tana biyema wani Kato suna magana har tana masa shagwaba.

Jin Hindu na taba shi yayi saurin juyowa yana fadin,
"ya akai?"

Ya fada yana kallanta.

"Ana mana magana muje muyi rawa"

Dan ba yanda zeyi haka suka sauko aka saka musu kidan,Nan da Nan aka taho ana musu liki mata da maza,sai yake yake Dan shi yanzu gaba daya baya cikin hayyacinsa.


Umar kuwa duk ya rude da shagwabar da Zainab ke masa,sai lallabata yake,sai Kuma aka kira Amarya da Ango suyi rawa,hannu ya zira a aljihun sa ya fito da nite na kudi ya Mika mata tare da fadin muje muyi liki sai in samo miki abunda zakici.

Babu musu suka jero abun sha'awa suka nufo su,tunda suka taho Hilal ya kafa mata ido yana kara karewa dinkin jikinta kallo da yanda kayan sukai mata mugun kyau harta karaso wajan su,tana murmushi ta fara masa kiki shida Amaryar sa,

Kallanta kawai yake yana aiyana irin mugun rainin hankalin ta,gaba daya ta nuna kamar bata ma taba ganin sa ba,tana masa kiki shida Hindu shi Kuma Umar yana mata,sauran abokansu ma suka fara musu ita da Umar suna tsokanar sa.

Wannan karan ba iya Hilal ba har Hindu saida taji kamar ta kashe Zainab din,Dan gaba daya sun koma kanta ita da Umar, Zainab kuwa ganin ana mata liki yasa ta dago tana kallan Hilal,ganin ya hade rai kamar ba Ango ba yasa ta fara rawa a wajan tana Dan juyawa,ai kuwa Umar ya fara zuba mata kudi kamar ya haukace,duk ya rude.

Hilal ji yake kamar ya kamata ya fita da ita daga cikin hall din,ganin ta fara jin juwa ga uban karti a kanta yasa ta fita daga cikin filin,ta nufi hanyar waje,da sauri Umar ya bita.

Hilal da Hindu wajan zaman su suka koma yayin da Hilal yaji kamar ya bisu wajan,wayarsa ya Ciro ya bara kokarin Kiran Umar din,amma har ta katse be dauka ba,dama yasan ba lallai ya dauka ba,tsaki yaja da karfi har Hindu sai da taji da dago,kallansa tayi tare da fadin,
"Baby wai menene yake damun ka,yau fa Ranar muce,amma sai faman hade rai kake kamar baka San wajan,Kuma kasan bazanji dadi ba"
Ta fada a shagwabe.

ZAINAB Where stories live. Discover now