20

15 0 0
                                    

KARAMCI WRITER'S ASSOCIATION
(Karamci Writer's Association)

    SAKAMAKON KAUNA

NA

KHAIRAT UP

      Vote @wattpadkhairi_muhd.

  
*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

_____________________20.

Bamu yi waya da Yaya ba  tunda muka isa garin harkokina kawai nake yi na shiga cikin su na saje dasu su ma sun ja ni a jikinsu sosai ayyukan ma tare muke yi ban sa k'iwa ko son jiki ba. Abin ko ya yi wa da dama dad'i ina jin Wata na cewa "Tabbas! Yanzu Baba ya yi aure kin ga yarinya mai son jama'a da mutunta mutane gaskiya wannan kofar ta yi."

"Wallahi kuwa ladingo tana da kirki sosai da sosai Allah dai Ya basu zaman lafiya ,Ya kawo zuri'a dabbaya."

"Amin!."

Na cigaba da harkokina har yau ban tambayi Su'ad ba kuma bana son sanin inda take ko ya ake ciki ni dai na san ina cikin farin cikin kasancewa da mijina duk da dai bamu gama sabawa ba amma a hankali-hankali mun yi sabo tamkar wa da k'anwa.

Washe gari aka yi kamu irin namu dai na gargajiya harda gudu na amare. Abin ya burge ni ya kawatar har yanzu akwai masu raya al'adun mu na da. Washe gari aka yi lalle babu wani fate-fate na wahala komai mai sauk'i kuma mai burgewa nima sun burge ni.

Washe gari za ayi daurin aure.

Inda muke kwana yau an kara bak'i ya cika Adda ta sa a kaimu gidan kawarta a bayan layin ko da yake layi biyu ne a tsakaninsu. Da ni da Subai'a da Maimuna muka tafi dan su raka ni su ma zasu kwanan dan sun zame min tamkar kawaye dan na Saba da su basu da wata hayaniya. Muna tafe muna hira ne wasu samari suka tsaida mu na yi tunanin ma samarinsu ne sai dai ga mamakina sai na ga suna nufin ni suke son magana da yadda na saki baki ina kallonsu haka su Subai'a suka saki baki su na kallonsu su ma.

   "Baiwar Allah kin yi shiru?."

Da k'yar na lalubi kalmar da zan fad'a musu. "Matar aure ce ni ku yi hak'uri." Na juya zan tafi suka kuma katse ni.

  "Haba Baiwar Allah bai kamata ba ni ma din mijin aure ne amma in kin ba ni damar zama mijin na ki."

Me yasa wai yanzu maza ke raina kalmar matar aure? Da ka ce kana da aure sai su yi ruwa su yi tsaki su ce su ma mazan auren ne tsaki na yi har ya fito fili kan na ce "Idan ni ba ka yarda da maganata ba ga yan'uwana nan ka tambayesu matsayina.

Maimuna ta yi tsalam ta ce "Muhammad da gaske ne matar aure ce dan Allah ku yi hak'uri ku tafi."

"Ta ya zan yarda ba bakin ku d'aya ba?."

Haushi ne ma ya tik'e ni na kuma yin tsakin na juyar da kaina na cigaba da tafiya gabana na fad'uwa na dafe kirjina juyawa na yi dan tabbatar wa da kaina abin da nake zargi ilai kuwa na hango shi tsab a tsaye daga dan nesa da mu duk da akwai dan duhu hakan bai hana ni gane shi ba a fili ko cewa na yi "Innallillahi na shiga uku!."

  Cikin takun isa da nutsuwa ya nufo inda muke ban san lokacin da na kama hannun Subai'a ba saboda wata harara da na ga ya maka min da sauri na yi k'asa da kaina gashi mayun samarin nan biyu basu tafi ba sun tsaya sun kafe sun yi mana cirko-cirko a kai wani irin haushinsu ma na ji ,ji na yi ina ma na mangaresu ma kowa ya huta.

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now