15

8 0 0
                                    

Karamci Writer's Association
  (Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

     SAKAMAKON KAUNA!

     NA

KHAIRAT UP

      *FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

Ina masoya kayan Oriflame masu kyau da inganci ga Aisha Lame nan ta zo muku da kayan Oriflame kala-kala iri-iri a cikin farashi mai rahusa.
Domin mallakar naki ki tuntubeta a wannan layin.
   0703 666 2633

    
                  Pg 15.

Bai taba had'uwa da mace marar imani irin Su'ad ba ya dauka dauke mata wuta da ya yi zai karyar mata da zuciya shi yasa ya rabu da ita ya shareta ,ya dauka zuwa yanzu ta nutsu ashe da akwai saura ya dawo da niyan komawa da ita Lagos sai dai bai san ta fi shi wayo ba. Yana son Su'ad amma dole ya yakice ta daga cikin zuciyarshi da rayuwarshi ya godewa Allah da ba shi da d'a ko 'ya da Su'ad da bai san irin amsar da zai bahi ko bata ba so cuta ne amma hak'uri magani ne ba zai iya tona sirrin gidanshi ba ba zai iya tona asirin Su'ad ga su Gwagwo ba taje ta gani ai duniya ce wanda bai zo ba ma jiran shi take.

Sallama ya yi wa Gwagwo ya shige part dinsu. Ranar bai iya yin barcin kirki ba kuka ya kwana yana yi kamar ba namiji ba sosai ya ji zafin abin da ta yi masa saboda so mara algus yake yi mata.

*

Su'ad.

Bayan tafiyar Aliyu da kwana biyu ta koma ruwa tsundum dan kasa daurewa tayi har ta kai ma bata iya boyewa yanzu kuma cikin ranta bata son bayanawar amma ta kasa boye hakan ta rasa me ke ingizata ta yi tarraya da Habib. Ranar da zasu tafi kasar waje ma taga Alameen ya ganta kuma a inda ya ganta da yadda ya ganta da Habib ya sa ta ji kunya duk da ta san bazai kulata ba hakan ko ce ta faru ya dauke kansa ya tafi ya barsu a wurin.

Ita kuma suka tafi US. A can wata iriyar kazamar rayuwa ake yi da ita Su'ad din domin kuwa tamkar wata karuwa haka Habib ya maidata ayi amfani da ita a basu makudan kud'i cikin kankanin lokaci ta yi kud'i wanda har ya sa ta manta da matsayin ta a lokacin duniya kawai ce a gabanta (innallillahi wa inna illahir rajun mata mu farga.) Habib ko jira yake ya gama amfani da ita ya ware ya barta kuma ya kwashe kud'in ko biyo shin nan da ta yi asiri suka sa aka yi mata saboda turawan da ya turawa hotunanta da vedios din ta da ya d'auka bata sani ba sun tutura masa kud'in ta a kai ta can sai dai ya San ko me zai gaya mata bazata yarda suje ba shi yasa ya had'a baki da kawarta aka kai sunanta gun malami ya gama da ita. Mahaukatan kud'i yake da ita ba kananu ba gashi duk abin da ya ce mata shi take yi bata masa musu tamkar uban ta haka take kallon shi. Da ya ce Su'ad kaza zata yi ba musu ta riga ta zama abin wasa yara wadda ake amfani da ita da remote control yes Habib na controlling rayuwar Su'ad amma waye sila? Su'ad da kanta ita ce silar shigarta wannan rayuwar da bata biyewa sharrin shaidan da kawayen banza ba da Habib bai maida ta haka ba.

*

Washe gari da wuri ta tashi tayi masa abin da ya bukata ta adana. Sai da ta gama nata shirin tsab ta saka dogon hijab din ta kan  doguwar rigarta ba matsatse ba ta shiga dakin da sallama cikin sa'a shi ma ya yi shirin shi na fita so yake kawai ya fita tashi ya yi da son fita daga gidan ko yaji sauk'i a ranshi.

   K'asa ta tsuguna "ina kwana?."

"Lafiya lau" ya fad'a ba yabo ba fallasa.

"Ga abincin na kammala maka."

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now