6

11 0 0
                                    

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

Domin tallata hajjarki tuntubi wannan layin.

09065856251.

K.W.A.
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari).

     Sak'amakon Kauna!.

Na Khairat UP

Vote @wattpad khairi_muhd.

               Pg 6.

Gombe!.

Yanzu da gaske Daddy ba za ka janye wannan hukuncin ba? Baka ganin Anbaby yarinya ce har yanzu ni gani nake a barta ta kammala karatun ta in ya so sai ayi ko ma meye.

    Shekarunki nawa na aure ki? Bana jin kin kai sha takwas lokacin da na aure ki gashi kin Haifa min Aalima,Maryam,Basma da Bassam me kuma ki ke so? Ban ce zata daina karatu ba anma a gidan mijinta zata yi.

Nunfasawa ta yi sannan tace "Allah Ya sa albarka."

Ya saki fara'a dan haka yake so ta fad'a daman.

Ni ko na san a gidansu aka zugo shi ko in ce aka saka shi kuma na sani dan a k'untata min ne ni kuma bazan basu damar da zata sa su hana min 'ya karatu ba wannan makircin Sakina ne.

Shafa fuskata da ya yi shi ya sa na yi firgit na kalle shi.

"Ki yarda da ni bazan cutar da Aalima ba ke shaida ce a kan irin son da nake yi mata na fi so a kullum in na kawo abu ki yi na'am ki goya min baya kai tsaye ba tare da shakku ba babu wanda ya isa ya bak'anta miki ko yaranmu a duniyar nan in har ina raye ina numfashi zan tsaya tsayin daka a kan ku.

     Murmushi na yi kawai ko ba komai yana nuna kulawa a kan mu bazan watsa masa k'asa a ido ba.

*

Ina komawa gida na shiga d'akin su kai tsaye Ma Sha Allah ta yi kyau cikin shigar lace tayi kyau dan tabarakallah Aalima na cikin sahun kyawawan mata tana da idanuwa manya kuma fara ce sosai in na ce fara ina nufin fara idan ta irin mai tafiya da mai kallon ta ne tana da diri tamkar ya ni sai na kasa daina kallonta...

  "Ammi ban yi kyau ba ko?."

Dariya na yi na karasa cikin d'akin sosai na dafa ta na ce "Tabarakallah An babyn Daddy ta girma."

Murmushi ta yi ta ce "Ammi wane irin bak'i za ayi haka da sai na yi kyau?."

   Hmm! Daddy ne ya ce ki shirya za ki yi bak'o ne kila ma yana falon Daddynku .

Gabanta ne ya buga nan da nan annurin fuskarta ya sauya ta koma ta zauna da baya kan ta ce "Ammi me ya sa yanzu? Karatuna fa?."

"Za ki cigaba mana Aalima ke kin sani Daddy ba zai bari kowannenku ya yi ta zama har wannan lokacin ko fiye da haka bai aurar da ku ba ko kin manta dokar familynku?."

"Ammi wannan dokar ai ba fadar Allah ba ce...."

Na bata rai na ce "kul! Kar na kuma ji kiyi abin da aka sa ki in sha Allah khairan."

   "Idan kuma bana son shi fa?."

"In sha Allah ma handsome ne zai sace zuciyar Aalima ta."

Sunkuyi ta yi da kan ta tana mai jin kunya.

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now