7

10 0 0
                                    

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

K.W.A
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)

  *Sakamak'on K'auna*

Na

Khairat UP

Vote@wattpad khairi_muhd.

                   7

Yanzu in Su'ad taji ya yi aure ya zai yi? Shi bai san ma dalilin da ya sa aka yi mishi haka ba bai ce musu yana buk'atar aure ba taya ma zai iya dasu su biyu baya son tashin hankalin Su'ad kuma bazai iya kin bin umarnin Gwaggo ba ajiayar zuciya ya s'auke ya tashi yaje ya yi wankan ya fito ya saka gajeran wando da singlet ya fita falon ya zauna kan one seater ya dafa goshinsa.

"Jikin ne?."

"Uhm'uhm ba komai kawai na gaji ne."

"Ayya daman ai da gajiya yanzu dai baka jin komai ko?"

"Eh! Bana jin komai alhamdulilahi da sauk'i."

Wayarshi ta soma ruri ya kalle ta dauko min kila Gwagwon ce.

Toh ta tashi ta dauko masa ta kawo mai .

Kiranta ya yi.

"Hello Gwagwo."

"Hello Baba ya jikin? Ka ci abinci? Da sauk'i? Babu inda ke maka ciwo ko?....."

"Gwagwo Wallahi da sauk'i naji sauk'i sosai babu inda yake min ciwo yanzu ma abinci zan ci in sha magani."

"Ma sha Allah! Ka ci ka sha ka huta kaji ban da damun kan ka . Gobe yayyunka zasu zo in sha Allahu."

"Toh sai sun zo."

Suka ajiye waya. Su'ad da ta kura masa ido tana jiran Karin bayani kakalo murmushin karfin hali ya yi ya ce "Su Adda ne zasu zo dubani gobe kiyi abinci da dama."

"Ni fa ka san kasuwanci na baya son zama wuri guda kawai."

"Ban gane ba."

"Ina nufin bazan zauna ba gobe ina da kaya da zasu zo."

"Kayan ki sun fi lafiyata?."

"Ban ce ba ka fahimce ni...." Ya daga mata hannu ya isa kije zan koma gidan Gwagwon anjima in zauna a can tunda dai kin sani za ayi ta zuwa dubiya nufin ki ni zan zauna ni kadai duk wanda yazo ya yi da ni kije anjima zan koma gida.

Ko gezau bud'ar bak'in ta sai cewa tayi "Eh Wallahi da ya fi ma ba mai sa ni aiki ko ya bata min kaya."

Takaici ma bai sa shi yin magana ba in Su'ad ta yi wani abun kamar ba mai hankali da tunani ba ya fara zargin ma anya kuwa tana son shi? Saboda ta sauya akwai sauyi a tattare da ita sosai.
   Kiran Alameen ya yi ya ce ya zo ya maida shi gidan Gwagwo.  Alameen bai ja maganar ba kawai bayan magariba ya karasa ya taho da shi Su'ad na kallo harda daga musu hannu.

*

"Ke dazu na ni wai an yi daurin auren ki da Baba Aliyu?. Da gaske ne ko kuma sharrin mutsne ne?."

" Da gaske ne Aisha."

"Ma Sha Allah amma na yi miki murna gaskiya kun dace."

"Hmm! Wane dacewa baya sona ko kallon inda nake baya yi fa."

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now