KARAMCI WRITER'S ASSOCIATION
(Karamci Writer's Association)SAKAMAKON KAUNA
NA
KHAIRAT UP
Vote @wattpadkhairi_muhd.
______25
*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014._____________________
"Wallahi ban taba tsanar mutum kamar yadda na tsani Halima da yaranta ba kwata-kwata sun gama da ni ta gama cin riba."
"Kar ki yi saurin karaya Sakina ba na so ta samu lagon ki zamu yi maganin ta kafin lokacin."
"Wai fa had'a auren nan na sa aka yi dan in ga me za ta yi sai kuma na ga ta karbi abin da kyau wannan mata makira ce ta karshe."
"Hmm! Yanzu yaya kike ganin za ayi?."
"Kaina ya kulle ki bari zamu yi wani abun kafin auren."
"To."
*
Dr ya sa ana gyara bangarensu na can Kumo an yi fenti a gidan gaba d'aya an gyara ko ina an sa wa Halima sabbin kayan furniture's an yi mata gyaran zamani kayan su sun riga su isa. Shirye-shiryen biki kawai ake yi yayin da wasu zuciyar su ke fes wasu kuma zuciyarsu kudum. Wasu daga cikin masu bakin cikin cigaba Halima sun had'a da yayyun Dr da suke dabi da ita tun asali bare da suka ga yanzu kud'i sun zauna mata, wayewa ta zo mata ga kwalliya da kuma aji da ta karo gashi yanzu bata raga musu in sun yi mata zata maida musu ko kuma ta d'auke su ta watsar tamkar ba ta san da iskar da ta kwaso su ba. Ga Hajjama yanzu tana sonta bata yarda da zance in sun kai mata. Ga Sakinar ma bata da wani fuss a gidan sai abin da Halima ta ce abu dai gashi nan goma da ashirin.
Dr ne zaune kan kujera a falon shi yana karatun jarida kamar yadda ya saba idanunshi sanye da farin glass irin na likitoci dai, hankalin shi gaba daya na kan jaridar ta shi fuskar nan murtuk babu wata fara'a daman shi haka yake mutum ne shi me tsare gida baya daukar wargi balle ya baka fuskar da zaka raina shi mutum daya ce ke iya bi da shi Halima ta san kan shi ta san yadda zata tafiyar masa da rayuwarsa shi yasa matsayin ta daban yake a kirjin shi baya hada ta da kowa dan duk wani yanayi na shi tana ganewa har ma ta san yadda zata bi dashi.
Sanyayyan k'amshin da ya doki hancin shi ya sa shi yin murmushin gefen baki ya gyara zaman shi ya ajiye jaridar ya yi sauri ya juya yace "Statue" tsayawa ko tayi a inda take ba tare da tayi motsi ba sai dai murmushin da yake dauke da kyakyawar fuskar ta hakorin makkan ta ya yi mata kyau ainun hannun ta kuma kofin shayi ne da ta kawo masa, sanye take da wata arabian gown tayi mata kyau ainun sai kamshi take lebben ta ko lip blam ne kawai ta shafa musu.
"Hmm! Yau wa na kama?."
Bata ce komai ba tunda a statue take.
Sai da ya gama zagayeta tsab tukuna kafin ya samu cikin ta ya yi mata wani irin mintsini da sai da ta motsa had'e da cewa "Ouch". Dariya ce ta kama shi kafin ya samu kunnen ta ya sumbata ya gangaro kan hancin ta kafin ya yi mata kan lebbanta kafin ya saketa ya kuma yi freeing din ta ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ajiye kofin shayin ta juya tana kallon shi da sauri ya yi baya ya ce "Me?."Ai da gudu ta nufe shi da sauri ya yi gefe ya na zagaye d'akin tana bin shi Wallahi sai na rama bazan yarda ba sai na rama dan mugunta ta kuma kasa kama shin daman a lokuta da dama haka suke yi in soyayyar ta tashi sai ya ga ta jigata sosai tukuna sai ya tsaya ta kama shi yau ma hakan ce ta faru kan kujerar suka fad'a suna kallon junan su ido cikin ido cike da so da K'auna wani irin abu kawai ke yi musu kai kawo a kwanyar su, gashin kanta da ya dan kwanto fuskarta ya yi maza ya maida mata baya ya ce "Gimbiyata kullum dai ba kya tsufa kin zama beni kamar ba ke ce za ki aurar da Aalima ba."
YOU ARE READING
Sakamakon kauna.
Romancelabari ne a kan soyayya, cin amana,yaudara,son masu wani labari ne mai dauke da darassuka ku biyo alqalamin khairat don jin ya wannan abu zai kasance.