5

10 0 0
                                    

K.W.A
  (Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.)

By Khairat UP.

   Wattpad khairi_Muhd.

     *Sakamak'on K'auna*

(Na canja mishi suna daga So Hana Ganin laifi zuwa Sakamak'on K'auna)

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

5

"Dan Allah kiyi min rai ki ba wa d'ana auren 'yarki Wallahi Aliyu yana bukatar taimako yana cikin wani hali..... Bakinta ban da karkarwa babu abin da yake yi uwa ake fad'a ban da uwa waye ke damuwa da damuwar dan shi haka? Babu mahaifiyar dai ita ce sama da komai da kowa babu ya ita duk fadin duniyarka."

"Subahanallahi! Haba Innarsu Zaitun Amira fa yarki ce Aliyu namu ne ni ko wace iriyar zuciya gareni da zan kasa baki Amira ? Me baku yi min ba ni da ita? Ai ko ba Aliyu ba ko wani kika dauko kika kawo ki ka ce a bashi Amira zan bashi balle jininki tsoka daga jikin ki."

"Bazan taba mantawa da ke ba a rayuwata kin min abin da babu wanda zai min nagode! nagode ! Yadda kika faranta min Allah Ya fatanta miki sakamakon kaunar da kike yi mana ki ka bani gudar jininki nagode da soyayya. Bari na je gun Baffan shi muzo ki kira wanda zai mata wakilci."

"Shi kenan."

Jikin Inna har rawa yake yi ta fita. Kai tsaye bayan layinsu ta nufa gidan wan mahaifin Aliyu.

"Salamu alaikum."

"Wa'alaikum salam! Ah lale Innar Baba ce bismillah."

"Mari ina Baffansu?."

"Lafiya? Ya na gan ki haka?."

Hmm! Ki fada min Baffansu na nan?.

Eh yana nan ya je masallaci amma na san ...

"Salamu alaikum Mari an kamala dai ko?."

"Wa'alaikum salam sannu da dawowa na gama sai dai ga Innarsu Baba tana neman ka."

"Toh ! Toh ! Aisha lafiya dai ko?."

Eh lafiya ba lafiya ba taimako za ka yi min Baffansu.......

Alhamdulilahi na ji dadin wannan lamarin zama bai same mu ba Allah Ya tashi kafadun Aliyu muje.

Nan aka sanar a massalaci za ayi daurin aure daman juma'a ce kuma anyi la'asar , Yayyan Amira Musa da Yusuf suka yi wakilcin kanwarsu tunda babu mahaifinsu kuma su ba yan nan ba ne zama ne ya kawosu asalinsu yan Katsina ne.

Nan aka daura aure kan sadaki naira dubu ashirin.

Sai da Inna taji an daura ta hadiyi yawun da ya tsaya mata a mak'oshinta tayi hamdala burinta ya cika.

*

"Yanzu baza ki kwana ba da gaske?." Ya fad'a yana murza yan yatsun hannayenta.

"Zan so na kwanan Habib amma bazai yuwu ba ka san Aliyu bazai bar ni ba kuma ban san a gano ni har a sa min ido na fi son mu cigaba da yin abin da muke yi a sirrance ba tare da mun yi wa kan mu tonon asiri ba."

"Bana gajiya da ke ne My love ki bar wancan solobiyon ki dawo gareni nayi miki alkawarin zama da ke."

Gefen fuskar shi ta shafa sannan ta ce "Soon in sha Allah kar ka damu ba yanzu ba sai nan gaba."

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now