KARAMCI WRITER'S ASSOCIATION
(Karamci Writer's Association)SAKAMAKON KAUNA
NA
KHAIRAT UP
Vote @wattpadkhairi_muhd.
*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.___________________23
Bamu samu komawa Gombe ba sai da na ji dadin jikina sosai tukuna sannan na samu komawa gida Gombe. Abin da Dadda ta yi min sai da ta ba ni tausayi maimakon na ji ba dadi saboda tabbas na kwareta tunda na san hankalin ta bazai taba kwantawa ba sannan in wani abu ya same ni ita ya sama ba Hajjama ba na yi mata alkawarin bazan kuma aikata abin da na aikata ba sai dai kam abin da na yi shi ya kwatar min 'yancina a gun duk wani mahaluki da yake cikin gidansu Nasir shi ya kuma kwatar min 'yancina a gurin Nasir din shi kan sa sai ya zama na ni ma na sauya takuna babu wanda nake shayi ko tsoro a cikinsu harda Hajjama din iyaka in je in gaida ta in dawo gurina in ta amsa oho in ma bata amsa ba oho na daina yi musu aikin komai in aka yi sallar la'asar in shirya mata jikokinta Aalima da Maryam in kai mata su a hankali-hankali sai muka fara sabo da Hajjama saboda yanzu ta fara gane kyawawan hallayena kuma ta gane da zuciya daya nake zaune da danta da ita kanta saboda biyayyar da nake yi mata Sakinar da suke so bata yi musu dan bata ma taba zuwa dan gaisheta ba sau uku ta shigo garin Gombe amma zata zo gun uwarta bata zuwa gun Hajjama sai ta aika mata wai "tana gaisheta". Alak'armu ba kamar da ba yanzu ta fahimci cewa na riga na zama dolensu.
Ina yaye Maryam na samu ya maidani makaranta aiko ba karamin dadi na ji ba na yi waec dita da neco nayi jamb kuma cikin hukuncin ubangiji na cinye abin da ake so. Na cike fannin Mass Com dan ina son aikin jarida ko abin da ya shafe shi.
Cikin shekaru biyar zuwa shidda na zama wata Hajiya da ni na zama yar gayu na waye saboda yanzu ina mu'amala da yan gayu wayayyu a gurin karatu na sai na kara samun course na kwalliya da iya magana.
Ban kuma haihuwa ba sabida na yi planning ban kuma koma Gombe ba sai a cikin wannan lokacin da nake karatu Hajjama da kanta ta kai ni ta kuma yi mana nasiha ni da Sakinar da shi kan shi ubar gayyar.
Wani irin zama muke yi da Sakina sabida tana da kananun maganganu da gutsiri tsoma ga labe da gulma da an yi abu zata kira yayyar shi ya ta gaya mata ta kira ni ta yi min tas in bawa iska ajiyarta saboda babu ruwana da su duk miskilanci na Dr duk rashin maganar shi ni nake murza kambuna a gidan ai tun sanda na tafi din nan na barshi tun a sannan na nunawa kowa cewa ni ce nan komai din shi ba zai iya babu ni ba.
Yana da kishi shi yasa da ya ga na fara wayewa na fi da sai ya yi kokarin hanani yin aiki ni kuma na ce ban san wannan zancen ba dole na yi case har gaban Hajjama ta shigar min kuma da kanshi ya sama min a wani gidan jarida ina yin Editing stories. Shekarata biyu a nan na haifi yan biyuna Basama da Bassam. Zo ku ga gata da murna gun Daddy abin ba sauk'i can na tattara na koma a can familu house za ayi suna.
Nima yan uwana suka zo ran suya aka ce wai yayyunshi ne zasu yi kamar yadda suka saba yi dan su kuntatta min ni had'e rai na ci mur na ce aa ban yarda ba sai da kowa ya yi nasa su dau daya su bamu daya su ka yi ta mamakin yanzu bana daukar isksncinsu ko tsiyarsu. Haka aka yi suka dau rago daya muka dau rago daya.
Sakina daman tana bakin cikin bata haihu ba sai batani take yi a gurinsu suna hawa suna zama wai na maida Nasir bawana , sai yadda nace masa yake yi kamar wata uwarsu balle yanzu da na haifi namiji.
YOU ARE READING
Sakamakon kauna.
Romancelabari ne a kan soyayya, cin amana,yaudara,son masu wani labari ne mai dauke da darassuka ku biyo alqalamin khairat don jin ya wannan abu zai kasance.