13

9 0 0
                                    

K.W.A
{Karamci shi ne tushen mu'amala tagari}

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

Domin tallata hajjarki tuntubi wanan number...09065856251

SAKAMAKON KAUNA
              NA
         KHAIRAT UP

    PG 13.

"Ni ba haka muka yi da kai ba kuma ba haka muka yi da Abba ba ya za a katse min karatu ayi min aure kuma yanzu a zo a ce min bazan koma ba an yi min adalci kenan?."

Dr ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ki taimake ni Halima ki taimake ni na yi wa Hajjama biyayya...."

"Ban hana ka yi mata biyayya ba amma ni dai bazan fasa karatuna ba." Na sa kai na bar dakin na barshi a gurin.

Ina fita daga d'akin na ga yayyunshi a bakin kofar suna min kallon banza ni na na auna musu harara na yi gaba na barsu baki bud'e.

     Ina jinsu a tsakar gidan suna maganata da Hajjama.

"Uh'uh kar ku ce min juya shi take yi?."

"Wallahi Hajjama ki daina raina kankantar ta juya shi take yi kamar waina in baki tashi a tsaye ba za ki ga Nasir ya fita daga hannunmu musamman ma ke. In har ta koma makaranta ta tabbata Nasir ya fita daga hannunki."

Baki ta kama kan ta ce "Shi kenan ai mu zuba mu gani ba ayi dan da zai kawo matar da zata sa ya kin jin maganata ba bai haifu ba."

"Gwara dai ki san na yi kam."

Da haka kullum suke zuge matar nan a kaina tsaf ita kuma take hurawa d'anta wutar tsanata ko ya hana ni sukuni ni kuma muna samun matsala da shi dan na kafe nima bazan yarda ba.

Kan Dr ya yi zafi ya rasa inda zai saka ranshi ya ji dad'i gaba daya sun caja masa kwakwalwa.

"Yanzu ke ba za ki bani goyon baya na yi abin da Hajjama take so ba? Kina ganin yadda duk kuka maida ni ke da za ki sa na ji sanyi a gun ki ke ce za ki na kuntata min haba Halima haba ki ji tausayina mana."

Kuka na fashe da shi sosai na ce "Shi kenan tunda ni ba mutum ba ce ko kuma dan iyayena talakawa ne shi yasa za ayi min haka ina gani fa yan gidanku duk basa so na harda ita Hajjama din , ina sane da kallon mai aiki suke yi min, ina sane da irin ayyukan da suke tula min ban taba yin magana ba amma yanzu shi ne zaa yi min haka."

Rungume ni ya yi a jikin shi sannan ya ce min " Hajjama mahaifiyata ce ba ni da na biyunta Wallahi matar nan da ki ke gani ta yi mana komai musamamn ma ni da ta fifita a cikin yaranta ni ta tsayawa tsayin daka har na yi ilimi na kawo wannan matakin a rayuwata bayan rasuwar Baffanmu ita tayi mana komai a lokacin da dangi suka juya mana baya ta yi duk iya fafutuka da kokari dan ganin ta sa mun yi nasara a rayuwar mu yanzu ya ki ke gani in na bujure mata saboda na yi aure? Na san ke mai tarbiya ce   Dadda da  Abbanki da Auntynki sun yi miki tarbiya kuma sun koya miki bin nagaba da ke kar ki watsa musu k'asa a ido wannan kadamin da muke ciki na dan lokaci ne ni na yi miki alkawari in sha Allah a gaba zan maida ki karatun za ki yi na yi miki wanna alkawarin amma yanzu mu yi hak'uri uwa ce zamu ga cigiba a nan gaba."

Wannan lallabanin da ya yi shi ya saukar da ni ya sanyaya min rai na, na hak'ura da kudurina.

Ba abin da ba na yi wa Hajjama haka ya'yan yayyunshi in sun zo da kannen shi. A nan ta fara dan sasauto min tana amsa ni in ina magana sai aka rage min aiki sosai.

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now