12

12 0 0
                                    

K.W.A
(karamci shi ne tushen mu'amala tagari).

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*
*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

Domin tallata hajar ki za ki iya tuntubar wanna layin. 09065856251.

    SAKAMAKON KAUNA

     NA

KHAIRAT UP.

             PG12.

Hannu bibiyu ya sa ya dafe kan shi yana huci wani irin daci bakinshi ke yi mishi innallillahi wa inna illahir rajun kawai yake maimiatawa a hankali ya fara jin sauk'i a kirjinshi zaunawa ya yi a kan kujera kusan minti goma bai iya cewa komai ba. Ita kuma duk ta tsure ta zama abar tausayi bata son su rabu ta wanan hanyar ta fi son su rabu salin-alin cikin mutunci ba tare da kimarta ta baci a idanun shi ba.

"Gaskiya Aliyu ka ba ni mamaki da ba ka dauki kananun maganganu a kaina ba sai yanzu? Me ya sa zaka bada kofar da za a rusa mana zaman lafiyar mu ? Aliyu bai kamata ka na jin maganganun mutane ba ka san irin son da na ke yi maka ai ka san...... "

"Wallahi Su'ad idan baki bar gabana ba zan iya aikata miki komai a tunanin ki duk abin da nake yi ban sani ba ne? Ko kina tunanin damar da kika samu ban san abin da nake yi ba ne? Su'ad na bud'e miki kofa na baki dama kiyi duk abin da ki ka ga dama amma banda taba mutuncin aurena da yake kan ki ni... Ya kasa karasawa yaji wani irin nauyi da kunyan abin da zai fada ya yi tsaki ya fita daga gidan."

Zaunawa tayi dabas a k'asa ta ce "innallillahi na shiga uku wane munafukin ne ya kawo masa gulma?. Yanzu ya zan yi na karyata hakan , ya zan yi na wanke kai na a gun Aliyu? La'ilah."

Da sauri ta tashi ta dauko wayarta ta goge duk wani abu da zai iya tona mata asiri ta kira Habib ta ce ya canja taku  ya dan jinkirta na yan kwanaki akwai matsala.

*

Bakin layinsu ya fita ya samu wani dakali ya zauna a kai ya hade kan shi da gwiwar sa ya saki kuka kamar karamin yaro ashe haka ake jin zafin cin amana? Ashe haka ake jin ciwon abin ? Ya Allah ko makiyina kar ka jarabce shi da irin wannan musibar.

*

"Gwagwo ya kamata ki kira Baba Ali ki yi ma sa maganar tariyar Amira ba kya ganin shirun ya yi yawa? Kin ga fa mahaifiyarta tayi kawaici sosai bata taba tambayar mu ba ta sa mana ido mu kuma muka nemi abin nan aka bamu kuma mu sai mu bar yarinya a gaban iyayenta?."

"Wallahi Muhaseen jira nake yazo kin san Aliyu ba son ta yake ba tsoro nake ji in bashi ita ya je su yi ta yi mata wulakanci shi da matar shi."

"To ya gyara wanacn dakin na soro mana a kara masa da wancan filin ayi daki da falo a yi musu bandaki a ciki ya zama tana nan kina sa musu ido har ki ga yanayin zaman sai ki sa ya dauketa."

"Hakan ma shawara ce mai kyau zan yi magana da Ayuba (kaninta ne) ya zo ya duba gun ya tsara a fitar musu da shi ni kaina sai hankalina ya fi kwanciya gaskiya."

Nan suka tattauna suka tsaida magana. Filin Gwagwon ta sa aka saida ta bada a fara yin aikin dan tana son alakar nan ta dore tana ji a jikinta Amira alkhairi ce a rayuwar Aliyun ta. Ba a yi shawara da Aliyu ba aka fara gini a gidan Gwagwo da ke gidan da girmanshi kuma da fyalle-fyallen dakuna a waje sai aka had'e su kuma Gwgwon ita kadai ce a gidan tun farko ta so Aliyun ya yi hakan sai yaki saboda Su'ad ta ce bata so bazata zauna ba yanzu kuma sai tayi gaban kanta dan ta nuna masa nata matsayin a da ma bata son ta zama irin iyayen nan marasa hak'uri da yaransu ko surukansu ba.

*

Aliyu zuba mata ido kawai ya yi baya son ya yanke hukunci irin wannan cikin fushi babban takaicin shi ma musa masa da ta yi ga shi bazai iya gayawa kowa ba takaici goma da ashirin kenan.

Ga nacin Amira ga takaicin Su'ad duk haushinsu yake ji cikin Ikon Allah ya samu aikin aka kirashi can zai fara aikin dasu kafin su dawo da shi Kano contract din aiki a can Lagos na shekara biyu ne daga nan zai iya komawa inda yake so.

Da wanna farin cikin ya manta da wata Su'ad da al'amuranta rayuwar shi kawai yake yi ba ruwanshi da ita sai da ya gama komai ya gaya mata ya samu aiki a Lagos zai tafi in ta ga dama ta kintsu ta ji tsoron Allah ta daina in bata ga dama ba ta cigaba in baya ganin ta Allah yana ganinta akwai dalilin da ya sa bai sake ta ba har a wanan lokacin sai dai in ta kuma bai san irin abin da zai yi mata ba ya ajiye mata kud'i ya yi gaba ba ko waiwaye ya barta da baki a bud'e tana mamakin sauyawarshi duk yadda aka yi Yana da babbar hujja a kan ta tunda har ya kafe a kan hakan kuma buyaginta wannan karon bai jijiga shi ba.

*

Gidansu ya je don yi sallama da Gwagwo nan ya ga ana aikin gini da mamaki ya ce "Gwgwona ya haka kuma?"

"Gini nake yi maka kai da Amira."

"Amira wace haka?" Sai da ya fadu hakan ya san ya yi katobara ya dafe bakinshi ya yi lakwas yana karbar hararar Gwagwon.

"Kiyi hak'uri."

"Kai dai ka sani aure dai an daura kuma na gaya maka ko bayan raina ka saki yarinyar nan ban yafe maka ba Wallahi."

"Kiyi hak'uri abin da kike so shi zan yi."

"Ya rage nake. Wannan gurin naku ne zata tare da kai a nan kafin ka samo mata nata ita ma ka ji tsoron Allah ka yi adalci."

"In sha Allah."

"Gwagwo zan tafi yau sai Allah Ya dawo da ni kuma zamu dinga yin waya zan na yi miki aike sai na ga yanayin garin da aikin sai na ga yadda zan na zuwa hutun."

"Allah Ya yi muku albarka Allah Ya bada sa'a, Allah Ya sa a fi haka."

"Amin."

"Bari a kirawo Amira kuyi sallama kan ka tafi."

Da kyar ya ce "To."

Da kanta ta yafa mayafinta ta fita ta shiga gidansu Amira ta kirawota.

Daki ta shiga ta barsu a gurin.

Kusan dakika biyar babu wanda ya yi magana a cikinsu da kyar ta karya shirun ta ce "Ina kwana."

"Lafiya Lau. Zan tafi Lagos na samu wanna aikin."

Da fara'a ta ce "Ma Sha Allah,ubangiji Ya dafa Ya bada sa'a Ya sa a fi haka."

Yaji dadin addu'ar shi sa ya amsa "Amin."

"Kiji tsoron Allah daga makaranta sai makaranta in fita ta zama dole ki gaya min ban da kule-kulen samari yanzu ke matar aure ce. Ya dauko kud'i ya bata kiyi amfani da su."

"In sha Allah! Yaya zan yi yadda ka ce in Sha Allah. Allah Ya tsare hanya."

"Amin. In an gama wancan bangaren za ki dawo nan kafin mu ga abin da Allah zai yi."

"Toh ta fad'a."

Suka dada yin sallama ta Gwagwon sanan ya tafi ya barsu da kewa.

Sakamakon kauna.Where stories live. Discover now