K.W.A
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari)SAKAMAKON KAUNA!
NA
KHAIRAT UP.
Vote@wattpad khairi_muhd.Pg 14
"Haba baiwar Allah bai kamata ina bin ki ina ta son yi miki magana kina share ni ba ko ba dan ni ba dan Allah ki tsaya."
"Bawan Allah dan Allah ka rabu dani ka daina bi na ni matar aure ce."
"Ni ma mijin aure ne." Ya fad'a da fara'a kwance a kan fuskar sa.
"Ba wasa nake yi maka ba da gaske ni matar aure ce anyi aure na kar wani ya gan ka da ni ayi...."
Daga baya Amira ta ji an ce "Me kike yi a nan?."
A tsorace ta juya dan Jin muryar wanda ba ta yi zato ba cikin ina-ina ta ce "Yaya Ali!."
Hararta ya fara yi kan ya juya ya kalli saurayin ya ce "Malam matata ce."
"Ku yi hak'uri dan Allah ban yi zaton da gaske take ba."
Hanun Amira ya ja suka yi hanyar gida suna zuwa kofar gida ya saki hannunta ya maka mata harara sannan ya ce "Dan ba na nan shi ne ki ka fara kule-kulen samari? To kar ki damu na kusan baki takardar ki ai sai ki kula koma waye amma ina so ki kula kar ki sake na kuma ganin kina kula wani da aure na shi ne gargadin da zan miki kawai.
"Wallahi ba ni na kula shi ba kuma islamiya naj...."
Shigewa ciki ya yi ya barta a gun ta saki kuka kusan minti biyar ta yi a gun tana kuka kan ta shiga ciki bangaren su ta shige ta gyara fuskarta kar Gwagwo ta gane ta yi kuka.
*
Har yanzu bata dawo ba ne Amira din?.
Ta dawo tana zuwa na ganta a waje.
Toh. Ya Su'ad din?.
Tana lafiya tana gaishe ki .
Bana amsawa ai da tana gaisheni zuwa zata yi ta gaishe ni ba wai ta bada sak'o ba ni ban san ma ranar karshe da na ganta ba Wallahi. Allah dai Ya kyauta wannan matar taka wuri ta samu daga wurin ka amma ni ban san dan da na haifa zai tsaya yana kallon matarshi tana raina ni amma baya cewa komai.
Kiyi hak'uri.
Kullum dai zancen kenan in yi hak'uri. Wadda ta ke ganin girman uwarka ka rainata baka son ta wadda ka ke so din kuma ta raina uwarka kayi ta yi kai ne solebiyo.
Shi dai bai ce komai ba yanzu ma da yaje gidan Su'ad bata nan kuma taki daga wayar sa ya je gaida iyayenta ko can taje amma shiru bata gidan Suma tamabayarta suke yi ya rasa wacce iriyar rayuwa ce Su'ad ta sa kan ta a ciki ya san bata ji ko a da amma tana shakkar ya kamta da laifi amma yanzu... Wani irin kamshi ne ya sauya masa tunaninsa ya ji ya dawo duniyar da ake ciki juyawa ya yi ya gan ta cikin abaya ta sauya kaya fuskar nan natural beauty ba wani sirki ko powder babu a fuskar sai man lebbe fes da ita bai taba yi mata kallon kurrila ba sai yau farinta mai kyau ne babu wanan bleaching din na zamani da yan mata suke yi, idanuwanta irin sexy eyes din nan ne masu daukar mai kallonsu sauri ya yi ya sunkuyi da kan shi ganin tana kallonshi.
"Gwagwo sannu da gida."
"Yauwa yar albarka.kin dawo lafiya?."
"Lafiya lau. Kin ci abincin da na ajiye miki?."
"Eh! Ya yi dadi kuma har muna yar kokawa da Ali yaji abinci mai dandano."
Murmushi kawai ta yi ta dauke kan ta. Shi kuma a fakaice yake kallonta ya rasa wane irin mayen karfe ke jan ra'ayin shi dan ya kalle ta cikin ran shi ya ce "She's so simple." Wayar shi ta soma ringing ya dauko *Saffiya* ya gani a kan screen din wayar ta shi ya ki d'auka har kusan sau hudu daga karshe Gwagwo ta ce mi shi "Ka d'auka mana."
YOU ARE READING
Sakamakon kauna.
Romancelabari ne a kan soyayya, cin amana,yaudara,son masu wani labari ne mai dauke da darassuka ku biyo alqalamin khairat don jin ya wannan abu zai kasance.