*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.K.W.A
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)SAKAMAKON KAUNA!.
NA
KHAIRAT UP .
PG 8.
Ammi! Ammi! Firgit ta yi ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga ta sauk'e ajiyiyar zuciya ta ce "Haba Bassam ban hanaka yi min irin wanna abun ba?."
"Sorry Ammi tun dazu nake kiranki ke ce ba ki ji ba shi ya sa na tashe ki kiyi hak'uri amma."
"Ok ya isa me ya faru?."
"Uhm daman Aunty Salima ce ta zo da su Faruk suna falon k'asa."
Tashi ta yi ta ce "ka je ina zuwa."
"To Ammi."
Aunty Salima yayar mijinta ce kuma ba K'aunar ta take yi ba haushinta take ji a tunanunta a kanta komai na Daddy ke karewa irin abubuwan da suka yi mata bata mantawa balle su goge a idanta yanzun ma sai da ta bata lokaci kan ta fita ta samesu a falo tare da Sakina suna hira daman ta saba ganin wannan in dai wani dangin Dr zai zo toh fa zasu zauna suyi ta hira da Sakina sabida ita jininsu ce ahalinsu dr wasu irin ahali ne masu matukar nuna son kai a kan bare wanda ba dan cikinsu ba.
Da fara'a na karasa na zauna kan ns gaidata na yi mata sannu da zuwa.
Ta amsa Sama-Sama ta dan sha mur suka cigaba da hirarsu da Sakina daman ni yanzu basa gabana na daina biye musu nasan ciwon kaina sosai da dai an yi min yanzu kuwa ba wannan maganar.
"Bassam!."
"Na'am Ammi."
Ya ba a kawowa Aunty ruwa da lemo ba, akwai cake ma a cikin fridge na sama ka kawo musu su ci.
To Ammi.
Ina nan zaune ya yi yadda nace sannan na mike na dauki wayata na ce "Bari na koma ciki sai anjima."
Da alamu dai na bata mamaki da da ne rasa inda zan sa ta nake biyayya kuwa tamkar wadda nake wa uwata suna wulakantani haka nake yi musu.
"Wai Sakina haka ta koma?."
"Hmm Aunty kin gani ai shegen girman kai gareta kina ganin ta haka gani take ta fi kowa baya ma mu dangin Yaya."
"Oh wato kan mage ya waye? Damu take zancen."
"Na ji ana shirye-shiryen bikin Aalima da Sufyan."
Ta tabe baki sannan ta ce "Haka na ji amma ai yace a can za ayi bikin an ci sa'a bata hana ba."
"Ta isa ta hana ne ? Dole ayi bikin jikarmu a gidanmu haka muke mu Hajiya ke yin komai shi ya ma fara kin kai bikin Aalima can ai bai isa ba bare wata da aka auro."
"Atoh gwara ayi a can mu nuna mata matsayin ta ni fa wannan iyayin da iskancin da take yi saboda aikin da take yi ne fa shi sa take jin kanta wata A ce."
"Wai har yanzu bata bar aikin ba? Ina Hajiya ta hana wato bata isa ba ko?."
"Ga zahiri nayi mamaki ma da kika zo ki ka same ta kin san tun safe in ta tafi bata dawowa sai bakwai ko takwas na dare."
YOU ARE READING
Sakamakon kauna.
Romancelabari ne a kan soyayya, cin amana,yaudara,son masu wani labari ne mai dauke da darassuka ku biyo alqalamin khairat don jin ya wannan abu zai kasance.