Karamci Writer's Association
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014._Domin tallata hajjarki za ki iya tuntubar wanna layin 09065856251_
SAKAMAKON KAUNA
NA
KHAIRAT UP
Vote@wattpad khairi_muhd.
Pg 9
Ikon Allah ne kawai ya kai Aliyu d'akin shi hannunshi dafe da kirjinshi har yanzu bai yarda da abin da ya gani ba ji yake ina ma mafarki ne ya tashi daga wannan mumunan mafarkin tabbas so cuta ne in dai irin son da yake yi wa Su'ad ne to tabbas so cuta ne bai san iya adadin son da yake yi mata ba a kan ta kusan kowa sai da suka yi fad'a,a kan ta babu wanda ya goyi da bayan shi daga baya ne ma aka fara sasauta mata yanzu irin Sakamakon Kaunar da zata saka mishi da shi kenan? Innallillahi wa inna illahir rajun Allah na tuba Allah ka yafe min ina ma ban ga wannan bakar ranar ba ina ma na makance kan na ga wanan mumunan ganin wannan shi ake kira bak'in gani. Da ya kulle idanshi su yake gani ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa gaba d'aya baya cikin hayyacin shi gashi gobe za shi interview din.
*
Suna zaune suna sharholiyarsu sun manta da cewa akwai Allah ko kuna komai zai iya faruwa a ko wanne lokaci gaba d'aya Su'ad ta daina tunanin komai sai son duniya ta sa a gaba da ganin ta mallaki duniya ba karamin rud'i duniya ke yi mata ba ta manta da aure a kan ta rayuwarta kawai take yi ba damuwa sabida ta gama sa wa a ranta ta tsira ba mai kamata ko tona mata asiri.
Cikin hirara da suke yi ns taji kamar an kira sunan ta sai dai ko da ta waiga bata ga kowa ba sai ta cigaba da harkarta duk da zuciyar ta na kwabarta a kan kiran da muryar mai kiran amma bata maida hankalinta a kai ba. Ta riga ta gama tsara karyar da zata yi wa Aliyu game da kashe wayarta shi ya sa ba ta yi tunain neman shi da wani layin ba.
"Habib kwana biyu ina yawan jin fargaba sai na ga kaman akwai abin da zai same ni."
"Haba me zai same ki bayan gani ke bari ki ji ni fa yanzu babban burina auren ki da wannan matsiyacin ya mutu na aure ki gaba daya wannan rayuwar da muke yi ta gundureni bata burge ni so nake na killace ki a gidana da ni kika dace ba wancan mutumin ba ke fa matar manya ce."
Murmushi ta yi kanta ya kuma fasuwa kafin ta ce "Ina son Aliyu tabbas ina son shi amma son da nake yi wa kud'i da rayuwar hutu ya fiye min a kan Aliyun tunda kai za ka bani su to meye wani Aliyu lokaci nake jira da zamu rabu salin'alin kasan kuwa sama da shekara ban yarda Aliyu ya taba koda dan yatsa na ba balle a kai ga ya taba jikina."
Wani irin murmushin mugunta ya yi mata kan ya gyara zaman shi ya ce "Kina burge ni Su'ad kina burgeni sosai saboda ba kya b'oye sirrin zuciyarki."
Nan suka cigaba da hirarsu.
*
Duk yadda Amira ta so hana kanta kiran Aliyu kasawa tayi ji take yi kaman ana ingizata ko kuma in bata kira shi ba wani abu sai sami rayuwarta.
Sai da ta kira ya fi sau biyar harta sare sai kuma taji ya d'aga in taji da kyau ma muryarshi a dashe kamar mara lafiya ko wanda yake mura ko wanda ya yi kuka haka ta daure ta ce "Hello ina wuni fatan ka isa lafiya?." Bakinta har harhardewa yake yi wajan had'a kalmomin dan karta bata mishi rai.
"Lafiya wace?."
"Ni ce Amira....." Tsaki ya yi diff kuma ya kashe wayar ,haushin kowa yake ji mussmman ma ita wannan anacen da ta addabi rayuwarsa aka kakaba mishi ita yarinyar ta fiya naci da taurin kai.
A bangaren Amira kuwa ji ta yi wani irin kuka ya zo mata tana jin haushin yadda yake yi mata amma bata iya yin fushi da shi ta rasa wannan wane irin so take yi mishi wanda baya barin ta ga laifin shi hannayenta ta daga sama ta ce "Ya Allah ka kawo min saukin abin da yake damuna idan Yaya Aliyu ba alkhairi ba ne a tare da ni Ya Allah ka kawo min karshen wannan zaman."
*
"Kamar yadda ya fad'a Su'ad asalin yar unguwarsu ce Yaksai a bayan layinsu gidansu yake gidansu Su'ad gida ne irin na gidan yawa wanda kowa sha'anin gaban shi yake yi ba mai kwabar wani dalili kuwa mazan gidan ba tsayayyu ba ne ba suma ba su wani damu da al'amuran gidan ba ne ba sai dai mahaifin Su'ad mutum ne tsayayye mai kamewa da sanin ya kamata shi ne karami a cikin yan'uwan shi bangaren shi yana daga k'arshe a gidan matarsa guda Inna Aisha wadda take yin dambu da wake da shinkafa na siyarwa , shi kuma yana yin faci ne a bakin titi duk da haka basa rasa ci ko sha daidai gwargwadon iyawarshi ya na yi dan ganin iyalin shi basu rasa komai ba. Ya'yan shi hudu maza biyu mata biyu Su'ad ce karama a gidansu sai dai ta fi kowa buri a dakinsu tana da son a ce ita yar wata ce hakan ya sa ta jajirce wajan karatu musamman na boko ta iya turanci sosai da sosai saboda tana mu'amala da ya'yan manya na unguwar tun Innarta na tsawatar mata harta hak'ura ta koma yi mata fatan shiriya yayarta Amina ta yi aure yaranta ma biyu yayyunta maza Aminu da Hafizu suna karatu a bayero university kuma suna yan bugabugarsu dan Hafizu ma karamin shagon aski ne da shi a bayan layinsu in baya nan Aminu na shagon da haka suke tallafar gidansu suna rufawa juna asiri sai dai duk wannan bai ishi Su'ad ba burinta mai girma ne sosai hangenta mai tsayi ne tana da burin auren hamshakin mai kudi, ta sha fad'a bazata tashi a talauci ba kuma ta kare a talauci ba dole ne ma ta auri maikudi ta more rayuwarta da kuruciyarta tunda bata mora a gidansu ba ta mora a gidan miji.
Mahaifinta mutum ne mai sa ido sosai kan lamuran gidanshi sai dai duk takurarshi da tsade gidanshi bai iya tankwara ko juya Su'ad ba domin kuwa bata da tsoro ko shayin kowa haka Allah Ya yi ta gashi bata iya magana ba kuma ko maganrta zata kashe ka sai ta gaya maka gaskiya haka take kai tsaye take yin komai.
YOU ARE READING
Sakamakon kauna.
Romancelabari ne a kan soyayya, cin amana,yaudara,son masu wani labari ne mai dauke da darassuka ku biyo alqalamin khairat don jin ya wannan abu zai kasance.