1

69 1 2
                                    

Karamci Writer's Association.
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari).

Sakamakon Kauna!

_Domin tallata hajarki zaki iya tuntubar wannan layi 08065856251_

*
*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.
_Bismillahir rahmanir Rahim_
*

"Tun muna cikin d'aki nake tamabyar ka kud'in nan kayi min shiru wai me ka ke nufi da ni ne? In baka bani ba waye zai bani?."

"Kin taba tambaya ta abu na hana ki ne? Tunda kika ji nace miki kiyi hak'uri zan baki amma ba yau ba."

"Wallahi bazan yarda ba,zaman wani nake yi ne ko zaman ka? Toh ka ma san yadda zaka yi dani dan yau yau din nan zaka bani dan ban ga abin da zai rabani da kai ba ,kullum sai na yi yar murya zaka bani kud'i so ka ke in dinga fita daban baka da kud'in kula da ni ka auro ni? Ta mike tsaye ta jujuya jikinta sannan ta ce "Kalle ni da kyau ai ka san ni ba kalar almajirai bace toh ban yarda in fita daban ba a cikin k'awayena."

Tuntuni ya daina mamakin hallayen Sa'ada bai taba yarda zai yi dana sanin da ake cewa zai yi in ya auri wannan yarinyar ba sai yau, yau ina ya ga ranar k'in jin magana? Innallillahi wa inna illahir rajun ya dinga furtawa ya koma ya kwanta jikin kujerar yana sauke wahalallen numfashi tabbas yana son ta kuma yana kaunarta amma bazai lamunci wannan iskancin ba dalili kuwa dan kuwa raini na daya daga cikin abin da ya tsana a rayuwarsa."

Tashi ya yi zai bar gidan tayi sauri ta sha gaban shi. "K'arya ka ke yi Aliyu karya ne ni Su'ad ina magana kayi gaba ka bar ni ban san wannan labarin ba."

Aliyu mutum ne mai zuciya ya sani in ya tanka mata ko ya biye mata zai yi mata lahani haka ya sa ya sa hannu ya dan hankad'ata gefe ya fice daga falon ya barta tana ta ihu da bala'i.

"Zaka dawo ka same ni ai ni kujera ce dole a zauna dani."

Ban da sarawa babu abin da kan shi yake yi.

Babur din shi ya kunna ya tafi layinsu majalisarsu za shi gun abokin sa ,amininsa shi kad'ai ya san halin da ya ke ciki.

*

"Kin shirya ko kuwa?."

"Hmm! Wane shiri? Ai Aliyu sharrin sa ya fi na wutar nepa ya gudu ya bar ni da jarfa."

"Maganin ki ni daman na san za a zo wannan wurin Su'ad na sani ba yadda bamu yi da ke ba ki bar wannan Aliyun ki k'i gashi nan ai tun ba aje ko ina ba kina gani common dubu hamsin ta gagareshi ya bake ko ya manta ya kike ne ko wacece ke?. Ki auri attajiri ki kak'i ki ka makalewa wannan matsiyacin gashi nan ai. Ni dai kin ga sai anjima mun wuce."

Rasa abin fad'a ma tayi kawai ta ajiye wayar ta saki kuka ,kukan bakin ciki dana sani yau ita Su'ad ita ke kukan dubu hamsin.

*

Yana k'arasawa ya fak'a babur din shi a gefen dakalinsu, suka tatafa da abokanan shi ya samu wuri ya zauna.

"Ya dai Ali ya na gan ka haka?." Inji Jadar abokin shi ne.
(Abokanan Aliyu tun na k'uruciya biyar ne harda shi ya cike na shidda Faisal, Muhammad jadar,Yaseer,Auwal,Aminullahi sai shi Aliyu).

"Normal ne me ka gani?." Inji Aliyu.

"Na ga fuskar ka wata iri ko dai kai da madam ne?."

"Uhm'uhm ko d'aya kawai na gaji ne bana jindadi ko kasuwa ma ban samu na je ba ina gida tun safe."

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now