3

18 0 0
                                    

Karamci Writer's Association
    (Karamci shi ne tushen mu'amala tagari).

       Na

Khairat UP

Watpad khairi_muhd.

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

_Domin tallata hajarki za ki iya tuntubar wannan layin 09065856251_

              Pg 3.

Ka'idar shi ce kan ya je kasuwa sai ya bi ta gun Innarshi ya gaida ta sannan yake tafiya tazararsu ba mai yawa ba ce ba layi biyu ne tsakaninsu.

Yana faka Babur din shi lokacin da Amira ta fito daga gidan kenan cikin shiga ta kamala saida kirjinta ya buga lokacin da ta gan shi ta rasa gane abin da ke damun ta a duk san da take ganin Aliyu in har zata ganshi to tabbas zata ji jikinta ya yi sanyi,kirjinta na bugu da sauri da sauri , bata sakewa har sai sun rabu kullum tunaninta ko dai duk tsoron shi ne?.

      "Ina kwana Ya Aliyu."
Ko kallon ta bai yi ba kamar kullum ya yi shigewar shi ciki sai jikinta ya yi sanyi ta tafi kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki ta rasa gane wace iriyar k'iyayya ce wannan gashi bata jin haushin shi k'ara burge ta ma yake yi. Haka ta tafi jiki babu wani laka.

*

"Asalamu alaikum."
"Wa'alaikum salam."
    
Kai ne tafe?.

Eh inna zan wuce nace bari na shigo tukuna.

Ka kyauta.

Ina kwana inna.

Lafiya lou ya ka ke?.

Lafiya , Alhamdulilahi.

Ma Sha Allah.

Inna zan wuce kasuwa ayi mana addu'a.

Ai muna yi ba fashi Allah Ya yi wa rayuwa albarka.

Amin Inna Amin.

Har ya mike ta kuma tsaida shi.

    Youwa ka kawo takurdun ka na boko inji Baffan ka na Lagos ya yi waya jiya da Kabira ta zo ks tura takardun kila Allah zai sa a dace ko rabon ne ya zo.

Toh Inna Allah Ya sa rabon ne.

Amin.

Da farin ciki ya tafi Kasuwa ranar har wannan murnar ta matar da shi damuwar da Su'ad ta saka shi.

*

Su'ad kuwa yana fita ta kunna wayarta, tana kunnawa sak'oni suka yi ta shigowa ciki har da na Habin babban yaro.

     "Hi ! Kar fa ki manta da alk'warin mu. Don ko wane irin lokaci zan bayyana miki kuma in lokacin ya zo ba gudu ba ja da baya.
         Habib"

Sako na biyu ma na shi ne.

   "Na jima ina k'ewar ki ,na jima ina rokon Allah da ya dawo min da ke cikin rayuwata duk da na ji haushi da kika zabi wannan fak'irin a kaina amma duk da haka baki dusashe a idanuwana ba. Ina son ki rabu da wannan mutumin nayi miki alkawarin kasancewa da ke har k'arshen rayuwata a inuwata.
          Habib."

Murmushi tayi hade da jin kanta yana yawo a sama ta sani ita din mai kyau ce kuma mai kyan diri ce komai nata perfect ne ta sani ita din matar manya ce bata san lokacin da soyayyar Aliyu ta shigeta ba har ta rufe mata ido taji in ba shi ba babu wanda zata rayu da shi, in tace bata son Aliyu ta yi k'arya sai dai ta fi son hutu,kudi,mutunci,gayu da 'yanci irin na matan manya kamar kowacce matar manya shin in ta bar Aliyu ya rayuwarta zata kasance? Wata zuciyar ta k'wabe ta in kika bar Habib za ki bar tarin alkhairin dukiya da ke jiran ki. Karshe dai bata samu mafita ba ta tashi dan yin shirin fita.

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now