19

15 0 0
                                    

KARAMCI WRITER'S ASSOCIATION
(Karamci Writer's Association)

    SAKAMAKON KAUNA

NA

KHAIRAT UP

      Vote @wattpadkhairi_muhd.

                    

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

Domin tallata hajarki za ki iya tuntubar wannan layin 09065856251.

_ina ma'abota masu son kayan Oriflame? Aysha Lame ta shirya tsaf domin gwangwaje ku hajiyoyi Hajiya sai da gyara ciki da waje tana kayan aiki masu kyau domin morar wannan garabasar za ki iya neman ta ,ta wannan layin.
   07036662633
A kan farashi mai rahusa.

Ina masoyan natural drink? Maso son hibiscus (zobo) Jaysaar_Foods sun kawo muku hadin zobo a saukakke ba tare da kin ji d'ar ba ga lafiya,ga dad'i ga kamshi mai sanyayya zuciyar maigida kar ki bari ayi babu ke zaki iya nemansu ta wannan layin.

👉🏻09065856251.

___________________19.

Bai iya ce mata komai ba kawai ya ja kujera ya zauna kusan mintina biyu bai yi magana ba daga baya kuma ya kalleta ya ce "Na dauka ni da ke mun zama abu daya? Na d'auk'a idan kowa ba zai fahimce ni ba ke za ki fahimce ni , na d'auk'a kina daya daga cikin wadda zata yi min uzuri a fad'in duniyar nan ,na dauka ni abokin ki ne ke kawata ce kafin mu zama mata da miji ban san cewa kina min wani kallo na daban ne ba. Idan na kauce ke ya kamata ki dawo da ni hanya ki saita ni , ke kan ki baza ki so abin da zai hadani da mahaifiyata ba saboda aljannata amma ki ka kasa ganewa Wallahil azim Halima bana kin ki hasalima son da na ke yi miki ya fi na kowa bayan Hajjama Wallahi ina son ki ,Wallahi ina kaunarki fadar yadda nake jin ki a raina bata baki ne ki dago kan ki ki kalle ni ki ga yadda na koma da ni da wawa marabar mu kadan ce tun ana ba ni baki har an sa min ido saboda rashin ki ba ni da wata nutsuwa ko farin ciki... To ki manta da ni ki tuna da Dadda me ta yi miki? Kin san ko iya adadin hawayen da ta zubar saboda ke? Saboda rashin ki? Meye laifin ta? Me ta yi miki daman laifin wani na shafar na wani? Duk dan kar a maida ki gidana? We can resolve it ai why sai kin gudu? Why?.Yayyunki fa? Me suka yi miki? Mai suka yi miki?. Kin dauki hakkina ni da Aalima kin rabani da ita yanzu kuma kin kuma daukar hakkina baki sanar da ni cikin ki ba duk dan kiyayya? Wai me ma aka yi miki? Karatu ne za ki koma ,Gombe ne shi ma za ki koma , yayyun ne su ma zasu daina yi miki abin da ba kya so, kannena za su dinga ba ki girman ki dan Allah ki yi hak'uri ni bana son na ji komai , kawai ki manta komai ki dawo cikin rayuwata na yi miki alkawarin kasancewa adali mai kula da ke. I promise you that."

Sai da na yanka mi shi harara kamar idanuwana zasu fad'o ba dan wai ina jin haushin shi ba Allah Ya sani kaso casa'in na haushin shi da nake ji ya sauka maganganun da ya fad'a gaskiya ne babu abin da Dadda ta yi min, ba bu abin da su Hamma suka yi min babu abin da Aalima tayi....

  "Za ki bi ni mu koma ko sai na d'auke ki a kafada ta har Gombe?."

Ban san lokacin da na yi dariya ba na dake shi a kirji aka ce tsakanin mata da miji sai Allah!. Nan na manta da komai kuma na rike alkawarin shi kam a raina zan koma makaranta zan koma Gombe zan samu respect din da nake bida daga gidansu. 

  "Ban ma kirasu na gaya masu ba bari na fara kiran Baiwar Allah Dadda ko ta samu hankalinta ya kwanta."

  Bugu uku ko ta dauka da sauri.

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now